Alvarez zai ci gaba da taka leda a Man City - Guardiola

Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana Julian Alvarez a matsayin “Ɗan wasanmu ne” yayin da yake amsa tambayoyi game da makomar ɗan wasan Argentina.

An tambayi makomar Alvarez, wanda ake alakanta mai shekara 24 da cewar zai koma Atletico Madrid, bayan da City ta ci Chelsea 4-2 a filin wasa na Ohio.

"Babu abin da zan ce. Alvarez zai ci gaba da taka mana leda idan ya kare hutu, bayan Copa America da Olympic da ya buga," in ji Guardiola.

Alvarez, wanda kwantiraginsa a City zai kare a karshen kakar 2028, ya buga wa Argentina gasar Olympics a Paris, ya kuma ce kafin Faransa ta fitar da su zai yanke shawarar makomarsa.

Guardiola ya kara da cewa: "Na tabbata idan ya dawo zan rungume shi tare da taya shi murnar lashe kofin Copa America da buga Olympics, kuma za mu fara aiki tare. Wannan sh ne gaskiya.

"Abin da ke faruwa a halin yanzu, ina da abubuwa miliyan dubu da nake yin tunani game da kungiyata.

"Mako mai zuwa za mu buga Community Shield da Manchester United a Wembley. Sai kuma mu kara da Chelsea a Stamford Bridge, wannan ne kawai damuwata."

City ta kammala wasan sada zumunta a Amurka ba tare da ƴan wasanta sun ji rauni ba, amma ya maye gurbin Rico Lewis a karawar da Chelsea da mai tsaron gida, Ederson saboda ɗan buguwa."

Ana sa ran ƴan wasan biyu za su murmure su kuma fuskanci United a Community Shield a mako mai zuwa, kafin a fara gasar Premier da wasa da Chelsea a Stamford Bridge.