Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda mutum zai iya gane warin jikinsa
- Marubuci, Novelia Wiley
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Shin za ka iya gane shekarun mutumin da ke zaune a gefenka ta hanyar warin jikinsa?
Zai iya yiwuwa mutumin yana sanye da turare, amma duk da haka za ka iya gano shekarunsa ta hanyar warin jiki.
Ta hanyar bincike, na gano yadda ake gano hakan.
Shi dai warin jiki ya bambanta tsakanin kowane mutum. Amma kuma yana sauyawa yayin da mutum ke girma.
Wannan na faruwa ne ba kawai saboda muhallin da mutum ke zama ba, har ma da yadda yake cuɗanya da al'umma.
'Yadda iyaye ke gane warin jikin jarirai'
Lokacin da mutum ke ƙarami, warin jikinsa ba ya fitowa sosai saboda rashin aikin gaɓoɓin da ke fitar da zufa yadda ya kamata da kuma ƙarancin ƙananan halittu da ke rayuwa a fatar mutum.
Amma duk da haka, iyaye na iya tantance warin jikin ƴaƴansu ƙanana.
Wannan warin jiki na ƙara danƙon soyayya da ƙauna tsakanin iyaye da ƴaƴansu.
Kuma hakan na rage damuwa ga iyaye, yayin da suke ƙoƙarin sanya yaran nasu farin ciki, domin warin jikin ƙananan yara na da jan hankali sosai.
Sai dai kuma masu jegon da kan yi fama da damuwa sanadiyyar haihuwa, ba su iya tantance warin jikin jariransu.
Sauyawar warin jiki
A lokacin balaga, warin jikin mutum kan sauya lokaci zuwa lokaci. Wannan na faruwa ne sanadiyyar sinadaran da jiki ke fitarwa waɗanda ke haɓɓaka gaɓoɓin saduwa, waɗanda su kuma ke haɓɓaka aikin ɓangaren fatar jiki da ke samar da zufa da kuma maiƙo.
Yawancin waɗannan gaɓoɓi na samar da ruwa da kuma gishiri.
Sinadaran Apocrine, masu samar da maiƙo da zufa na fitar da wani wari, wanda ya sha bamban ga kowane mutum.
Sinadarn su ne ke samar da maiƙon da ke sanya fatar kai da ta jiki laushi. Sai dai a lokacin da suka cakuɗa da ƙananan ƙwayoyin halittu, sai su riƙa fitar da warin jiki da zai iya damun mu.
Yayin da yaran da ke tasowa ke fitar da wani wari, warin kan canza a lokacin da suka balaga, kuma warinsu na asali kan ɓace, wanda hakan ke sanyawa warin ya sha bamban da wanda iyayensu suka sani tun asali.
Ta yaya za ka gane warin jikinka?
Maiƙon da fatar mutum ke fitarwa kan ƙaru a lokacin balaga.
Duk da cewa kuma takan ragu yayin da muke ƙara tsufa, kowane ɗan'adam na da nashi warin jikin da ya sha bamban da na saura.
Wannan ya dogara ne da abubuwa da dama, kamar abincin da mutum ke ci, da aikin wahala, da sinadaran jiki, har ma da yanayin fatar mutum.
Gaɓoɓin da ke tantance warin jikin na ɗan'adam na da ƙoƙari sosai wajen gano bayanai game da shi kansa, musamman a wuri mai duhu ko kuma wuraren da yake da wahala mutum ya gani ko ya ji abin da ake faɗa.
Hakan na da matuƙar muhimmanci wajen zaɓen abokin/abokiyar zama ko kuma bambance jinsin mutum.
Me yake faruwa idan muna ƙara shekaru?
Yayin da muke ƙara daɗewa a duniya, fatar jikinmu na saki saboda raguwa gam ɗin da ke riƙe fata.
Hakan na rage aikin ɓangarorin fatarmu da ke samar da zufa da kuma maiƙo.
Wannan ke sanyawa jikin tsofaffi bai cika riƙe zafi ba.
Wannan kan rage ayyukan sinadaran da ke a fatar jikin ɗan'adam, sai ya haifar da raguwar sinadarin Vitamin E, wanda hakan ke rage yawan iska daga jiki.
Waɗannan abubuwa ne ke haɗuwa suna sauya yanayin warin jikin mutum a lokacin da ya zarce shekara 40 a duniya.