Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne shafin hada-hadar kudi na Binance?
- Marubuci, Angela Henshall
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, London
Binance shi ne babban shafin hada-hadar kudin kirifto a duniya da ake amfani da shi ta hanyar saye da sayarwa na wasu kadarorin intanet.
An yi kiyasin cewa akwai mutum miliyan 150 da ke amfani da Binance. Da farko kamfanin na da shalkwata a kasar China kafin daga baya ta koma Malta, duk da cewa an yi mata rajistar biyan haraji a tsibirin Cayman.
Ta yaya ake amfani da kudin kirifto?
A takaice a iya cewa kudin kirifto kudade ne na intanet. Ba a saka su a aljihu kamar sauran takardun kudi ko sulalla, su kudi ne da hannu ba ya iya taba su.
To sai dai duk da cewa ba ma iya ganinsu ko taba su, kudaden na da daraja.
Ana taskance kudaden kirifto a wani asusun ajiya na intanet da ake kira 'Wallet' da ake samu a wayar hannu ko kwamfuta, inda mai shi zai iya aika wa mutanen da ya sayi wani abu daga gare su. Haka kuma ana iya yin hada-hadar musayar kudi da su kamar yadda Binance ke yi.
Wane ne Changpeng 'CZ' Zhao?
Mutum mai janyo ce-ce-ku-ce da ya kirkiri kamfanin Binance, Changpeng Zhao, ya ajiye mukaminsa na shugaban Kamfanin a shekarar 2023 bayan ya amince da aikata almundahanar kudi.
A kan haka ne, a makon da ya gabata wani alkali a Amurka ya yanke hukuncin cewa Binance zai biya dala biliyan 4.3, daya daga cikin manyan tara da aka taba biya a tarihin Amurka.
Ma'aikatar shari'ar Amurka ta ci tarar kamfanin, tana mai cewa Binance na taimaka wa masu amfani da shi wajen ketare iyaka, lamarin da ke sa masu barna da 'yan ta'adda tura kudade cikin sauki.
An ga yadda kamfanin ya gudanar da hada-hadar kudi mai yawa a kasashen Siriya da Iran da kuma Rasha.
Hukumar hada-hadar hannayen jari ta Amurka ta ce kamfanin da kuma Zhao sun saba dokokin da ke kare masu zuba jari, don ya ci gaba da aiki a Amurka.
A yanzu, Richard Teng dan kasar Singapore ne shugaban kamfanin.
Me ya sa aka kama mutane a Najeriya?
A farkon wannan makon ne aka kama wasu manyan jami'an kamfanin Binance biyu a Najeriya bayan da suka shiga kasar. Sai dai Kamfanin bai yi wa BBC karin bayani game da kamen ba.
A ranar Talata gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso ya ce an yi hada-hadar dala biliyan 26 a kamfanin Binance a Najeriya daga mutanen da ba za a iya gano su ba.
Cardoso ya kuma yi kira ga hukumar yaki da rashawa ta Najeriya, da 'yansanda da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro su hada hannu wajen gudanar da bincike kan hada-hadar kudaden kirifto a kasar
Me ya sa batun ya taso a yanzu - Me gwamnati ke tunanin na faruwa?
Kamen da aka yi wa jami'an Binance na zuwa ne bayan haramta hada-hadar kamfanonin kirifto a Najeriya.
Hukumomi sun damu kan yadda ake amfani da kudin kirifto wajen aikata almundahanar kudi tare da karya darajar kudin kasar.
A watan Nuwamban 2022, Banince ya bai wa 'yan kasuwar Najeriya damar ajiye kudade tare da cire naira daga asusun ajiyarsu na Binance, inda hakan ke nufin za su iya sayar da naira a kan kudin kirifto kamar Bitcoin.
Cikin watannin da suka gabata, an yi ta zargin kamfanin Binance da kayyade farashin canjin kudin kasar. Zarge-zargen da mahukuntan kamfanin suka musanta.
Gwamnatin Najeriya ta yi ikrarin cewa kamfanin Binance ne ke kara ta’azzara matsalar karyewar darajar kudin kasar, ta hanyar yada-jita-jitar kayyade farashin dala, lamarin da ya sa naira ta fadi da kusan kashi 70 cikin dari na darajarta a watannin baya-bayan nan.
A makon da ya gabata ne Jaridar Financial Times ta ruwaito Bayo Onanuga, mataimaki na musamman ga shugaban Najeriya na cewa Binance ya kwace ayyukan Babban Bankin Najeriya na kayyade farashin kudin kasar.