Ko Barca za ta ci gaba da jan ragamar La Liga bayan wasan Mallorca?

Real Mallorca za ta karbi bakuncin Barcelona a wasan mako na bakwai a gasar La Liga da za su kara ranar Talata.

Barcelona ce ke matsayin farko a kan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da maki 16, iri daya da na Girona mai biye da ita.

Barcelona ta doke Celta Vigo 3-2 ranar Asabar 23 ga watan Satumba, ita kuwa Mallorca ta sha kashi a gidan Girona da ci 5-2 a karawar mako na shida.

Real Mallorca, wadda take ta 16 a kasan teburi ta ci wasa daya, ta kuma yi canjaras biyu, sannan aka doke ta karo uku daga wasa shidan da aka fara bana a La Liga.

Wasan da suka kara a La Liga bara kakar 2022/2023

Lahadi 28 ga watan Mayun 2023

  • Barcelona 3 - 0 Mallorca

Asabar 01 ga watan Oktoban 2022

  • Mallorca 0 - 1 Barcelona

'Yan wasan Barcelona da za su kara da Mallorca:

Ter Stegen, João Cancelo, Balde, R. Araujo, I. Martínez, Gavi, Ferran, Lewandowski, Raphinha, Iñaki Peña da kuma João Felix.

Sauran sun hada da Christensen, Marcos A., Romeu, S. Roberto, Gündoğan, Kounde, Astralaga, Lamine Yamal da kuma Fermin.