Wane tasiri korar jami'an tsaro daga aiki ke yi a Najeriya?

Sojoji a birnin Legas

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Ƙwararru a harkar tsaro na jan hankalin Najeriya dangane da yawaitar korar jami'an tsaro daga aiki, bayan kwashe shekaru suna samun horo da tattara bayanan sirri.

A ranar Talata ne hukumar tsaro ta DSS ta ƙasar ta sanar da korar ma'aikatanta guda 115 daga aiki duk da dai hukumar ba ta fito fili ta faɗi dalilan korar ba, amma ta ce ta yi hakan ne sakamakon wasu sauye-sauye da take yi.

A makon da ya gabata ne rahotanni suka karaɗe Najeriya kan raɗe-raɗin sallamar wasu manyan sojoji fiye da 100 sakamakon sauyin manyan hafsoshin tsaro a ƙasar da ya biyo bayan zargin kitsa juyin mulki.

Ana dai ganin cewa korar ma'aikatan tsaron daga aiki na da tasiri sosai ga tsarin tsaron ƙasar.

'Ba laifi ba ne korar mai laifi daga aiki'

Dakta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, da ke nazari kan harkokin tsaro a yankin Sahel ya ce kamar kowane ma'aikaci a Najeriya, shi ma jami'in tsaro idan ya yi laifi za a iya korar sa.

"Babu shakka idan jami'in tsaro ya yi laifin da ya saɓa yarjejeniyar aiki da suka saka hannu tsakaninsa da wanda yake yi wa aiki, doka ta bayar da damar a kore shi kamar kowane ma'aikaci. To amma idan ka dubi irin ƙwarewarsu da ilimin da suke da shi to irin wannan ne muke jan hankalin gwamnati a kai."

Dakta Kabiru Adamu ya ce korar ma'aikatan da hukumar DSS ta yi shi ne abin da ya fi tayar musu da hankali.

"Akwai yiwuwar sun aikata laifin da za a kore su. Wannan ba laifi ba ne. Amma yadda hukumar ta wallafa hotunansu. Wannan gaba ɗaya an ɓata musu rayuwarsu domin hakan zai iya shafar tunaninsu."

"Sannan akwai abin da a sashen bincike da ake kira "counter espionage" da ƙasashe ke ɗauka na hana bazuwar bayananta na sirri. To bayyana hotunansu zai bai wa ƙasashen da ke hamayya da Najeriya damar iya amfani da su waɗannan jami'an wajen tatsar bayanan da za a iya yi wa ƙasa zagon ƙasa," in ji Dakta Kabiru.

Hanyoyi uku na amfana daga waɗanda aka kora

Dakta Kabiru Adamu ya lissafa wasu hanyoyi guda uku da ya ce ya kamata hukumomin tsaro su bi domin hana tsoffin jami'an tsaron su shiga hannun masu yi wa tsarin tsaron ƙasar zagon ƙasa.

  • Ɓangaren ƙwararru: Wannan wani ɓangare ne da ake kafawa na ƙwararru da ake kira "thinktank" domin amfana daga basira da ƙwarewar da manyan jami'an tsaro da aka kora ko aka yi wa ritaya daga aiki ta yadda za su taimaka da ƙwarewarsu wajen tsare-tsaren ciyar da ƙasar gaba.
  • Sake tunaninsu: Wannan kuma wata dabara ce ta sake amfana daga ƙwarewar matsakaita ko ƙananan jami'an tsaro ta hanyar sake ba su horo da yi musu afuwa sannan kuma a saka su a wani tsarin tsaro na daban wanda ba na gwamnati ba wanda ake kira da 'Industrial Security'.
  • Bibiya: Wannan ma yana da muhimmanci samun alƙaluman jami'an da aka kora ko aka yi wa ritaya domin sanin wurin da suke da haƙiƙanin abin da suke yi ta hanyar bibiyar su. "Wani abu mai tayar da hankali shi ne yanzu babu irin waɗannan alƙaluman waɗanda suka bar aiki da kuma abin da suke yi," in ji Kabiru Adamu.