Waɗanne kalubale sabbin gwamnonin Sokoto da Zamfara za su fuskanta?

A ranar 29 ga watan Mayun shekara ta 2023 ne ake rantsar da sabbin gwamnoni da za su fara mulki a karon farko da kuma wasu da za su koma wa'adi na biyu a Najeriya.

Kusan ko wace jiha a kasar na da irin ta ta matsalar, amma akwai wadansu jihohi musamman a arewacin Najeriya da sabbin gwamnonin da za su karbi mulki ke da jan aiki a gabansu na warware wadannan matsalolin.

Jihar Sokoto

Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin jihohin da jam'iyyar APC za ta karbi mulki bayan hukumar zaben Najeriya INEC ta ayyana Ahmed Aliyu a matsayin wanda ya lashe zabe.

Ga wasu daga cikin kalubalen da ke gaban sabon gwamnan na Sokoto.

Tattalin arziki

Dr. Mansur Isa malami ne a jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto, ya ce abu na farko da ya kamata sabuwar gwamnatin Sokoto ta mayarda hankali kai shi ne habaka tattalin arzikin jihar wacce ta kasance daya daga cikin jihohin da suka fi talauci a Najeriya.

"Gwamnati da za ta sauka ta tattaro basuka da yawa kuma hakan ya raunata tattalin arzikin Sokoto, ta karbi kudaden ne da sunan aiwatar da ayyukan ci gaban al'umma amma har yanzu ba a yi su ba," a cewar Dr. Mansur.

Masanin ya ce a halin yanzu kudin da ake samu a jihar ya na tafiya ne a kan biyan ma'aikata albashi kuma babu kudin da zai rage ra-ra a yi amfani da shi wajen sauran ayyukan raya kasa.

"Dole ne sabuwar gwamnati ta bijiro da sabbin hanyoyin farfado da tattalin arziki idan har ana so al'ummar Sokoto su samu ci gaba".

Ayyukan raya kasa

Wani kalubale da sabon gwamnan Sokoto zai fuskanta shi ne tarin ayyukan raya kasa da jihar ke bukata.

Akan wannan batun kuwa Dr. Mansur ya ce a halin da ake ciki, jihar ta na bukatar sabuwar gwamnati ta aiwatar da ayyukan raya kasa wadanda za su shafi al'umma kai tsaye.

Ya ce ayyuka irinsu gina asibitoci da makarantu da hanyoyi da kuma samar da ruwan sha su na daga cikin abubuwa da mazauna jihar ke bukata.

"Asibitin Sokoto na bukatar gyara kwarai, idan ka shiga za ka ga yadda ake karancin magani sannan gine-ginen asibitin na bukatar a sabontasu; Haka batun ruwan sha ana sayarda jarka daya daga Naira150 zuwa 250 a wasu yankuna don haka mutane na bukatar a gyara duk wadannan" acewar Dr. Mansur.

Tsaftace Aikin Gwamnati

Dr. Mansur Isa malami a jami'ar Usman Danfodiyo ya ce wani kalubale da ke gaban sabuwar gwamnatin jihar shi ne tsaftace aikin gwamnati ta yadda za a baiwa ma'aikata damar yin aiki ba tare da kutse daga 'yan siyasa ba.

"Shekaru da dama an daina baiwa wasu ma'aikatu kudin gudanarwa kuma wannan ya shafi kuzarin ma'aikata da gudanar da aiki.

Wasu ma'aikatu basu da takardun yin kwafi-kwafi na ayyukan ofis-ofis wasu kam ma basu da ko kwamfutoci; A yanzu haka akwai wasu ma'aikatu da aka yankewa wutar lantarki saboda rashin biyan kudin wuta" in ji Dr. Mansur.

Jihar Zamfara

Zamfara jiha ce da ke arewa maso yammacin Najeriya, tana da ma'adinai sannan mazaunanta suna harkar noma da kiwo.

Amma wani abu da ta yi fice da shi a shekarun baya-bayan nan shi ne rashin tsaro da ya haddasa asarar rayuka da kuma dukiya mai dumbin yawa.

Yanzu dai sabuwar gwamnati za ta karbi mulki daga hannun gwamna mai barin gado Bello Matawalle na jam'iyyar APC, kuma sabon gwamna mai jiran gado Dauda Lawal na jam'iyyar PDP ya na da kalubale a gabansa.

Farfesa Yahaya Tanko masanin siyasa ne a jami'ar Usman Danfodiyo ta Sakoto, ya ce dole ne gwamnan mai jiran gado ya daura damarar magance matsalolin kamar haka;

Matsalar tsaro

Sanin kowa ne Zamfara na fama da matsalar tsaro kuma akwai jan aiki a gaban zababben gwamna na samarda zaman lafiya a matsayinsa na babban jami'in tsaron jihar.

Farfesa Yahaya ya ce "jihar Zamfara tayi fice wajen rikicin 'yan fashin daji da satar mutane da kuma satar dabbobi, a duk kananan hukumomi 14 na jihar babu inda ake da zaman lafiya kashi 100% kuma wannan shi ne babban kalubale da ya kamata gwamnan ya magance".

Ya kara da cewa akwai dubban daruruwan 'yan gudun hijira da suka tumbatsa zuwa sassa daban daban na Najeriya wadanda dole ne a inganta tsaro domin su koma garuruwansu na asali.

"Akwai rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya da kuma Hausawa da Fulani a halin da ake ciki yanzu, abunda ya kamata shi ne a yi sasanci tsakanin al'ummomin nan biyu domin hana ci gaban wannan gabar da 'yan bindiga da barayin shanu suka haddasa", a cewar Farfesa Yahaya.

Ya kara da cewa "akwai bukatar a samar da hanyoyi domin dawoda aminci tsakanin al’umma dake husuma da juna, a yi afuwa sannan a bude sabon babi na zamantakewa a Zamfara".

Inganta rayuwar ma'aikata

Duk da yake ba a jihar Zamfara kadai ma'aikata ke bukatar ingantacciyar rayuwa ba, amma su na Zamfara lamarinsu ya fi kamari ne sakamakon rashin tsaro da kuma karancin walwala.

Farfesa Yahaya Tanko masanin siyasa a jami'ar Usman Danfodiyo ta Sakoto, ya ce "hakkokin ma'aikata sun makale, akwai bukatar a rika biyan albashi akai-akai sannan a gyarawa musu albashin ta yadda akalla za su rika biyan wasu daga cikin bukatunsu cikin sauki.

Shi albashi biyansa ya na baiwa malami kuzarin aiki, baya ga wannan ya kamata a gyarawa Zamfara makarantu musamman na Furamare da Sakandare". in ji Farfeson.

Har'ilayau ya ce akwai makarantu da yawa dake rufe sakamakon rashin tsaro, ya kamata gwamnati ta inganta tsaro sai a bude su

Samar da Ababen more rayuwa

Jihar Zamfara ita ce 'kurar baya' wajen samarwa al'ummarta ababen more rayuwana a jihohin da ke arewa maso yammacin kasar.

Masanin siyasa Farfesa Yahaya ya ce samarda ruwan sha da gina tituna da habaka tattalin arziki suma abubuwa ne da sabon gwamna ya kamata ya mayarda hankali kansu a Zamfara.

Ya kuma ce dole ne a inganta tattalin arzikin jihar saboda mutane suna fama da fatara da yunwa da kuma koma baya.

"Da ma da noma da kuma kiwo mutane da dama suka dogara, ga shi masu satar mutane da kuma 'yan fashin daji sun hana ayi noma da kiwo a garuruwa da yawa na Zamfara, mutanen kauyuka sun koma matalauta, suna gudun hijira kuma sun koma mabarata" a cewar Farfesa Yahaya.

Sharhi

Babu ko shakka, sabbin gwamnonin Sokoto da Zamfara suna da jan aiki a gabansu bisa la'akari da abunda masana da suka fito daga yankin suka fada.

To amma idan akwai niyya mai karfi, ko babu komai, gwamnonin za su yi iya kokarinsu wajen magance wasu daga cikin matsalolin da aka bayyana.

Yanzu dai abunda ni Salihu Adamu Usman da kuma sauran 'yan Najeriya za mu jira mu gani nan da shekara hudu masu zuwa shi ne yadda zababbun gwamnonin za su tunkari matsalolin da ke addabar jihohin nasu.