Yadda al'ummar ƙabilun asali na Amurka ke rayuwa

Karl Kloster ɗan asalin ƙabilar Ojibwe ne mai aiki a wurin adana tarihi na Grand Portage
Bayanan hoto, Karl Kloster ɗan asalin ƙabilar Ojibwe ne mai aiki a wurin adana tarihi na Grand Portage
    • Marubuci, Haruna Ibrahim Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Duk da ci gaba irin na ƙasar Amurka, ɗaya daga cikin munanan abubuwan da suka yi mata tabon da ba zai taɓa gogewa ba shi ne halin da aka jefa ƙabilu mazauna ƙasar na asali tun kafin isar mutane daga nahiyar Turai.

A yanzu Turawa da sauran al'umma sun mamaye ƙasar ta Amurka daga kowane ɓangare na duniya, kuma idan har kana son sanin asalin al'umma ko ƙabilun da suka kasance a ƙasar tun kafin zuwan baƙi sai ka je wasu yankuna na gefen ƙasar.

Wannan ne ya sa na kai ziyara wani yanki da ake kira Grand Portage da ke iyaka da ƙasar Canada ta arewacin jihar Minnesota da ke Amurka.

Bukkokin ƙabilar Ojibwe waɗanda ke kallon gaɓar tafkin Gichigame
Bayanan hoto, Bukkokin ƙabilar Ojibwe waɗanda ke kallon gaɓar tafkin Gichigame

Ɗaya daga cikin ƙabilun ƴan asalin Amurka ita ce wadda ake kira Ojibwe ko Chippewa sannan suna kiran kansu da Anishinaabe.

Anishinaabe na nufin mutanen asali. Mutane ne da ke zama a kusa da wani tafki da ake kira Gichigame, wanda a yanzu aka fi sani da ‘Lake Superior’ a turance. Shi ne tafki mafi faɗi a doron ƙasa.

Tafki ne wanda ke kan iyaka tsakanin Amurka da ƙasar Canada.

Duk da cewa al’ummar wannan ƙabila sun yaɗu a faɗin duniya, amma yanzu haka suna da wani yanki da aka ware musu da ke zama tamkar ƙasa mai ƴancin kanta amma a cikin jihar Minnesota da ke Amurka, yankin na kan iyaka ne da ƙasar Canada.

Marie Spry, ƴar kwamitin tafiyar da gwamnatin ƙabilar Ojibwe
Bayanan hoto, Marie Spry, ƴar kwamitin tafiyar da gwamnatin ƙabilar Ojibwe

Marie Spry, mai shekara 77 a duniya wadda ƴar asalin ƙabilar Ojibwe ce ta ce “tabbas ƙasarmu mai zaman kanta ce, mu ne ke tafiyar da lamurranmu kuma muna da kotunanmu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Ba mu da jami’an ƴansanda namu na kanmu saboda ba mu da mutane da yawa”.

A halin yanzu yankin na da jimillar mutane kimanin 300, waɗanda suka haɗa da manya da yara ƴan asalin ƙabilar, sannan akwai kimanin mutum 1,000 ƴan ƙabilar a doron ƙasa, inda wasunsu ke zaune a wasu ƙasashe da kuma wasu sassa na Amurka.

Marie na daga cikin mutane shida da ke tafiyar da lamurran yankin Grand Porte. Za a iya cewa ta yi kusan rayuwarta kacokan ne a wannan yanki na Grand Portage in ban da zaman da ta yi a garin Silver Bay, mai nisan kimanin mil 90 daga garin na ta na asali.

An zaɓe ta ne a matsayin ɗaya daga cikin masu tafiyar da lamurran yankin tun shekara ta 2012, kuma ana yin zaɓen ne bayan kowace shekara huɗu.

Kamar yadda ya kasance a tarihin ƴan ƙabilar, rayuwarsu dogara ne lacokan kan arziƙin da suke samu daga tafkin, ta hanyar kamun kifi da kuma sufuri. A yanzu ma su ne ke amfani da duk kuɗin da aka samu daga arziƙin yankin, musamman abin da ya shafi yawon shaƙatawa da cacar Casino.

Tarihin ƙabilar Ojibwe

Butumbutumin ɗan asalin ƙabilar Ojibwe ɗauke da kaya a gidan adana kayan tarihi na Grand Portage
Bayanan hoto, Butumbutumin ɗan asalin ƙabilar Ojibwe ɗauke da kaya a gidan adana kayan tarihi na Grand Portage

Ojibwe ita ce ƙaɓila mafi ƙarfi a tsakanin al’ummun da ke zama a gaɓar tafkin na Lake Superior.

Suna rayuwa ne ta hanyar kamun kifi a tafkin Lake Superior, suna farautar dabbar Beevar domin amfani da fatarta wajen yin sutura sannan kuma suna cin shinkafar daji.

A cikin shekarun 1700, tafkin ya kasance mai matuƙar muhimmanci a harkar kasuwanci na duniya, wannan ya sanya al’ummar suka zamo masu matuƙar ƙima da daraja.

Sun kasance mutane da suka ƙware wajen farauta sannan kuma suna da masaniya sosai kan yankunan da ke maƙwaftaka da tafkin.

A fannin sufuri sun ƙware wajen haɗa kwale-kwale masu inganci kuma marasa nauyi, hakan ya sa kwale-kwalen ƴan ƙabilar Ojibwe suka kasance suna iya ɗaukar kaya masu yawa.

Duk da cewa al’ummar Ojibwe ba mutane ne masu girman jiki ba, amma mutane ne masu ƙarfi da juriya.

Wannan ne ya sanya turawa suka riƙa ɗaukan su haya domin yi musu aiki a lokacin da suka iso Amurka, kasancewar suna iya yin aiki fiye ma da dabbobin da ake amfani da su wajen ɗaukar kaya da ayyuka a gona.

Sukan ɗauki kaya tun daga yankuna na kan tudu har zuwa bakin tafki, zuwa cibiyoyin kasuwanci da turawa suka kafa, tun daga bakin tafkin har zuwa tekun Pacific, wanda ake amfani da shi wajen safarar kaya daga Amurka zuwa Turai.

Turawa sun laƙaba wa labin da ƙabilar ke bi idan sun ɗauki kaya da suna ‘Grand Portage’.

Hanyar ta ratsa ne ta tsakanin duwatsu da gefen rafuka har zuwa gaɓar tafkin Gichigame ta gabas.

Karl Kloster ɗan asalin ƙabilar Ojibwe shi ma ƙwararren mai haɗa kwale-kwale ne
Bayanan hoto, Karl Kloster ɗan asalin ƙabilar Ojibwe shi ma ƙwararren mai haɗa kwale-kwale ne

Da farko dai al'ummar Ojibwe sun yi cinikayya da turawa cikin lumana, sai dai daga baya abubuwan sun taɓarɓare.

A shekarun 1782 zuwa 1783 al'ummar ta yi fama da cutar ƙaranbau wadda ta samo asali daga nahiyar Turai, wannan ya halaka mutanen yankin da dama, kuma suna ganin cewa hakan ya sa al'unsu da dama sun gushe sanadiyyar mutuwar tsofaffi waɗanda su ne suka san al'adu da harshensu na asali.

Haka nan kuma hanƙoron ƙwatar ƴanci ya ƙara jefa yankin cikin rashin tabbas.

Zanen tarihin yadda al'ummar Ojibwe suke rayuwa kusa da tafkin Gichigame, wanda ke ajiye a gidan tarihi na gandun dajin Grand Portage a kan iyaka da ƙasar Canada

Asalin hoton, Grand Portage State Park

Bayanan hoto, Zanen tarihin yadda al'ummar Ojibwe suke rayuwa kusa da tafkin Gichigame, wanda ke ajiye a gidan tarihi na gandun dajin Grand Portage a kan iyaka da ƙasar Canada

A ƙarni na 19 ne aka tabbatar da iyakar da ke tsakanin Amurka da yankin Canada wanda ke ƙarƙashin mulkin tutrawan Birtaniya.

Wannan ya sa an raba ƴan ƙabilar zuwa gida biyu, wasu na cikin Amurka yayin da wasu ke cikin Amurka.

A shekarun 1850 kuma wani abin tashin hankali ya faru ga ƙabilar bayan an ƙirƙiri jihar Minnesota, inda suka yi zargin cewa an ƙwace musu ƙasarsu, kuma aka kora su zuwa wani ƙaramin yanki, wanda shi ne a yanzu ake kira Garnd Portage.

Sun yi zargin cewa baƙin turawa daga nahiyar Turai sun ci zarafinsu kuma sun yi ƙoƙarin tursasa musu rungumar baƙin al'adu da sunan wayewa.

Har yanzu wasu daga cikin ƴan ƙabilar na ci gaba da kamun kifi a tafkin Superior Lake kuma suna gudanar da al'adunsu iyakan gwargwado.

Sun ce har yanzu suna jin kansu a matsayin ƴan ƙasa kuma suna alfahari da tarihinsu.