Barca da United na ci gaba da tattaunawa kan Rashford, Arsenal na son Watkins

Lokacin karatu: Minti 2

Ana sa ran Arsenal za ta samu ci gaba a yunkurin dauko dan wasan Ingila mai taka leda a Aston Villa, wato Ollie Watkins mai shekara 29, wanda tun ya na karami ya ke kaunar kungiyar, kuma wannan ne karo na biyu da take tuntuba akan dan wasan(Mail)

Manchester United na tattaunawa da Barcelona domin sayar da dan wasan gaba na Ingila, Marcus Rashford, 27, sai dai babu tabbas ko kulub din na Sifaniya zai kammala komai don dauko dan wasan kafin ranar Litinin. (Telegraph)

Kungiyoyin Bayern Munich da Borussia Dortmund sun bi sahun Tottenham a son dan wasan Ingila mai taka leda a Southampton Tyler Dibling, mai shekara 18. (Sun)

Ana sa ran mai kai hari na Colombia Jhon Duran, 21, zai yi gwajin lafiya a Landan a ranar Alhamis, gabannin komawarsa Al Nassr bagatatan kan kudi fam miliyan 64 daga Aston Villa. (Athletic)

A shirye Arsenal ta ke ta tuntubi Bayern Munich kan mai kai hari na Faransa ajin 'yan shekara 21, Mathys Tel, 19, kafin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa a watan Junairu. (Football Transfers)

Gunners da Chelsea na bincike kan Tel inda ita ma kungiyar Manchester United are ke bibyar halin da dan wasan ke ciki. (Independent)

A bangare guda kuma, ita ma kungiyar Tottenham na son dan wasan amma bashi. (Mail)

Napoli ta yi watsi da tayin fam miliyan 54.5, kan mai kai hari na Najeriya da ke taka leda a Galatasaray Victor Osimhen. (Corriere dello Sport)

Napoli ta shaidawa wakilan dan wasan Argentin Alejandro Garnacho mai shekara 20, cewa a shirye su ke su sake daukar shi idan Manchester United da rage burin da ta ci akan dan wasan. (Fabrizio Romano)