Najeriya za ta ɗauko sabon koci daga ƙasar waje

Finidi George

Asalin hoton, NFF

Bayanan hoto, A ranar 13 ga watan Mayun da ya gabata NFF ta ƙaddamar da Finidi (tsakiya) a matsayin babban kocin Super Eagles na dindindin

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta sanar da shirinta na ɗauko mai horarwa daga ƙasar waje domin yunƙurin kawo gyara a wasannin tawagar ƙasar ta Super Eagles.

Nigeria Football Federation (NFF) ta ce za ta ɗauko mai ba da shawara kan wasanni wato Technical Adviser a Turance don ya jagoranci wasannin neman shiga gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2025 da kuma na Kofin Duniya da suka rage.

Bayan rashin nasarar da Super Eagles ɗin ta yi a wasannin da ta buga zuwa yanzu, Ministan Wasanni John Eno ya bai wa NFF wa'adi domin shawo kan matsalar ta hanyar sauya tawagar kociyoyin ƙungiyar.

Kazalika, ya nemi cikakken bayani daga NFF game da yadda Najeriya ta buga wasanni biyu - ta yi canjaras da Afirka ta Kudu sannan Benin ta doke ta a wasannin neman shiga Kofin Duniya.

Wannan ta sa NFF ɗin ta sanar da matakin hayo mai horarwa daga ƙasar waje bayan kammala ganawar da mahukuntan hukumar ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Musa Gusau suka yi a ranat Alhamis.

Sai dai zuwa yanzu babu tabbas game da abin da hakan ke nufi ga kociya Finidi George, wanda aka sanar a matsayin babban kocin tawagar a watan da ya gabata.

Duk da cewa sanarwar ba ta ce za a kori Finidi ba, amma hakan na nufin ko dai ya ajiye aikin gaba ɗaya ko kuma ya ci gaba a matsayin mataimakin wanda za a kawo, kamar yadda ya yi wa Jose Peseiro mataimaki.

"An bai wa NFF abin da bai wuce mako ɗaya ba ta gabatar da sauye-sauyen da za ta yi don tabbatar da zama cikin shiri na zagayen wasannin za a shiga," in ji ministan.

Sanarwar da NFF ta fitar bayan taron ta ce: "Kwamatin ya amince ya ƙarfafa sashen horarwa na Super Eagles da ƙwararru. Haka nan, za a sauya wa ƙaramin kwamatin horarwa fuska nan take."

Tun bayan da Finidi tsohon kocin kulob ɗin Enyimba ya karɓi aikin, maki ɗaya kacal Najeriya ta samu daga cikin shida da ya kamata bayan canjaras 1-1 da Afirka ta Kudu har gida, da kuma 2-1 da Benin ta doke ta a birnin Adbijan na Ivory Coast.

Da wannan sakamon, Super Eagles ɗin ta koma ta biyun ƙarshe a teburinsu na wasannin neman shiga Kofin Duniya da maki uku cikin wasa huɗu da ta buga.

A taƙaice Najeriya ba ta ci wasa ko ɗaya ba bayan ta yi canjaras 1-1 a wasa biyu da ƙasashen Lesotho da kuma Zimbabwe a ƙarƙashin tsohon koci Jose Peseiro.