Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane irin hadari tashar nukiliya ta Zaporizhzhia da Rasha ta mamaye a Ukraine ke da shi?
Masu sanya ido kan makamashin nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya sun ce za su yi kokarin sanya ido na dindindina tashar makamashin nukiliya mafi girma a Turai - da ke kusa da fagen daga a Ukraine - domin ganin ba a fuskanci hatsarin nukiliya ba.
Rafael Grossi, shugaban International Atomic Energy Agency, ya yi gargadi kan hatsarin makamin nukiliya.
Bayan an kwashe makonni ana yunkurin zuwa tashar ta Zaporizhzhia, yanzu dai ya jagoranci tawagarsa zuwa tashar inda 'yan kasar Ukraine suka kwashe watanni shida suna aiki cikin mawuyacin hali.
''Duk da hare-haren da ake kai wa ba su haddasa wani bala'i ba kawo yanzu, to amma akwai barazana da ka iya haddasa wani bala'i ga muhalli nan gaba,'' kamar yadda IAEA ta bayyana a cikin sabon rahoton da ta fitar.
Yanzu haka jami'an hukumar sun lura da wata babbar barna a wani sashe na tashar nukiliyar da ke yankin Ukraine.
Rahoton ya kara da cewa ''IAEA ta damu matuka kan yanayin da ake ciki a ZNPP wanda bai canza ba.'' To amma ta yaya yakin da ake yi sai iya barna a tashar, kuma ya girman barnar zai iya kasancewa?
Me ke faruwa tashar nukiliya ta Zaporizhzhia a halin da ake ciki?
Rasha ta kwace tashar nukiliya ta Zaporizhzhia ne a farkon watan Maris, cikin mako na biyu da kutsen da ta yi cikin Ukraine.
Fadan da ake yi tsakanin dakarun Rasha da Ukraine ya datse kusa da tashar da ke kusa da birnin Enerhodar, kuma a lokacin wani gini ya kama da wuta, wanda hakan ya haifar da damuwa a ilahirin nahiyar Turai.
Tashar Zaporizhzhia na da kofofin ruwa shida da kuma rumbunan da dama da ke zuke tattakar nukiliya.
A baya, wani jami'in Ukraine ya ce an taba harba makami daga sama da ya lalata daga cikin na'urorin da ke wurin.
An yi kokarin kashe wutar da ta tashi wurin a lokacin, kuma ba tare da bata lokaci ba Majalisar tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta kira taron gaggawa, inda ta yi tir da harin.
Sai dai Rasha ta zargi yan koren Ukraine da haddasa gobarar.
Babban bala'in da zai iya faruwa
Babban bala'in da ake fargabar zai iya faruwa idan har makami mai linzami ko roka ta afka wa na'urorin da ke sarrafa nukiliya shi ne zai lalata tukane da na'urorin kai tsaye.
An shirya tukanen ta yadda za su iya jure wa duka daga wani abu da zai iya lalata su, amma kuma ba za su iya jure wa harin roka ko makami mai linzami ba. Hakan na nufin za a iya samun fashewar sinadarai da samuwar iska mai guba matsawar aka samu fashewar tukanen.
''Matsawar roka ta harbi tukanen, abin da zai faru shi ne za su fara yoyo da hakan zai haifar da bala'i a Turai, musamman a yankin Cremia da ilahirin Ukraine,'' in ji Olha Kosharna, masani da ke aiki da hukumar makamashin Ukraine.
Shi ma wani masanin Andrey Ozharovsky da ke aiki da Rasha, wanda ya kware kan kwashe tattakar nukiliya daga cikin jama'a ba tare da matsala ba, ya ce matsawar hadari ya faru a tashar nukiliya ta Zaporizhzhia, zai haifar da gurbacewar iska a dalilin fitar sinadarin radioactive Caesium-137, da ka iya tafiya mai nisa ta iska.
Hakan kuma zai haifar da cutuka ga jama'a masu nasaba da gurbacewar iska da kuma lalata kayan gona, wanda hakan zai haifar da matsalar abinci a shekaru masu zuwa.
Haka kuma wani bala'in shi ne na fashewar rumbun da ke ajiyar tattakar sinadarai a cewar masana nukiliya.
Abun da kasashen duniya za su iya yi?
Yarjejeniyar Geneva ta haramta kai hari ga tashohin nukiliya, a karkashin sashe na daya na dokar Geneva convention da aka samar a 1949, saboda tsoron mutuwar al'umma da hakan zai haifar. Sai dai kuma an halasta lalata tasha, idan har ana amfani da ita a matsayin makamin soji a maimakon samar da makamashi da zai taimaka wa al'umma. Ba a tashar nukiliya kawai ba, an haramta kai irin wadannan hare-hare a sansanonin soji da ke makwabtaka da tashohin nukiliya saboda hadarin da ka iya shafar su. A baya Ukraine ta bukaci kasashen duniya da su taimaka da na'urorin da za su rika kakkabo duk wani makami da ya tunkari tashar nukiliya ta Zaporizhzhia. Sai dai kuma hakan ba zai yiwu ba, saboda kasashen da ke taimaka wa Ukraine na tsoron idan suka yi haka, Rasha za ta fassara hakan da cewa sun shiga yakin ne kai tsaye.