Yadda Ribadu ya yi martani ga El-Rufai kan zargin shigar da guba Najeriya

Lokacin karatu: Minti 2

Ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya mayar da martini ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai wanda ya nemi bahasi kan shiga da wata guba mai haɗari cikin ƙasar.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya zargi ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, a ƙaƙashin jagorancin Mallam Nuhu Ribadu, da sayo kimanin kilogiram 10 na wani sinadari mai haɗari da ake kira 'thallium sulphate', daga ƙasar Poland.

El-Rufai ya yi wannan zargin ne a cikin wata wasiƙa da ya aike wa ofishin Ribadu, wadda kuma ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce jagororin adawar ƙasar na neman ƙarin haske game da wannan batun.

Saƙon na shi ya ce "Sinadarin thallium na da matuƙar haɗari kuma sinadari ne da ba kasafai ake samunsa ba''.

Ya ce ya aike da wasiƙar ne domin ya nemi cikakkun bayanai kan yadda aka sayo sinadarin, yayin da ya nuna barazanar da irin wannan sinadari ka iya yi kan lafiyar al'umma.

El-Rufai ya nemi ofishin Ribadu ya yi bayanin dalilin shigo da sinadarin da kuma amfanin da za a yi da shi.

"Ina so in jaddada cewa ba ni da wata manufa ta daban na yin waɗannan tambayoyi, na yi su ne don in tabbatar da cewa an bi tsarin da ya kamata, kuma an bi matakan da suka dace na kare lafiya.''in ji shi

Amma rahotannin da jaridun Najeriya suka wallafa a ranar Lahadi da dare na cewa ofishin mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro ya yi martani ga Malam El-Rufai, inda ya musanta zargin da tsohon gwamnan jihar Kaduna ya yi.

Ofishin mai bayar da shawara kan harkokin tsaron ya kuma buƙaci El-Rufai ya gabatar da hujjojin da yake da su game da batun ga hukumar tsaron DSS domin gudanar da cikakken bincike.

Jaridun Najeriya sun ruwaito cewa wani jami'i a ofishin Malam Nuhu Ribadu, Birgediya-Janar OM Adesuyi ne ya rubuta wasika a madadin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaron.

Wasiƙar ta ce "Ina wakiltar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, kuma bayan miƙa saƙon gaisuwar shi gare ka, ina kuma tabbatar maka cewa saƙon ka na ranar 11 ga watan Faburairu mai neman a yi maka bayan ikan zargin sayen kimanin kilogiram 10 na gubar Thallium Sulphate.

"Wasiƙarka ta kuma nuna cewa shugabannin ƴan adawa na da bayanai game da sayen wannan guba. Saboda haka, an umarce ni da shaida maka cewa ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro bai sayo wannan guba ba, kuma ba shi da aniyar yin hakan a nan gaba.

"Haka nan kuma, an bani wani umarnin na sanar da kai cewa an gabatar da wannan batu ga hukumar DSS domin ta ci gaba da bincike. Ya kai maigirma, da sauran masu tarayya da kai cikin wannan zargi, waɗanda ke da bayanai game da batun, ku sani cewa hukumar tsaro ta DSS za ta gayyace ku domin gabatar da shaidun da za su taimaka wajen gudanar da cikakken bincike da zaƙulo gaskiyar lamarin.

Jaridun Najeriya da dama sun ruwaito cewa da farko ba a samu wanda zai amsa wasikar da ofishin mai bai wa shugaban Najeriyan kan tsaro ya aika wa tsohon gwamnan jihar Kaduna ba, inda masu gadi shuka ce shugaban su baya nan, don haka ba su da iko sanya hannu domin karɓar saƙon, amma daga baya aka sake mayar da wasikar kuma masu gadi suka karɓa.