Abin da ke faruwa a cikin jikin mutum a yanayi na tsananin zafi

Asalin hoton, Getty Images
Akasari tsananin zafi, da ƙarancin iskar shaƙa, da yanayi maras daɗi, da yawan motsa jiki, duka waɗannan ayyuka kan haifar da hauhawar zafin jikin mutum. Idan ba a kula ba kuma zai iya haifar da matsala ga lafiyarmu.
Mutum kan galabaita lokacin da jikinsa ya ɗauki zafi, akasari saboda yin aiki a wuri mai zafi.
Idan zafin jikin mutum ya zarta ma'aunin 40C, jikin kan rasa damar sanyaya kansa kuma hakan ka iya haifar mana da bugun-zafi, wanda ka iya kashe mutum.
Ga sauran abubuwan da ya kamata ku sani game da haɗurran ƙaruwar zafi a jikin mutum.
Me tsananin zafi ke haifarwa a jikinmu?
Yayin da jiki ke ƙara zafi, jijiyoyin jini sai su buɗe. Hakan na sa jini ya sauka ƙasa sosai wanda zai sa zuciya ta fara aiki cikin ƙunci wajen tura jini zuwa sassan jiki. Wannan zai haifar da wasu alamu kamar raɗaɗi a kan fata ko kuma ƙafafuwa su kumbura saboda buɗewar jijiyoyin jini.

Asalin hoton, Getty Images
Jikin mutum na nuna alamu ne idan zafi na ƙaruwa ta hanyar ƙara yawan kwararar jini ga fatarsa, inda yake fito da zafin daga cikin jiki zuwa kan fata. Hakan na haddasa gumi, wanda ke bushewa kuma ya sanyaya jikin.
Sai dai gumi kan sa jiki ya rasa ruwan gudanarwa da gishiri, da kuma daidaito tsakaninsu a cikin jiki.
Idan aka haɗa wannan da kuma ƙarancin yawatawar jini, zai iya jawo bugun-zafi. Alamun cutar sun haɗa da:
- jiri
- ruɗewa
- raɗaɗi a gaɓɓai
- gumi mai yawa
- gajiya
Idan jini ya yi ƙasa da yawa, haɗarin kamuwa da bugun zuciya na ƙaruwa.
Me ya sa jikinmu ke zama haka?
Jikinmu na fama wajen daidaita zafin jikin kan ma'aunin 37.5C ko da kuwa muna cikin dusar ƙanƙara ne ko kuma tsananin zafi.
Wani yanayin zafi ne da jikinmu ke sabawa da shi kuma har ya fara aiki da shi.
Amma yayin da zafin ke ƙaruwa, shi kuma jiki yana ta kaiwa da kawowar yadda zai sanyaya kansa.
Hakan kan buɗe jijiyoyin jini da ke kusa da fata waɗanda ke haddasa zafin da muke ji a inda muke. Yayin da gumi ke bushewa, shi kuma zafin da ke cikin jiki na ƙaruwa sosai.
Bugun-zafi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Idan jiki ya fuskanci zafin da ya kai ma'aunin 39 zuwa 40C, sai ƙwaƙwalwa ta umarci gaɓɓai su rage aiki, sai kuma gajiya ta shigo.
Idan ya kai 40-41C, za a iya samun bugun-zafi - idan ya zarta 41C kuma sai jiki ya fara mutuwa gaba ɗaya.
Daga nan kuma sai sauran na'urorin jiki sa samu matsala, sinadaran halittar jiki su fara lalacewa, kuma akwai haɗarin wasu gaɓɓan jiki su daina aiki.
A irin wannan yanayi, jiki ba zai iya yin gumi ba ma saboda jini ya daina zuwa jikin fata, abin da ya sa za a dinga jin sanyi da kuma sauyin yanayi.
Bugun-zafi - wanda ke faruwa duk lokacin da zafi ya zarta ma'aunin 40C - na buƙatar taimakon likitoci, kuma idan ba a kula da shi nan take ba, yiwuwar mutum ya tsira da rayuwarsa ba ta da yawa.
Mafi kyawun hanyar da za a bi wajen sanyaya jiki ita ce a jefa mutum cikin ruwan ƙanƙara, ko kuma a saka wa mutum ƙanƙara a ƙugu da hammata - inda jijiyoyin jini masu muhimmanci suke - amma ya danganta da tsawon lokacin da mutum ya ɗauka a cikin tsananin zafi.
Farfesa George Havenith, ƙwararre kan muhallin da ɗan Adam ke raye a Jami'ar Loughborough, ya ce yanayin ɗumin da iska take da shi - humidity a turance - na da matuƙar muhimmanci game da yawan gumin da muke yi.
Idan ɗumin da ke cikin iska ya yi yawa, damar da muke da ita ta yin gumi na raguwa kuma hakan na hana mu sukuni.
Ko zafi na kisa?

Asalin hoton, Getty Images
Tsananin zafi ka iya yin kisa. Akasarin kisan kuma ta hanyar bugun zuciya ne da sauran bugu yayin da jiki ke ƙoƙarin daidaita yanayinsa da kansa.
Ana iya gane irin yawan mace-macen da za a iya samu da zarar yanayin ya zarta ma'aunin 25C zuwa 26C.
Sai dai kuma hujja ta nuna cewa an fi samun yiwuwar mutuwa idan zafi ya ƙaru a lokacin damina ko kuma farkon bazara, fiye da tsakiyar bazarar, inda ake ganin ranar farko ta tsananin zafin ta fi koyaushe haɗari.
Dalili ne shi ne, muna sauya ɗabi'unmu ne yayin da bazara ke ƙoƙarin farawa har zuwa cikinta ta yadda za mu saba da zafin.
Me zan yi idan na ga tsananin zafi ya bige wani mutum?
- Idan za a iya sanyaya musu jiki cikin rabin awa, to da alama lamarin bai yi tsanani ba.
- A kai su wuri mai sanyi-sanyi.
- A ce su kwanta kuma su ɗaga ƙafarsu sama kaɗan.
- A umarce su su sha ruwa mai yawa sosai.
- Za su iya shan lemuka masu ƙara kuzari
- A sanyaya fatar jikinsu - a watsa musu ruwa tare da yi musu fifita. Ya kamata a saka musu ƙanƙara a hammata ko wuya.
- Sai dai kuma, idan ba su farfaɗo ba cikin minti 30 to fa bugun-zafi ne zai biyo baya.
- Lamari ne gaggawa da ke buƙatar kulawar likitoci nan take.











