Me wasiƙar da Nnamdi Kanu ya rubuta wa Donald Trump ta ƙunsa?

Me wasiƙar da Nnamdi Kanu ya rubuta wa Donald Trump ta ƙunsa?

..

Asalin hoton, Reuters

Nnamdi Kanu, jagoran ƙungiyar da ke fafutukar kafa ƙasar Biafra, IPOB wadda gwamnatin Najeriya ta haramta, wanda kuma kotu za ta yanke wa hukunci ranar 20 ga watan Nuwamban 2025 bisa tuhumar cin amanar ƙasa, ya rubuta wa shugaban Amurka, Donald Trump wasiƙa, kamar yadda sashen BBC Igbo ya rawaito.

A cikin wasiƙar mai shafi huɗu, jagoran haramtacciyar ƙungiyar ta IPOB ya yi bayani kan yadda shari'ar da ake yi masa ta fara da kuma halin tsaro da ake ciki a yankudu maso gabashin Najeriya, inda ya fito.

Nnamdi Kanu ya yi amfani da damar wajen tattauna abubuwa da dama da suka faru tsakaninsa da gwamnatin Najeriya tun lokacin da ya fara fafutukar kafa ƙasar Biafra.

Ya nemi Donald Trump da "ya yi bincike dangane da kisan da ake yi a kudu maso gabashin Najeriya da wasu al'amuran na daban."

Zarge-zargen Nnamdi Kanu kan jami'an tsaro

..

Asalin hoton, Getty Images

A wasiƙar, Nnamdi Kanu ya yi zargin cewa jami'an tsaron Najeriya sun yi yunƙurin kashe shi har sau huɗu.

Kanu ya kuma ƙara da cewa kisan da ake yi a Najeriya na faruwa a jihohin Benue da Kogi da kuma yankunan arewaci "sakamakon ayyukan ta'addanci".

Sai dai kuma ya ce kisan da ke faruwa a kudu maso gabashin ƙasar ya sha bamban, inda ya ce jami'an tsaro ne babbar matsala a yankin, inda ya yi zargin cewa "jami'an tsaron na ɗora alhakin kisan da ake yi ga mutanen da suke kashewa."

Hujjojin Nnamdi Kanu

A wasiƙar tasa, Nnamdi Kanu ya lissafa wasu lokuta da ya ce jami'an tsaro sun kashe mutanen da ya bayyana da Kiristoci-Yahudawa a Najeriya.

  • Ranar bikin Biafra - Mayu 30, 2016.
  • Waɗanda aka kashe a makarantar National High School Aba - Fabrairu 9, 2016
  • Waɗanda aka kashe a farmakin Operation Python Dance 2 - Satumba 12 - 14, 2017
  • Waɗanda aka kashe a Obigbo, Port Harcourt - Oktoba, 2020

Nnamdi Kanu ya bayar da alƙaluman da manzon Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman, Agnes Callamard da Amnesty International da sauran alƙaluma.

A wane hali Nnamdi Kanu yake?

Tun dai 2021 ne Nnamdi Kanu ke tsare a hannun gwamnatin Najeriya kuma yake fuskantar shari'ar kan cin amanar ƙasa.

Halin da Nnamdi Kanu yake ciki a halin yanzu ya sa ƴan Najeriya da dama dasa ayar tambaya cewa shin daga ina jagoran na IPOB ya rubuta wasiƙar?

A ranar 20 ga watan Nuwamban 2025 ɗin nan ne wata babbar kotu da ke zamanta a Abuja za ta yanke wa Nnamdi Kanu hukunci, bayan gaza kare kansa da kotu ta ba shi damar yi.

Kotun ce dai ta bai wa jagoran haramtacciyar ƙungiyar ta IPOB da ya bayyana a gaban kuliya ranar Juma'a ta 7 ga watan na Nuwamba domin kare kansa da kansa ba tare da lauyoyi ba.

Kotu ta saka ranar yanke wa Nnamdi Kanu hukunci
..
Lokacin karatu: Minti 3

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta saka ranar 20 ga watan Nuwamba domin yanke wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu hukunci.

Alƙalin Kotun Maishari'a, James Omotosho ne ya bayyana haka a zaman kotun na ranar Juma'a kan shari'ar da ake yi wa Mista Kanu kan zargin ta'addanci.

Maishari'a Omotosho ya ɗauki matakin ne bayan da Nnamdi Kanu ya kasa fara kare kansa bayan kwana shida da kotun ta ba shi domin yin hakan.

Kotun ta ce bayan Kanu ya gaza amfani da damar da aka ba shi domin kare kansa daga tuhumar da ake yi amsa, bai kamata ya ci gaba da iƙirarin da yake yi cewa an hana damar da kundin tsarin mulki ya ba shi na jin bahasinsa.

Nnamdi Kanu dai ya nemi ya kare kansa bayan korar lauyoyinsa, idan har kotu ta amince.

Idan bai kare kansa ba, kotu za ta rufe sauraron shari'ar tasa sannan kuma ta yanke masa hukunci bisa hujjojin da masu tuhumar sa suka gabatar mata.