Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Al-Hilal na son maye gurbin Neymar da Ronaldo, Manchester United na zawarcin Goretzka
Al-Hilal na duba yiwuwar soke kwantiragin dan wasan gaba na Brazil Neymar a watan Junairu, Al-Hilal na son maye gurbin dan wasan mai shekara 32, da dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara 39 da yake taka leda a kulub din Saudiyya. (Sport - in Spanish)
Manchester United da Chelsea na sahun gaba na son dauko dan wasan Sweden da Sporting Viktor Gyokeres mai shekara 26, a kaka mai zuwa. (Star)
A kaka mai zuwa dai farashin Gyokeres zai kai fam miliyan 63, fiye da adadin da aka yi hasasshe na fam miliyan 20 tun da farko. (Telegraph - subscription required)
Manchester United na son dan wasan tsakiya na Jamus, mai taka leda a Bayern Munich Leon Goretzka, mai shekara 29. (Florian Plettenberg)
A watan Junairu mai zuwa ne Real Madrid za ta yi hubbasar dauko dan wasan baya na Ingila, mai taka leda a Liverpool Alexander-Arnold, wanda kwantiragin sa zai kare a karshen kakar wasa. (Marca - in Spanish)
Sai dai Liverpool, na shirin kin amincewa da tayin farkoko-farko kan dan wasan a watan Junairun. (Football Insider)
Kungiyoyin Arsenal, Liverpool da Tottenham na son dan wasan tsakiya na Sweden mai taka leda a Eintracht Frankfurt Hugo Larsson mai shekara 20. (Caught Offside)
A watan Junairu ne ake sa ran Crystal Palace za tayi shirin sayen dan wasan tsakiya na Ingila ajin 'yan kasa da shekara 18, da ke taka leda a Sunderland, Chris Rigg, mai shekara 17 kan farashin fam miliyan 20. (Sun)
Everton ta nuna sha'awar dan wasan baya na Ghana mai taka leda a Brighton Tariq Lamptey mai shekara 24 idan kwantiraginsa ya kare an kuma bude kasuwar saye da saida 'yan wasa.