Ganduje ya zama sabon shugaban APC

d

Asalin hoton, Media aide

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ya tabbatar da zaɓen Dakta Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano, a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa.

An zaɓi Ganduje ne a lokacin taron kwamitin gudanarwar jam’iyyar na 12 da aka gudanar a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja babban birnin ƙasar.

Shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu na cikin manyan ƙusoshin jam'iyyar da suka halarci taron kwamitin zartarwar APC na ranar Alhamis.

Haka zalika, kwamitin zartarwar ya tabbatar da Sanata Ajibola Basiru a matsayin sakataren jam'iyyar na ƙasa.

Bayan sanar da nade-naɗensu, magoya bayan Ganduje da Ajibola Basiru sun ɓarke da sowa da kuma murna waɗanda rahotanni suka ce har sun kusa hargitsa shirye-shiryen wurin na wani ɗan lokaci.

Ranar 17 ga watan Yuli ne tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da babban sakataren APC Sanata Iyiola Omisore suka sanar da ajiye muƙamansu.

Daga bisani, jam’iyyar ta sanar da naɗin Sanata Abubakar Kyari, wanda shi ne mataimakin shugaban APC shiyyar arewacin ƙasar, a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar.

A ranar 27 ga watan Yuli ne shugaban ƙasar Bola Tinubu ya sanya sunan Sanata Abubakar Kyari cikin jerin mutanen da ya aika Majalisar Dattawan ƙasar don tantance su a matsayin ministocin gwamnatinsa.

Tun bayan saukar Abdullahi Adamu ne ake ta raɗe-raɗin cewar Abdullahi Ganduje, tsohon gwamnan na Kano zai iya maye gurbinsa a matsayin sabon shugaban APC.

Gabanin hakan dai ana ta ce-ce-ku-ce kan ko sunan tsohon gwamnan na Kano, kuma ɗaya daga cikin manyan na-hannun daman Shugaba Tinubu, yana cikin waɗanda za a naɗa muƙamin minista, musamman saboda rawar da ya taka tun farko samun nasarar shugaban ƙasar a zaɓen 2023.

Shugaban ƙasar ya sanya sunayen wasu a cikin tsoffin gwamnonin APC, a matsayin waɗanda zai bai wa muƙaman minista a gwamnatinsa.

Jawabin Ganduje na kama aiki

Sabon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce zai fara aiki ba tare da sanyin jiki ba don tabbatar da nasarar jam'iyyar mai mulki a zaɓukan gwamna na ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Imo da Kogi da kuma Bayelsa.

Tsohon gwamnan na Kano ya yi wannan jawabi ne jim kaɗan bayan tabbatar da shi a matsayin shugaban APC na ƙasa.

Ganduje ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu kuma ya yi alƙawarin cewa a zamanin mulkinsa zai tabbatar da ganin dimokraɗiyya ta yi tasiri a cikin gida. Ya kuma yi alƙawarin cewa zai tabbatar da rijistar haƙiƙa ta 'ya'yan jam'iyyar APC kuma zai mayar da hankali ga sha'anin gudanar da zaɓe da kuma sulhunta rikice-rikice.

A cewarsa, sabon shugabancinsa zai samar da yanayi bai ɗaya ga dukkan 'ya'yan jam'iyyar a lokacin zaɓukan fitar da gwani.

Wane ne Abdullahi Ganduje?

An haifi Abdullahi Umar a ƙauyen Ganduje da ke cikin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano a 1949.

Ya fara karatun Ƙur'ani da Islamiyya a ƙauyensu, inda ya samu ilimin addini. Ya shiga firamare ta Dawakin Tofa daga 1956 zuwa 1963.

Ganduje ya fara makarantar sakandiren Birnin Kudu a 1964 inda ya kammala a 1968.

Ya shiga makarantar horar da malamai da ke Kano tsakanin 1969 zuwa 1972.

Tsohon gwamnan jihar Kanon ya samu digirinsa na farko a fannin ilmin malanta a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria cikin jihar Kaduna a 1975.

A 1979 ne kuma ya kammala digirinsa na biyu a Jami'ar Bayero ta Kano, sannan ya sake komawa Jami'ar Ahmadu Bello daga 1984 zuwa 1985 don karanta fannin gudanar da harkokin gwamnati.

A 1993 ne ya samu digirin-digirgir daga Jami'ar Ibadan.

Siyasarsa

Ganduje ya shiga jam'iyyar NPN a jamhuriyya ta biyu sannan ya zama mataimakin sakatare na jihar Kano daga 1979 zuwa 1980.

Ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilai a 1979 ƙarƙashin jam'iyyar NPN, amma bai yi nasara ba.

A 1998, ya shiga PDP inda ya nemi jam'iyyar ta tsayar da shi takarar gwamna, amma bai yi nasara ba, maimakon haa sai ta tsayar da Rabi'u Musa Kwankwaso.

Amma aka zaɓi Ganduje a matsayin mataimakin Kwankwaso tsakanin 1999 da 2003, sun sake cin zaɓen gwamna da mataimakin gwamna a Kano a shekara ta 2011 zuwa 2015.

A 2015 ne kuma, aka zaɓi Dakta Abdullahi Umar Ganduje matsayin gwamnan Kano, inda ya yi wa'adin mulki biyu daga 2015 zuwa 2023.