Man United ta kara ƙudin da ta fara taya Branthwaite na Everton

Manchester United ta kara ƙudin da ta fara taya ɗan wasan Everton mai tsaron baya, Jarrad Branthwaite.

A watan jiya ne Everton ta ƙi sallama £35m da United ta fara taya ɗan wasan tawagar Ingila.

An fahimci cewar ta yi tayi na biyu kan £45m da karin tsarabe-tsarabe da ake sa ran cimma matsaya nan gaba.

To sai dai wasu rahotannin da aka sanar da BBC na cewa har yanzu Everton ba ta amince da tayi na biyun ba.

Branthwaite ya taka rawar gani a Goodison Park, wanda ya taimakawa ƙungiyar Merseyside ta ci gaba da zama a Premier League a kakar da ta wuce, wadda aka kwashe mata maki, sakamakon karya dokar ciniki daidai samu.

United na fatan kara karfin ƙungiyar kan fara kakar bana, musamman gurbin tsare baya, tana kuma tattaunawa da Bayern Munich kan ɗaukar Matthijs de Ligt, wanda ke tare da Netherlands a Euro 2024.

Raphael Varane ya bar Old Trafford a karshen kakar da ta kare, har yanzu ba a fayyace ko an kulla yarjejeniya da Jonny Evans ba.

Ana kuma tantamar makomar Victor Lindelof, wanda ya halarci filin atisaye a Carringhton ranar Litinin da sanyin safiya.