'Ana son amfani da fursunonin da aka saki a yamutsa zabe a Kano'

Asalin hoton, Getty Images
A jihar Kano da ke arewacin Najeriya ana ci gaba da cece-kuce kan wata afuwa da gwamnan jihar ya yi wa wasu fursunoni da ke jiran hukuncin kisa.
Cikin masu sukar matakin na gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje har da jam`iyyar adawa ta NNPP, wadda ta yi zargin cewa ya yi wa fursunonin afuwa ne don gwamnatinsa ta yi amfani da su wajen haddasa yamutsi a lokacin zaben gwamnan da za a yi a karshen mako, saboda a cewarsu, APC ba za ta kai labari ba.
Jam`iyyar NNPP ta yi zargin cewa takwararta APC mai mulkin jihar Kano ta hangi cewa ba ta da katabus a zaben gwamnan da ake sa ran yi a ranar Asabar mai zuwa; wannan ne ya sa take kulle-kulle da shirya kutungwila.
NNPP ta ce afuwar da gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa wasu fursunoni, wadanda ciki har da masu jiran hukuncin kisa su goma sha biyu dabara ce ta fitar da su domin APC ta yi amfani da su a lokacin zabe, ta yadda za ta tankwara sakamako…saboda ta fahinci NNPP za ta kasa ta.
Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda shi ne mai magana da yawun dan takarar gwamna na jam`iyyar NNPP a jihar, ya shaidawa BBC cewa sun yi allawadai da yi wa mutanen afuwa, saboda duk wanda aka ce kotu ta same su da laifin da ta kai ga yanke musu hukuncin kisa, hakan na nuna tabbas akwai matsala.
Don haka bai ga dalilin da zai sa a fito da su a wannan lokaci da ake gab da zabe ba, inda suka ce su na zargin za a yi amfani da su domin tada yamutsi a lokacin zaben gwamna da ke tafe, a karsjen makon nan.
Sai dai gwamnatin Kano ta musanta wannan zargin, tana cewa NNPP ce dai ta karaya ta fara neman dalili ko abin fada bayan ta sha kaye a zaben gwamna da ke tafe.
Kamar yadda kwamishinan yada labarai na jihar, Mallam Muhammad Garba, a hirarsa da BBC ya ce APC ta shirya wa zaben, kuma za ta kai NNPP kasa ko daga zaune, don haka babu abin da zai sa ta karya doka don cimma muradinta. Ya kuma kara da cewa mutane 12 kadai ta yaya za su je kananan hukumomi masu yawa da ake da su a Kano domin tada zaune tsaye
Zaben na bana dai za a iya cewa yana da zafi a jihar Kano, sakamakon zaman tsamar da ke tsakanin magoya bayan jam`iyyar hamayya ta NNPP da na jam`iyyar APC mai mulki.
Ko a zaben shugaban kasa da na `yan majalisar dattawa da ta wakilai da aka kammala an yi hargitsi a wasu sassan jihar har wasu sun rasa rayukansu, jam`iyyu biyun dai na zargin juna da haddasawa, kuma tuni maganar ta kai gaban alkali.
Irin abubuwan da suka faru, sun sa mutane da dama fargaba game da yadda zaben gwamnan da za a yi zai kasance. Masu fada a ji a jihar daga kan manyan 'yan kasuwa da malamai ke kira ga 'yan siyasa su sanyaya zukata tare da gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.











