Faransa ta maye gurbin Kimpembe da Disasi a Gasar Cin Kofin Duniya

Tawagar Faransa ta kira mai tsaron bayan Monaco, Axel Disasi domin maye gurbin Presnel Kimpembe, wanda ya kasa warkewa daga jinya da yake yi.

Faransa ce mai rike da kofin duniya da ta lashe a Rasha shekara hudu da ta wuce.

Tun farko Faransa ta bayyana Kimpembe, wanda da shi aka ci kofin duniya a Rasha, cikin wadanda za su wakilce ta a Qatar, amma har yanzu bai warke ba.

Za a fara Gasar Cin Kofin Duniya ranar 20 ga watan Nuwamba a kammala ranar 18 ga watan Disambar 2022.

Haka kuma Faransa ta gayyaci mai cin kwallaye a Moenchengladbach, Marcus Thuram, kenan tawagar ta ciki 26, bayan da Didier Deschamps ya bayyana 25 tun farko.

Disasi wanda aka haifa a Faransa, iyayensa daga Jamhuriyar Congo suke, har ma ta gayyace shi buga mata wasannin matasa 'yan kasa da shekara 20 a 2017.

Wannan shi ne karon farko da Disasi zai buga wa babbar tawagar Faransa tamaula, bayan wasa uku da ya yi a ta matasa 'yan kasa da shekara 20.

Faransa za ta fara wasan farko a rukuni na hudu ranar 22 ga watan Nuwamba da Australia a rukunin da ya kunshi Denmark da kuma Tunisia.

Jerin 'yan kwallon tawagar Faransa da za su buga Kofin Duniya a Qatar:

Masu tsaron raga: Alphonse Areola (West Ham), Hugo Lloris (Tottenham), Steve Mandanda (Rennes)

Masu tsaron baya: Lucas Hernandez (Bayern Munich), Theo Hernandez (AC Milan), Ibrahima Konate (Liverpool), Jules Kounde (Barcelona), Benjamin Pavard (Bayern Munich), William Saliba (Arsenal), Dayot Upamecano (Bayern Munich), Raphael Varane (Manchester United)

Masu buga tsakiya: Eduardo Camavinga (Real Madrid), Youssouf Fofana (Monaco), Matteo Guendouzi (Marseille), Adrien Rabiot (Juventus), Aurelien Tchouameni (Real Madrid), Jordan Veretout (Marseille)

Masu cin kwallaye: Karim Benzema (Real Madrid), Kingsley Coman (Bayern Munich), Ousmane Dembele (Barcelona), Olivier Giroud (AC Milan), Antoine Griezmann (Atletico Madrid), Kylian Mbappe (Paris St-Germain), Christopher Nkunku (RB Leipzig)