Vincic ne zai busa wasan Real da Milan a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon kafar Turai ta bayyana Slavko Vincic a matakin wanda zai yi rafli a Champions League tsakanin Real Madrid da Milan ranar Talata.
Wannan shi ne karo na biyu da alkalin wasan ɗan kasar Slovenia zai busa wasan Real Madrid a gasar ta zakarun Turai.
Haka kuma wannan shi ne wasa na huɗu da Real Madrid za ta buga a Champions League a bana, inda za ta karɓi bakuncin Milan a Santiago Bernabeu.
Tun farko Real ta doke Stuttgart, sannan ta yi rashin nasara a Lille, sai ta doke Borussia Dortmund a babbar gasar zakarun Turai ta kakar nan.
Vincic shi ne ya busa wasan karshe da Real Madrid ta doke Borussia Dortmund 2-0 a kakar da ta wuce, wadda ta ɗauki Champions League na 15 jimilla.
Da zarar Real ta kammala wasa da Milan, za ta mayar da hankali kan La Liga, inda za ta karɓi bakuncin Osasuna ranar Asabar 9 ga watan Nuwamba.
Daga nan Real Madrid za ta je gidan Leganes, domin buga babbar gasar tamaula ta Sifaniya ranar Lahadi 24 ga watan Nuwamba.
Real mai wasa 11 a La Liga tana mataki na biyu a teburi da tazarar maki tara tsakani da Barcelona, wadda ta yi fafatawa 12 a gasar ta bana.










