Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Trump na maraba da karyewar da dala ke yi a cikin shekaru uku
- Marubuci, Cecilia Barría
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo, Miami
- Lokacin karatu: Minti 6
Darajar dala na ci gaba da faɗuwa a duniya.
Ana tsaka da rikicin kasuwanci da Trump ya ɓullo da shi tun daga lokacin da ya sake komawa a kan muƙaminsa a Fadar White House a watan Janairu dala ta somawa faɗawa wannan yanayi na koma baya.
A wannan makon, darajar ta kai wani matsayi na zama kusa da ƙutal a cikin shekaru uku, idan aka daidaita ta da sauran manyan kuɗaɗen kamar Euro da Yen na japan da Fam na Ingila, hakan na faruwa ne daidai lokacin da su kansu masana'antun Amurka ke fuskantar koma baya a cikin watanni uku jere.
Wannan lamari ba Amurkawa ko wasu ƙasashe da tattalin arzikinsu ya dogara da ƙarfin dala kawai ya shafa ba har da tattalin arzikin duniya.
Wasu bankunan da ke saka jari, irin su Morgan Stanley da JP Morgan da Goldman da ke yin hasashen cewa dalar za ta ci gaba da karyewa a lokain da ake tsaka wannan rikicin kasuwacin da da ke barazana ga tattalin arzikin duniya.
"Dala ta karye sakamakon matakan Trump na ƙashin kai da maufofinsa da ke cike da kurakurai, waɗanda ke ci gaba da dusashen martabar Amurka," Gabriela Siller, ne a a cibiyar da ke nazarin ci gaban tattalin arziki a kamfanin hada-hadar kuɗi na BASE da ke Mexico ya sanar da BBC hakan.
A cewar Miller matakan shugaban ƙasar sun shafi cigaban Amurka sun kuma jefa fargaba a zukatana jama'a game da kimar dala ga wasu ƙasashen da ke amfani da ita a matsayin madogara.
Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalai na zahiri akan karyewar darajar kuɗin na Amurka shi ne yadda fitar da kaya daga ƙasar zuwa ƙetar ya zama wata babbar gasaa kasuwar duniya, saboda kayan da aka fitar za su yi araha ga masu saye daga waje.
A hannu guda kayan da ake shigarwa a Amurka za su yi tsada, saboda farashinsu ya ƙaru.
Kimar kuɗin ruwa
Galibi idan aka samu raguwar kuɗin ruwa a Amurka hakan na iya rage darajar dala kasancewar masu ajiyar kuɗi a bankuna da masu saka jari ba za su neme ta sosai ba.
Kenan faɗuwar darajar kudin na iya sa Asusun Ajiyar Kuɗin Amurka, (da ke daidai da manyan bakunan ajiya na ƙasashen duniya) zai dogara ga kuɗin ruwa ɗan kaɗan.
Ƙara yawan kuɗin ruwa kullum zai zama wata hanya ga babban bankin ƙasa ta yadda za i iya yaƙi da tashin farashi kaya, saboda matakin zai sa mutane ba za su sayi kaya da yawa ba a shaguna da wasu wurare na daban.
A haka Trump ya nemi Babban Bankin ƙasar ya rage yawan kuɗin ruwa.
Rashin yarda
A zahirin gaskiya masana tattali arziki da dama sun nuna damuwa cewa karyewar darajar dala a kwanan nan na nuna aukuwar wani abu mai matsala: za a daina yarda da Amurka.
"Yardar da duniya ke ba wa ƙasar da kuma dogaro da ita abu ne daɗaɗɗe da kai shekaru ɗari ko ma fi," in ji Barry Eichengreen wanda masani tattalin arzki a Jami'ar Kalifoniya.
"Duk wannan amincewa tsawon shekarun na iya tafiya a banza cikin ƙiftawar ido"
Dalilan Trump na son karya darajar dala
Gomman shekaru da gwamnatocin Amurka ke ƙarfafa inganta darajar dala
Haka ya taimakawa ƙasar wajen rage yawan ciyo bashi, kuma ya ƙara wa Amurka kwarjini ga ƙasashen waje.
Ya kuma kai ga yin matsin lamba ga ƙasashen da ba su ga macji da Amurka kamar Iran da Russia da Venezuela, ta hanyar rage musu damar samun dala.
Buƙatar dala ɗin sai ya ɗore - har ma a lokacin da Amurka ta shiga matsalar koma bayan tattalin arziki. Sai dai wasu masu sharhi na cewa gwamnatin Trump na ganin abubuwa ta wata hanyar daban.
Suna cewa shugaban Amurkan na hangen wannan matakin ne kawai zai iya saukakawa 'yan ƙasar a daidai lokacin da ya fito da wannan sabbin manufofi, ta yadda a cewar Trump idan aka karya darajar dalar zai taimaka wajen inganta ɓangaren masana'antun Amurka, domin dawo da abin da masu goyon bayan Trump ke gani a matsayin "lokacin sauyin alhairi" a Amurka.
"Ai Trump ba ya son dala mai ƙarfi domin kuwa za ta ƙara yawn shigar da kaya cikin ƙasarsa," a cewar Siller.
Wannan ra'ayi dai na nuna cewa Amurka na buƙatar dala maras ƙarfi ne domin ta bunƙasa masana'antun cikin gidanta, da sake samar da aikin yi da ƙara yawan fitar da kaya zuwa waje.
Kafafen watsa labaran Amurka da masana tattalin arziki na cewa akwai wata yarjejeniya da ake kira "Mar-a-Lago Accord" da shugaban tawagar ƙararru akan tattalin arziki da ke ba Trump shawara Stephen Miran ya bayar da shawarar aiwatarwa, na cewa akwai buƙatar a karya darajar dala.
Shakku game da kuɗaɗen asusun ajiya
Asusun ajiya wani nau'in kuɗi ne da manyan bankuna ko hukumomi ke ajiyewa a matsayin kadarar ƙasashe da akan ajiye. Ana amfani da shi wajen mu'amala tsakanin ƙasashe da saka jari da kuma biyan bashi.
Wannan yarjejeniya ko shiri da ake kira "Mar-a-Lago Accord", na daidai tunanin yadda ake kallo kimar dala ne a matsayin babban kuɗin duniya, ba wani abin tinƙaho ba ne, face abu ne da ake ganin ya zo ne domin ya ruguza tattali arzki da masana'antun Amurka kawai.
Neman dala ruwa a jallo kamar yadda wannan shiri ke kallo zai ƙara mata darajar da za ta sa kayan Amurka su yi matuƙar tsada a kasuwannin duiya.
Wannan kuma ba kome zai haifar ba face tilastawa masu kamfanonin a ƙasar fita waje su kafa masana'antunsu bisa dalilan rage kashe kuɗi a banza wajen biyan ma'aikata da sayen kaya.
Farfesa Kenneth Rogoff, masani tattalin arziki a Jami'ar Harvard kuma tsohon jami'in Asusun Bayar da Lamuni na duniya (IMF) YA CE, "Miller ya fito da wannan matakin ne da ya ke ganin kamar wata dubara ce, sai dai cike ya ke da illoli ga tattalin arziki".
Magori wasa kanka da kanka
Duk waɗannan abubuwa na tafiya ne tamkar tsarin 'kai ke kiɗanka da rawarka', a gwamnati da ke bin ra'ayinta ita kaɗai.
Daidai ya ke da irin matakin da Trump ya ɗauka a watan Afirilu da ya bayar da sanarwar ƙaƙaba dangogin haraji abin da ya rage ƙarfin tasirin Amurka ga masu saka jari daga wajenta har ma ya rage ƙarfin alaƙarta da kimar dala, abin da wani mataki ne kawai da gwamnatin ta fito da shi domin ta azurta kanta da kanta kawai.
Wannan yanayi na rashin yarda tsakanin masu saka jari da kuma ita kanta Amurka da kuma kuɗinta ba abu ne mai kyau ga makomar ƙasar, duk da wasu masana na cewa ba abu ne da zai ɗore ba.
Sai dai Amurka ta cike da fargabar samun hauhawar farashin kaya domin za su ci gaba da sayen kayan waje da tsada saboda ƙarin haraji da kuma karyewar darajar dala
Za su tuna alƙawari Trump a lokacin zaɓe na rage tsadar rayuwa.
A yanzu dai akwai ayoyin tambaya da dama, ko da yake jaridar Wall Street ta ruwaito cewa matsayin dala ya wuce ta faɗa garari kuma tana ci gaba da farfaɗowa.