Ƙasashe 10 da ba su taɓa zuwa gasar Afcon ba

Lokacin karatu: Minti 1

A daidai lokacin da hankali ya fara komawa kan gasar cin kofin Afirka da ake afatawa a Morocco hankali ya fara komawa kan lissafe-lissafen yadda gasar za ta kaya.

Wannan ne karo na 35 da ake fafata gasar tun daga watan Fabrailun shekarar 1957 da aka fara babbar gasar tamaular ta nahiyar Afirka.

Ƙasashe 24 ne ke fafatawa a gasar ta Acon ta bana wadda aka fara daga ranar 21 ga watan Disamban 2025 zuwa 18 ga watan Janairun 2026

To sai dai akwai wasu ƙasashe guda 10 da ba su sami gurbin shiga gasar ba ko kuma ma ba su taɓa zuwa gasar Afcon ɗin ba a tsawon rayuwarsu. Ƙasashen kuwa su ne kamar haka:

  • Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
  • Chad
  • Djibouti
  • Eritrea
  • Eswatini
  • Lesotho
  • São Tomé and Príncipe
  • Seychelles
  • Somalia
  • Sudan ta Kudu

An karkasa tawagar ƙasashe 24 da ke fafatawa a gasar ne zuwa rukunoni guda shida, inda kowane rukuni ke ɗauke da tawagar ƙasashe guda huɗu a cikinsa kuma tawagogin za su fafata a tsakaninsu domin fitar da guda biyu da suka yi zarra a matakin farko.

Ƙasashen ne za su tsallaka zuwa zagaye na biyu ko kuma zagayen da ake kira ƴan 16, inda za a fara fafata kifa ɗaya ƙwale.

Ƙasar Morocco ce ta karɓi baƙuncin gasar ta bana, inda ake tunanin za a nishaɗu ganin irin yadda ƙasar ta zuba jari matuƙa a harkar wasanni, musamman ma harkar ƙwallon ƙafa, inda har ta samu shiga cikin ƙasashen da za su yi haɗaka wajen karɓar baƙuncin gasar cin kofin duniya ta 2030.

Daga cikin sauyin da aka samu a gasar ta bana, akwai canjin lokaci, inda maimakon tsakanin watan Yuni zuwa Yuli da aka saba, a bana za a fara gasar ne a watan Disamba, matakin da aka ɗauka saboda shirye-shiryen gasar cin kofin duniya da ake yi.

Kuma wannan shi ne a karon farko da za a yi gasar cin kofin Afirka a lokacin da ake bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara.