Waiwaye: Shawarar ƙirƙiro sabbin jihohi da sace tsohon shugaban NYSC
Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Asalin hoton, NASS
Majalisar Wakilan Najeriya ta bayar da shawarar ƙirƙiro sababbin jihohi 31

Asalin hoton, NASS
A ranar Alhamis da ta wuce ne kwamitin sake nazarin kundin tsarin mulkin Najeriya na majalisar wakilan ƙasar ya bayar da shawarar ƙirƙiro ƙarin sababbin jihohi 31 a ƙasar.
Mataimakin shugaban majalisar wakilan, Hon.Benjamin Kalu ne ya bayyana haka lokacin da ya karanto wasiƙar kwamitin, a zaman majalisar da ya jagoranta na ranar ta Alhamis.
Idan aka amince da buƙatar yawan jihohin Najeriya zai kai 67.
Wannan batun dai ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin masu sharhi da masana, inda wasu ke suka game da shawarar
Tinubu ya ƙara yawan kuɗin kasafin Najeriya na 2025

Asalin hoton, @jidesanwoolu
A ranar Laraba da ta gabata ne shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya karanta wasiƙar da Shugaba Tinubu ya aike wa majalisar inda a ciki yake buƙatar majalisar ta amince da ƙari a kasafin kuɗin da ya gabatar na shekarar 2025 daga naira triliyan 49.7 zuwa naira triliyan 54.2.
A cikin wasiƙar, shugaban ya ce buƙatar ƙarin ta taso ne sakamakon samun ƙarin kuɗaɗe da ƙasar ta yi na naira tiriliyan 1.4 daga hukumar tattara haraji ta ƙasar FIRS, da naira tiriliyan 1.2 daga hukumar hana-fasa-ƙwauri - kwastam, sai kuma naira tiriliyan 1.8 daga wasu hukumomin gwamnati.
Bayan karanta wasiƙar shugaban ƙasar, shugaban majalisar dattawan ya buƙaci kwamitin da ke kula da kasafin kuɗin kan su gaggauta duba batun.
Ya kuma tabbatar cewa za a kammala dubawa da amincewa da kasafin kudin kafin ƙarshen Fabarairu.
Ƴanbindiga sun sace tsohon shugaban NYSC na Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Laraba da ta wuce ne wasu ƴanbindiga ɗauke da makamai suka sace tsohon shugaban hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya, NYSC, Birgediya Janar Mahrazu Tsiga, mai ritaya.
Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar Katsina, Dakta Nasiru Mu'azu, ya tabbatar wa BBC cewa an sace Janar Tsiga a garin Tsiga da ke yankin ƙaramar hukumar Bakori, a ranar Larabar da daddare.
''An sace shi ne tare da wasu mazauna garin 13 ciki har da mata biyu, a lokacin da maharan suka auka wa garin, kodayake daga baya mutum huɗu sun kuɓuta'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Kwamishinan ya kuma yi zargin cewa masu tsegunta wa 'yanbindiga bayanai ne suka tsegunta musu shigar tsohon Janar ɗin zuwa garin ''saboda a ranar Laraba da rana ne ya shiga garin, kuma da daddare suka je suka ɗauke shi''.
Tinubu ya sauke Farfesa Aisha Maikuɗi daga shugabancin Jami'ar Abuja

Asalin hoton, Family
A ranar Alhamis da ta wuce ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sauke Farfesa Aisha Maikudi daga muƙaminta na shugabancin Jamai'ar Yakubu Gawon da ke Abuja da aka fi sani da Jami'ar Abuja.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar a ranar ta Alhamis, ya ce Shugaba Tinubu ya maye gurbinta da Farfesa Lar Patricia Manko da za ta riƙe muƙamin a matsayin riƙo na wata shida.
Sai dai sanarwar ta ce sabuwar shugabar riƙon ba za ta iya neman muƙamin idan lokacin neman matsayin ya zo ba.
A watan Yunin shekarar da ta gabata ne aka naɗa Farfesa Aisha Sani Maikudi a matsayin shugabar jami'ar bayan cikar wa'adin mulkin shugaban jami'ar na shida, Farfesa Abdulrasheed Na'Allah.
Za a fara cin tarar masu ƙazanta a titunan Kano naira 25,000

Asalin hoton, GETTY
A ranar Litinin ne majalisar dokokin jihar Kano ta amince da ƙudirin haramci da saka tarar naira 25,000 ga duk mutumin da aka kama yana ba-haya ko fitsari ko zubar da shara da tofa yawu da majina a tituna da ƙarƙashin gadoji da gine-ginen gwamnati da ma wuraren taruwar al'umma.
Sai dai matakin ya janyo ce-ce-ku-ce da tayar da ƙura a jihar.
Bayan amincewa da ƙudurin majalisar ta miƙa wa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf domin sanya masa hannu wanda daga nan ne kuma zai zama doka.
Dokar ta tanadi cewa duk wanda aka samu da laifi kuma ya kasa biyan tarar ta naira 25,000 to hakan ka iya kaiwa ga kotu ta tasa ƙeyar mutum zuwa gidan yari.











