Wane ne sabon kocin Najeriya Bruno Labbadia?

Lokacin karatu: Minti 2

A safiyar Talata ce Hukumar Ƙwallon Kafa ta Najeriya, NFF ta sanar da naɗa Bruno Labbadia a matsayin sabon kocin tawagar Super Eagles.

Sakataren Hukumar NFF, Mohammed Sanusi ne ya sanar da hakan, inda ya ce, “Kwamitin NFF ya amince da naɗa Mista Labbadia a matsayin sabon kocinna Super Eagles.”

Labbadia ne zai maye gurbin Finidi Geroge, wanda ya ajiye aiƙinsa a watan Yuni, kwana kaɗan bayan ya zama kocin.

Labbadia ne zai zama kocin tawagar Super Eagles na 37.

Wane ne sabon kocin?

An haife shi ne a garin Darmstadt a ƙasar Jamus, a ranar 8 ga watan Fabrairun 1966. Tsohon ɗan ƙwallo ne wanda ya taka leda a ƙungiyoyin Darmstadt 98 da Hamburger SV da FC Kaiserslautern da Bayern Munich da FC Cologne da Werder Bremen da Armenia Bielefeld da Karlsruher SC.

Ya taɓa lashe kofin Bundesliga da ƙungiyar Bayern Munich yana ɗan kwallo a 1994.

Ya horar da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa irin su Hertha Berlin da VfB Stuttgart da VfL Wolfsburg da Hamburger SV da kuma Bayer Leverkusen da sauransu.

Ya zama ɗan Jamus na shida ke nan da zai ja ragamar tawagar ta Super Eagles bayan Karl-Heinz Marotzke (wanda ya horar da tawagar sau biyu tsakanin 1970 da 1974), Gottlieb Göller (1981), Manfred Höner (1988-1989), Berti Vogts (2007-2008) ada Gernot Rohr (2016-2021).

Yanzu dai babban aikin da ke gaban Labbadia shi ne jagorantar tawagar zuwa samun gurbin Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta 2025, inda tawagar za ta fafata wasannin guda biyu masu muhimmanci da Benin a ranar 7 ga Satumba a birnin Uyo na Najeriya, da kuma Rwanda a ranar 10 ga Satumba a birnin Kigali.

Jerin tsofaffin waɗanda suka horar da Super Eagles

  • John Finch (Ingila) – 1949
  • Daniel Anyiam (Najeriya) – 1954-1956; 1964-1965
  • Les Courtier (Ingila) – 1956-1960
  • Moshe Beit Halevi (Isra’ila) – 1960-1961
  • George Vardar (Hungary) – 1961-1963
  • Joey Blackwell (Ingila) – 1963 – 1964
  • József Ember (Hungary) – 1965-1968
  • Sabino Barinaga (Spain) – 1968-1969
  • Peter ‘Eto’ Amaechina (Najeriya) – 1969-1970
  • Karl-Heinz Marotzke (Jamus) – 1970-1971; 1974
  • Jorge Penna (Brazil) – 1972-1973
  • Jelisavčić ‘Father Tiko’ Tihomir (Yugoslavia) – 1974-1978
  • Otto Glória (Brazil) – 1979-1982
  • Gottlieb Göller (Jamus) – 1981
  • Adegboye Onigbinde (Najeriya) – 1983-1984; 2002
  • Chris Udemezue (Najeriya) – 1984-1986
  • Patrick Ekeji (Najeriya) – 1985
  • Paul Hamilton (Najeriya) – 1987; 1989
  • Manfred Höner (Jamus) – 1988-1989
  • Clemens Westerhof (Netherlands) – 1989-1994
  • Amodu Shaibu (Najeriya) – 1994-1995; 1996-1997; 2001-2002; 2008-2010
  • Johannes Bonfrere (Netherlands) – 1995-1996; 1999-2001
  • Philippe Troussier (Faransa) – 1997
  • Monday Sinclair (Najeriya) – 1997-1998
  • Bora Milutinović (Yugoslavia) – 1998
  • Thijs Libregts (Netherlands) – 1999
  • Christian Chukwu (Najeriya) – 2002-2005
  • Augustine Eguavoen (Najeriya) – 2005-2007; 2010; 2022
  • Berti Vogts (Jamus) – 2007-2008
  • Lars Lagerbäck (Sweden) – 2010
  • Samson Siasia (Najeriya) – 2010-2011; 2016
  • Stephen Keshi (Najeriya) – 2011-2014; 2015
  • Sunday Oliseh (Najeriya) – 2015-2016
  • Gernot Rohr (Jamus) – 2016-2021
  • José Peseiro (Portugal) – 2022-2024
  • Finidi George (Najeriya) – 2024
  • Bruno Labbadia (Jamus) – 2024-?