Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko fatan Najeriya na zuwa gasar kofin duniya ta 2026 zai cika?
- Marubuci, Emmanuel Akindubuwa
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa, Lagos
- Lokacin karatu: Minti 3
Ana zaman rashin tabbas, yayin da masoya ƙwallon ƙafa a Najeriya ke jiran hukuncin da hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa za ta yake kan ƙorafin da Najeriya ta shigar kan zargin DR Congo da yin amfani da ƴan wasan da ba su kamata aba a wasanni neman gurbin gasar cin kofin duniya ta 2026.
Tawagar Congo ta cire Najeriya ne a bugun fenariti a watan Nuwamba domin samun gurbi a wasannin neman gurbi na duniya da za a buga.
A watan Disamba ne Najeriya ta shigar da ƙorafi, inda ta zargin tawagar Leopards ta DR Congo da yin amfani da ƴan wasa Aaron Wan-Bissaka da Axel Tuanzebe - waɗanda dukkanin su sun taɓa buga wa Ingila wasa a tawagar matasa, inda Najeriya ta ce ba su cancanta ba domin dokar ƙasar Congo ba ta amince da ƴanwasa da suke da takardar zama ɗan ƙasa na ƙasashe biyu ba.
Yayin da wani sashe na magoya bayan tawagar Najeriya ke fatan ganin ƙasar ta samu wata damar, wasu kuma na ganin cewa tamkar babu adalci idan aka bai wa Najeriya dama a kan DR Congo.
Fifa ta tabbatar da cewa tana nazari kan ƙorafin, to amma ba ta sanar da ranar da za ta yi nazari ko kuma sanar da hukuncin da ta yanke ba, kuma tuni hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Najeriya - NFF - ta musanta raɗe-raɗin cewa an yi watsi da ƙorafin nata.
"Duk wani batu da ke cewa an yanke hukunci ba gaskiya ba ne," in ji daraktan yada labarai na NFF, Demola Olajire.
"Fifa ba ta faɗa mana, ko hukumar ƙwallon ƙafa ta Congo game da wani hukunci ba."
A lokacin da Najeriya ta shigar da ƙorafi, shugaban NFF Mohammed Sanusi ya zargi DR Congo da karya dokokin Fifa.
Bayan wasannin neman gurbi, Tuanzebe da Wan-Bissaka sun kuma buga wa tawagar DR Congo a gasar cin kofin Afirka ta 2025 a Moroko.
"Dokar ƙasar Congo ta ce ɗan wasa ba zai zamo mai takardar zama ɗan ƙasa biyu ba, amma wasu daga cikin ƴan wasansu na da fasfo na ƙasashen Turai da kuma Faransa," in ji Sanusi.
"Abin da muka lura shi ne an yaudari Fifa wajen amincewa da su."
Hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Congo ta yi watsi da zarge-zargen na Najeriya, inda ta bayyana matakin a matsayin wani "yunƙuri na samun nasara ta bayan gida".
Tawagar Congo za ta kara da ko dai ƙasar New Caledonia ko Jamaica a karawar da za yi ta wasannin neman gurbi tsakanin ƙasashen duniya a watan Maris.
Wanda ya yi nasara a wasan zai shiga cikin jerin ƙasashe 48 da za su buga gasar kofin duniya, a rukunin K, tare da ƙasashen Portugal da Uzbekistan da kuma Colombia.
Wane irin hukunci Fifa za ta yanke?
Waɗannan su ne matakan da Fifa za ta iya ɗauka idan ƙorafin ya isa gare ta a hukumance:
- Kora: Idan Fifa ta yanke hukuncin cewa dalilan Najeriya ba su da ƙarfi za ta iya watsi da ƙorafin, ta kuma ƙyale DR Congo ta ci gaba da wasan neman gurbin gasar cin kofin duniya.
- Bincike da yin hukunci: Fifa za ta iya yin bincike game da ƙorafin, idan ta gano cewa akwai saɓa ƙa'ida wajen tantance ƴan wasa, za ta hukunta hukumar (ta hanyar cin tara ko gargaɗi) ba tare da sauya sakamako ba.
- Yin hukunci: Idan abin ya yi ƙamari, Fifa ko kuma Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka za su iya sokewa ko kuma ƙwace maki daga mai laifi a miƙa wa mai ƙorafi ko kuma a cire wa ƙasar maki daga cikin wasannin da aka yi na cikin rukuni. A baya, akan yi wannan hukunci ne idan aka gano ƙarara cewa an take doka, ko dai ta hanyar bayar da bayanan ƙarya ko kuma sauya wasu bayanai.
Ga Najeriya kuwa abin a bayyane yake.
Duk da cewa Najeriya ta lashe lambar tagulla a gasar cin kofin Afirka ta 2025, wanda ya sanya ta ƙara ɗabbaƙa kanta a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da suka gawurta a ɓangaren ƙwallon ƙafa a nahiyar, amma abin da ya fito fili shi ne, a halin yanzu, Najeriya ba za ta je gasar cin kofin duniya ba, in dai ba wani abu ya sauya ba.