Senegal na dab da shiga ruɗani bayan ɗage zaɓe

An tura jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma zuwa babbar hanya a Dakar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zangar tare da kama mutane a Dakar
    • Marubuci, Yusuf Akinpelu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Lagos

Suna da ƙimar Senegal a matsayin tushen dimokuraɗiyya a yankin da ba shi da kwanciyar hankali na neman dusashewa, yayin da masu zanga-zanga suka yi arangama da ƴansanda a wajen majalisar dokokin ƙasar.

A ciki, ƴan majalisar dokokin ƙasar na ta muhawar kan ƙudirin doka mai cike da ce-ce-ku-ce na tsawaita wa'adin shugaban ƙasa da kuma jinkirta zaɓe na tsawon watanni shida bayan da shugaba Macky Sall ya soke zaɓen da aka shirya wanda ya rage makwanni uku kacal.

Khalifa Sall, babban ɗan'adawa kuma tsohon magajin garin Dakar, wanda ba shi da wata alaƙa da shugaban ƙasar ya kira jinkirin a matsayin 'juyin mulki ne' sannan ya buƙaci jama'a da su yi zanga-zangar nuna adawa da hakan.

Ƙungiyar ƙawancen siyasarsa ta sha alwashin zuwa kotu.

Thierno Alassane Sall, wani ɗan takara, wanda shi ma ba shi da alaƙa da shugaban ƙasar ya kira hakan 'babban cin amanar ƙasa' ya kuma buƙaci magoya bayansa da su taru a gaban majalisar dokokin ƙasar domin yin zanga-zanga da kuma tunatar da ƴan majalisar su tsaya a kan abin da aka san kasar.

Shawarar za ta buƙaci goyon bayan kashi uku cikin biyar na wakilai 165 domin samun amincewa.

Gamayyar jam'iyyar Benno Bokk Yakaar mai mulki, wadda ƙawancen Sall na jam'iyyar Republic ke da rinjaye a majalisar dokokin ƙasar.

Mista Sall ya nanata cewa ba ya shirin sake tsayawa takara.

Sai dai masu sukar sa na zargin sa da yunƙurin dagewa kan karagar mulki ko kuma rashin adalci wajen yin tasiri ga wanda zai gaje shi.

Ba da jimawa ba ya bayar da sanarwar ɗage zaɓen da ba a taɓa ganin irin sa ba, sai ga masu zanga-zangar sun mamaye babban birnin kasar, Dakar, domin nuna rashin goyon baya ga ɗage zaɓen.

Zanga-zangar Senegal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana ƙara nuna damuwa a ƙasar Senegal na cewa idan ba a gudanar da zaben ba kamar yadda aka tsara, tarzomar za ta iya bazuwa

An dade ana kallon Senegal a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da kwanciyar hankali a tsarin dimokuraɗiyya a yammacin Afirka.

Ita ce ƙasa ɗaya tilo a yankin Yammacin Afirka da ba ta taɓa yin juyin mulkin soja ba. Ta samu nasarar miƙa mulki sau uku cikin lumana kuma ba ta taɓa jinkirta zaɓen shugaban ƙasa ba.

A shekara ta 2017, sojojin Senegal sun jagoranci tawagar yammacin Afirka da aka aika zuwa makwabciyarta Gambia domin tilasta wa Yahya Jammeh da ya daɗe yana mulki bayan ya ƙi amincewa da shan kaye a zaɓe.

Kuma a yankin da aka yi juyin mulki, shugaba Sall ya kasance babban jigo a yunkurin da Ecowas ke yi na tilasta wa shugabannin soji gudanar da zaɓe tare da miƙa mulki ga farar hula.

Sai dai a halin yanzu tsarin demokradiyyar Senegal ya rataya a wuyar shugabanninta, kuma rikicin tsarin mulki na kara kunno kai. Manazarta sun ce kasar na fuskantar babban gwaji na ingancin zabe da 'yancin kai na shari'a.

Ƴan sanda sun kama magoya bayan 'yan takarar adawa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rikici ya barke yayin da 'yan sanda suka tsare magoya bayan 'yan takarar adawa
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Fargaba sai ƙara ruruwa take tun fiye da sama da shekaru biyu sakamakon abin da 'yan adawa suka ce da gangan ne ƙoƙarin cire su daga zaɓen ta hanyar gurfanar da 'yan takararsu da laifukan da ba su aikata ba. Har ma an haramta wata babbar jam’iyyar adawa ta tsayatakara.

Hukumomin kasar dai sun musanta yin amfani da tsarin shari'a don cimma wata manufa ta siyasa, kuma shugaba Sall ya ce yana ƙokarin kwantar da hankulan al'amura ta hanyar jinkirta kada kuri'a amma hakan bai yi tasiri ba ya zuwa yanzu.

Babban manazarci a Afirka ta yamma a Kamfanin tattara bayanai na Verisk Maplecroft, Mucahid Durmaz ya shaida wa BBC cewa "Shawarar ta jefa Senegal cikin yanayin rikicin tsarin mulki. Kundin tsarin mulki ya bukaci a shirya zabe akalla kwanaki 30 kafin karshen wa'adin shugaban kasa mai ci.

"Kuma dole ne a fitar da dokar da ke bayyana kalandar zaɓe kwanaki 80 kafin a kada kuri'ar. Ko da ya naɗa shugaban rikon kwarya bayan 2 ga Afrilu, za a yi sabani game da halaccin sa."

Gobara ta tashi bayan zanga-zangar 'yan adawa a Senegal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An dade ana kallon Senegal a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi samun kwanciyar hankali a Afirka ta Yamma

Hukumomin kasar sun hana amfani da intanet na wayar hannu a ranar Litinin din da ta gabata don hana abin da ta kira "sakonni na nuna kyama da kuma bata gari" daga yaɗuwa a intanet da kuma zai kai ga yin barazana ga zaman lafiyar jama'a - wato domin a wahalar da masu zanga-zangar.

Wasu mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa suna amfani da wasu hanyoyin kamar su Wi-Fi da Virtual Private Network (VPN) don samun amfani da intanet amma ba kowa ne ke iya yin hakan ba.

'Yan adawar sun yi Allah-wadai da rufe siginar tashar talabijin mai zaman kanta ta Walf TV, saboda tada zaune tsaye saboda yadda ta dauki nauyin nuna yadda ake gudanar da zanga-zangar.

An dai tsare wasu 'ƴan siyasa biyu na adawa da suka hada da tsohuwar firaminista, Aminata Toure, wadd a da ta hannun damar Shugaba Sall ce amma a yanzu ta zama daya daga cikin masu sukar sa, a takaice bayan zanga-zangar.

Zanga-zangar Senegal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kungiyar kasashen yankin Ecowas da kungiyar Tarayyar Afirka sun yi kira da a tattauna yayin da Tarayyar Turai ke son a gudanar da zaben cikin gaggawa.

Masu suka dai na fargabar cewa wannan dambarwar na iya jefa kasar cikin rudanin siyasa wanda zai iya zama hadari ga daukacin yankin Afirka ta yamma.

Gamsuwa da demokradiyya a Senegal ya ragu matuka a karkashin mista Sall. A cikin 2013, wani mai bincike a cibiyar sadarwa ta bincike mai zaman kanta Afrobarometer, ya gano cewa bayan mista Sall ya hau kan karagar mulki, fiye da kashi biyu bisa uku na al'ummar Senegal sun gamsu ko kuma sun gamsu da dimokuradiyya. Amma ra'ayin rabin al'ummar ya sauya a shekarar 2022.

Sai dai Mista Durmaz ya ce bai hango yuwuwar juyin mulkin soja ba saboda ƙasar Senegal tana da "jam'iyyun siyasa daban-daban, da kungiyoyin farar hula da masu fada a ji da shugabannin addini waɗanda ke shiga tsakani a rikicin siyasa tsakanin 'yan siyasa".

'Yan takara 20 ne suka shiga jerin sunayen 'yan takara na karshe da za su fafata a zaɓukan, amma wasu da dama ba a sanya su a cikin kwamitin tsarin mulki ko hukumar shari'a da ke tantance ko 'yan takarar sun cika sharuddan da ake bukata.

Wata mata da yarinya sun sauko daga cikin wata motar bas a babban titin Dakar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fasinjoji sun yi taho-mu-gama don sauka daga cikin wata bas yayin da 'yan sanda ɗauke da muggan makamai suka kutsa kai kan masu zanga-zangar

Shahararru daga cikin manyan 'yan adawa da aka hana tsayawa takara a zaben shugaban kasa sun hada da dan adawa Ousmane Sonko da aka dakatar saboda laifin cin zarafi da kuma Karim Wade, dan tsohon shugaban ƙasar, wanda ake zargi da zama ɗan kasar Faransa. Dukkansu sun ce shari’ar da ake yi masu na da alaka da siyasa.

Duk da jinkirin da aka samu, da wuya Sonko zai iya shiga zaɓen, domin tuni jam’iyyarsa ta maye gurbinsa da Bassirou Faye wanda shi ma yana gidan yari amma har yanzu ya cancanci tsayawa takara, in ji Mista Durmaz.

Mista Sonko ya nuna cewa yana iya tattaro magoya bayansa kan tituna don haka yayin da aka hana shi, akwai yuwuwar zaman ɗar ɗar.

Jam'iyyarsa ta Pastef da aka dakatar ta sha alwashin ja da baya kan jinkirin da aka samu, yana mai cewa hakan "babbar barazana ce ga dimokuradiyyarmu" da kuma " raina ra'ayin jama'a".

Ousmane Sonko na Senegal - gwarzon matasa ko mai tayar da hankali?

Wannan dai ba shi ne karon farko da aka hana manyan 'yan adawa tsayawa takara a zaben shugaban kasa ba. Dukkan su Karim Wade da Khalifa Sall an daure su ne bisa laifin cin hanci da rashawa a shekarar 2015 da 2018, bi da bi, kuma an hana su tsayawa takara a 2019.

A wannan karon, zargin cin hanci da rashawa na shari'a da ya shafi majalisar tsarin mulki, wanda jam'iyyar Karim Wade ta kawo, ya sa majalisar ta gudanar da bincike.

Shugaba Sall ya bayar da hujjar jinkirin zaɓen inda ya ce ana buƙatar lokaci don warware takaddamar da ta kunno kai tsakanin majalisar da wasu 'yan majalisar.

Duk da fushin da aka yi kan jinkirin da aka yi, jam'iyyar Democrat ta Senegal (PDS) ta mista Wade ta goyi bayanta, kuma idan 'yan majalisarta suka kada kuri'a da gwamnati, kudirin na iya wucewa.

Sai dai Wole Ojewale, kodinetan yankin na Dakar a cibiyar nazarin harkokin tsaro a yankin Afrika ta tsakiya, ya ce jinkirin bai dace ba.

"Shugaban ƙasa ba shi ne ke tafiyar da harkokin zaɓe ba, kuma har alkalan zaben ba su nuna shakku kan iya gudanar da zaben ba, ina ganin babu abin da zai kawo cikas ga harkokin siyasa."

Masu sukar Mista Sall dai na nuni da cewa wataƙila ya ji tsoron wanda zai gaje shi, firaminista Amadou Ba, na cikin hatsarin faduwa zabe.

"Jam'iyyarsa ta shugaba Sall ta rasa yadda za ta yi. Akwai alamun da ke nuna cewa wataƙila suna son ganin yadda za su sauya sheka, ko kuma su maye gurbin dan takararsu," in ji Mista Ojewale.