Tottenham na son Palhinha, Sancho na son barin Man Utd

RB Leipzig na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin Rasmus Hojlund

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Tottenham na tattaunawa da Bayern Munich kan ba da aron ɗan wasan Portugal Joao Palhinha, mai shekara 30, yayinda suke kokarin ganin tsohon ɗan wasan tsakiya na Fulham ya koma Firimiya. (Athletic)

RB Leipzig na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin Rasmus Hojlund kuma Manchester United na iya amfani da ɗan wasan mai shekara 22 na Denmark wajen musayarsa domin cimma yarjejeniya da ɗan wasan gaba a Slovenia, Benjamin Sesko mai shekara 22. (Athletic)

Ɗan wasan Manchester United Jadon Sancho mai shekara 25, ya shirya karɓan albashin da za a zabtare masa kashi 50 cikin 100 na abin da yake samu domin koma taka leda a Borussia Dortmund. (Bild - in German)

Ana saran Chelsea ta gabatar da tayi kan ɗan wasan Manchester United, Alejandro Garnacho, mai shekara 21, kafin a rufe kasuwar cinikin 'yan wasa. (Telegraph)

Ɗan wasan tsakiya a Ingila mai shekara 20, Nico O'Reilly zai sanya hannu a sabon kwantiragi da Manchester City bayan watsi da tayin Bayer Leverkusen na Jamus. (Fabrizio Romano)

Ƙungiyar Girona ta La Liga ta amince da yarjejeniyar ɗaukan ɗan wasan baya a Manchester City da Brazil, Vitor Reis mai shekara 19, a matsayin aro. (Fabrizio Romano)

Manchester City na son daidaitawa da ɗan wasan nan mai shekara 19, Claudio Echeverri domin tafiya zaman aro a Girona, yayinda ake tattaunawa tsakanin ɗan wasan na Argentine da ƙungiyar ta Sifaniya. (Fabrizio Romano)

Ƙungiyar Liverpool da Bournemouth ba za su daga kafa fa a farautar ɗan wasan Faransa, da Saudiyya ke hari, Nathan Zeze mai shekara 20. (TBR Football)

Chelsea na son ɗan wasan Club Brugge, Ardon Jashari amma ɗan wasan mai shekara 23 yafi son ya je AC Milan. (Sacha Tavolieri)

Everton zata jira satin karshe kafin gabatar da tayi kan ɗan wasan Juventus da Brazil, Douglas Luiz mai shekara 27. (GiveMesport)