Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaushe ne Mbappe zai fara cin ƙwallo a La Liga?
Sabon ɗan wasan da Real Madrid ta ɗauka a bana, Kylian Mbapppe ya buga wasa biyu a La Liga ba tare da cin ƙwallo ba.
Ya fara karawa a babbar gasar tamaula ta Sifaniya ranar Lahadi 18 ga watan Agusta a gidan Real Mallorca, inda suka tashi 1-1.
Ranar Lahadi 25 ga watan Agusta, Real Madrid ta fara wasan farko a bana a Santiago Bernabeu, amma na biyu a La Liga a bana.
Real ɗin ta doke Real Valladolid 3-0, inda Federico Valverde da Brahim Diaz da kuma Endrick suka ci mata ƙwallayen.
Koda yake kafin fara La Liga ta 2024/25, Real Madrid ta lashe Uefa Super Cup, bayan da ta ci Atalanta 2-0 a birnin Warsaw a Poland ranar 14 ga watan Agusta.
Kylian Mbappe ne ya ci wa Real ƙwallo na biyu a wasan, bayan Federico Valverde da ya fara zura na farko da ya bai wa Real damar lashe kofin farko a kakar nan.
Ranar Alhamis 29 ga watan Agusta Real Madrid za ta je gidan Las Palmers, domin buga wasan mako na uku a La Liga, watakila Mbappe ya fara cin ƙwalllo a ranar.
Real ta doke Las Palmers 2-0 a kakar 2023/24 ranar Laraba 27 ga watan Satumbar 2023, sannan ta je ta ci 2-1 a Las Palmers ranar 27 ga watan Janairun 2024.
Mbappe ya fara buga La Liga a Bernabeu a karon farkko ranar Lahadi, koda yake an sauya shi da Endrick, wanda ya ci ƙwallo na uku a karawar.
Bayan tashi daga wasan Mbappe ya ce ya ji daɗin wasan ya kuma yaba ga magoya baya, yadda suke karawa ƙungiyar kwarin gwiwa.
Ya kuma ce abin farinciki sun samu maki uku a wasan, sannan za su ɗaura ɗamarar lashe sauran karawar da take gabansu.
Mbappe ya koma Real Madrid kan fara kakar bana, bayan da yarjejeniyarsa ya kare a Paris St Germain a karshen kakar da ta wuce.
Wasu na cewa ƙyaftin ɗin tawagar Faransa mai kofin duniya ya koma Real Madrid ne, domin ƙwadayin lashe Champions League da ƙyautar Ballon d'Or.