Kasuwar bayan-fage da ake sayar da magungunan zubar da ciki a Honduras

Asalin hoton, Getty Images
Alkawarin mace ta farko Shugabar kasar Hunduras, Xiomara Castro, lokacin yakin neman zabe na yin garanbawul kan dokar kasar mai tsanani game da haihuwa cikin kwana 100 farko a ofis ta bayyana.
Shekara guda bayan nan ta sanar da cewa za a iya shan maganin hana daukar ciki a hukumance - amma ga wadanda aka yi wa fyade kawai. Da maraice Laura ta same mu, yayin da rana ke shirin faduwa.
Shekararta 25 a duniya, tana da cikin wata biyu sai dai ta ce ba ta shirya haihuwa ba.
"Wata biyu da suka gabata, na je na samu wani. Ban yi abin da ya kamata ba, karshe na dauki ciki," tana fada tana cije baki. "Yana da wuya na iya zama ni kadai ba tare da namiji ba. Rayuwata nake takankaina."
Tana zaune a Tegucigalpa babban birnin Honduras, wata kasa dake tsakiyar Nahiyar Amurka inda ake da dokoki masu tsauri kan haihuwa a duniya.
An hana shan magungunan daukar ciki a 2009 - amma yanzu an sassauta dokar ga matan da aka yi wa fyade. Zubar da ciki abu ne da ake yi wa hukunci da zaman gidan yari na shekara shida.
Amma daga baya Laura ta ji labarin wani magani na kansar ciki amma kuma ana zubar da ciki da shi. Lokacin da aka sa shi a gaban mata, yana sanya mata zubar da jini mai yawa, sai ya zubar da cikin baki daya.
Ta yanke shawarar shan wannan magani ta hannun wani dila Jose, wanda ta ce mutane da dama sa'anninta sun san shi a Tegucigalpa.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wata rana da yamma mun raka Jose zuwa wani wajen sayer da magani domin karbo maganin a wajen wani abokin hulda. Ya shaida mana cewa wata tsohuwar budurwarsa ce da take a asibiti take kawo masa.
Yace yana karbar kudi ne a hannu abokan huldarsa daidai da karfinsu. Makurar abin da yake karba shi ne lempira 7,000, kwatankwacin fan £230.
Yana iya kirga abokan huldarsa cikin sauki, saboda ba su da yawa.
"Dalibai, 'yan mata wadanda suka fara kwanciya da maza, matasa da tsofaffin mata, da matan da suka samu ciki bayan kwanciya .... mafi yawansu mata ne. Yawanci maza ne ke daukar nauyin haka."
Jose yana sayer da maganin hana daukar ciki amma ba shi da masu saya da yawa, yayin da ake da wani wajen sayer da magani ba bisa ka'ida ba a Tegucigalpa da ya yi fice. Kuma mun tabbatar da hakan ta yadda muka je muka sayi mahanin da kanmu kan lempira.
Wata kungiya da ke aiki da Majalisar Dinkin Duniya ta ce akan samun zubar da ciki mai hadari tsaknin 51,000 zuwa 82,000 a Honduras ko wacce shekara, kuma Jose ya ce ko da yaushe yana kan aiki.
Yayin da muka tuntube shi, sai yace yasan abin da yake yi ba ya kan daidai kuma ya amsa ba shi da horo kan harkokin magani. Amma duk da haka shi ne ke aikin ba da maganin, kuma ya bayyana mana sunayen wasu manyan abokan huldarsa da suka yi suna a kasar.
A wasu lokutan suna bayar da ruwan gishiri da domin taimakawa mtan su farfado daga zubar da jinin da suke.
Sugaba Xiomara Castro taki tattaunawa da BBC, sai dai ministan lafiya Dr Jose Manuel Matheu ya amince ya tattauna da mu kan yadda aka amince da shan magungunan hana daukar ciki.
Mun tambaye shi me yasa maganin sai wadanda aka ci zarafi ta hanyar lalata kawai.
"Ba kokarinmu mu rika tallata wadannan magungunan ba ne, ba wai rashawa muke son nunawa ba a wannan fanni, Ina amfani da wannan kalmar kai tsaye cewa wadanda aka ci zarafi ne kawai za a yarda su yi amfani da shi. Amma duk wadanda suka je suka yi ciki na banza, sai su girbi abin da suka shuka."
Amma ga mata irin su Laura da suke je suka yi ciki a kan titi sai su tafi da yaransu, kuma ba za a sayar musu da magani ba.
Amma ta ce yanzu tana shan maganin Jose duk da hadarin da yake tare da shi.
"Sukan zubar da ciki ba bisa ka'ida ba, kuma zafin hakan ya ninka sau uku idan aka kwatanta da wanda ake zubarwa hukumance," ta fada tana karkarwa.
"Ba ni da tabbacin cewa ba zan mutu ba, amma ba ni da wata hanyar sama da wannan. na san zuban da ciki bai dace ba, amma idan za a ba ni dama zan sha magani.










