Me ya sa Pakistan ke korar ƴan Afghanistan?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Yama Bariz
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Aiko rahoto daga, Torkham border crossing
- Lokacin karatu: Minti 3
Pakistan ta mayar da sama da ƴan Afghanistan 19,500 a wannan watan, daga ciki sama da 80,000 da suka fice kafin wa'adin da aka ɗaukar musu ya ci ranar 30 ga watan Afrilu in ji Majalisar Ɗinkin Duniya.
Pakistan ta ƙara ƙaimi wajen fitar da ƴan Afghanistan wadanda ba su da izinin zama da waɗanda aka bai wa izinin zama na wucin-gadi. Pakistan ɗin ta ce ba za ta iya ɗaukar nauyin su ba.
A kowacce rana ana mayar da tsakanin iyalai 700 zuwa 800, jami'an Taliban sun ce ana sa ran mutane miliyan biyu za su dawo a watannin masu zuwa.
Ministan harkokin wajen Pakistan Ishaq Dar ya kai ziyara Kabul ranar Asabar don ganawa da jami'an Taliban. Takwaransa Amir Khan Muttaqi ya bayyana damuwarsa game da mayar da ƴan ƙasar gida.
Wasu daga cikin ƴan Afghanistan ɗin da aka kora kuma yanzu haka suke kan iyaka sun ce a Pakistan aka haife su bayan iyalansu sun tsere wa rikici.
Sama da ƴan Afghanistan miliyan 3.5 ne suke rayuwa a Pakistan, Hukumar Kula da Masu Ƙaura ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kusan mutane 700,000 ne suka zo bayan Taliban ta karɓe iko a shekara ta 2021. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce rabinsu ba su da izinin zama.
Pakistan ta karɓi ƴan Afghanistan sakamakon yaƙin gomman shekaru, amma gwamnati ta ce yawan yan gudun hijira na barazana ga tsaro kuma ya na haifar mata da matsi.
A baya-bayan nan an samu ƙaruwar rikici a iyakoki tsakanin jami'an tsaron bangarorin biyu. Pakistan ta ɗora alhakin lamarin kan mayaƙan da ke zaune a Afghanistan amma Taliban ta ƙaryata.
Pakistan ta ƙara wa ƴan Afghanistan da ba su da izinin zama lokacin ficewa har ranar 30 ga watan Afrilu.
A mashigin iyakar Torkham kuwa, wasu ƴan Afghanistan da aka kora sun shaida wa BBC yadda suka bar Afghanistan shekaru da dama ko kuma yadda ba su taɓa rayuwa a can ba.
Sayed Rahman wani matashi ya ce ''gaba ɗaya rayuwata a Pakistan na yi ta a can na yi aure, me ake so in yi yanzu?''
Saleh wani uba n mai a ƴaƴa uku mata, yana cikin damuwa game da yadda ake rayuwa ƙarkashin Taliban. ‘Yaƴansa na zuwa makaranta a lardin Punjab da ke Pakistan, amma a Afghanistan an hana 'yanmata wadanda zarce shekaru 12 zuwa makaranta.
"Ina son ƴaƴana su yi karatu. Ba na son a yi asarar karatun da suka yi,'' ya ƙara da cewa," kowa na da damar neman ilimi."
Wani mutum ya shaida wa BBC cewar ''ƴaƴanmu ba su taɓa ganin Afghanistan ba, ni ma ban san ya take yanzu ba, za mu samu shekara guda kafin mu saba sannan mu samu aikin yi, ba mu da mafita."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A iyakar, maza da mata na fita ta kofofi daban-daban, yayin da jami'an tsaron Pakistan da Afghanistan ke sanya ido. Daga cikin wadanda suke komawar akwai dattijai da dama har da wani mutum da ake ɗauke da shi kan gadon ɗaukar majinyata.
Motocin sojoji na ɗaukar kaya na jigilar iyalai daga iyakar zuwa wasu matsugunan wucin-gadi. Wadanda suke daga yankuna masu nisa sukan zauna jiran motocin da za su mayar da su yankunansu.
Iyalan sun yi dandazo ƙarkashin hotuna don kauce wa yanayin zafi ko ƙura, kayan agaji sun yi ƙaranci yayin da ake samun hatsaniya saboda ƙarancin wurin zama.
Hedayatullah Yad Shinwari mamba a kwamitin kuɗi da Taliban ta kafa a sansanin ya ce ana ba su kuɗin Afghanistan 4,000 zuwa 10,000, wanda ke daidai da euro 41 zuwa euro 104 daga hukumomin Afghanistan.
Korar jama'a ta zama matsin lamba tattalin arziki Afghanistan mai mutane kusan miliyan 45.
Bakht Jamal Gohar shugaban hukumar kula da harkokin yan gudun hijira ta Taliban ya bayyana cewar “mun warware wasu matsaloli a tsakaninmu, amma shigowar mutane da dama za ta haifar da matsaloli.” Ya ƙara da cewa wadannan mutanen sun fice tun shekaru da dama da suka gabata sun bar kayansu wasu daga cikinsu ma yaƙin da aka yi shekaru 20 da suka gabata ya lalata musu gidaje.
Kusan dukkan iyalan sun shaida wa BBC cewar dakarun da suke tsaron iyakar Pakistan sun taƙaita abin da za su iya wucewa da shi, abin da ƙungiyoyin kare haƙƙin ƴan’adam suka yi Allah Wadai da shi.
A cewar Chaudhry Pakistan "ba ta da wani tsari da ya hana ƴan gudun hijirar Afghanistan kwashe kayan gidajensu".
Wani mutun zaune a gefen hanya cikin rana ya ce ƴaƴansa sun roƙi a bar su su zauna a Pakistan inda aka haife su. An ba su izinin zama na wucin-gadi amma aikinsa ya ƙare a watan Maris.
"Yanzu ba za mu taɓa komawa ba. bayan abin da aka yi mana" in ji shi.
Ƙarin rahoto daga Daniel Wittenberg da Mallory Moench.












