'Mun fara aikin tsaftace birnin Maiduguri da ambaliya ta ɗaiɗaita'

,

Asalin hoton, Borno State Government

Bayanan hoto, Madatsar ruwa ta Alau ce ta tumbatsa tare da ambaliya cikin birnin Maiduguri da kewaye
Lokacin karatu: Minti 3

Ma'aikatar muhalli ta Najeriya ta ce ta fara wani shiri na tsaftace birnin Maiduguri, na jihar Borno, bayan mummunar ambaliyar da ta shafi akalla kusan mutane miliyan biyu.

Aikin na hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin tarayya da na duba gari, da nufin tsaftace jihar domin kauce wa sake barkewar wasu cutuka bayan amai da gudawa da aka fara samun wadanda suka kamu da cutar, sakamakon dagwalon da ambaliyar ruwan ta bari.

Gidaje da dama sun rushe, hanyoyi sun lalace, amfanin gona ya daidaice, sai kuma fama da rashin wadataccen tsaftataccen ruwan sha.

Dakta Yakubu Baba shi ne shugaban ma'aikatan hukumar duba gari, ya shaida wa BBC cewa mai aukuwar dai ta faru wato ambaliyar ruwa - abu na gaba shi ne lalubo hanyar tsaftace barnar da ta yi.

''Wannan aikin za a yi shi ne karkashin ofishin ministan muhalli na kasa, mun je birnin Maiduguri mun duba irin barnar da ambaliyar ta yi, muna fargabar yadda bandakuna suka lalace da yadda mutane ke bayan gida a wuraren da suka samu zai haddasa cutuka masu yaduwa.

''Misali hanyar ruwan sha da ta bayan gida na mutane da na dabbobi da sokaye duka sun hade wuri guda, don haka muka debi samfurin ruwan domin a yi binciken kwakwaf a kai, da kuma daukar mataki na gaba na tsaftace shi saboda mutane za su iya daukar cutuka idan sun sha ruwan ko wanka ko wani uzuri ba tare da sun tsaftace shi ba,'' in ji Dakta Yakubu.

Dakta Yakubu ya kara da cewa abu mai muhimmanci da suke son kare afkuwarsa ita ce cutar kwalara wadda ake dauka daga ruwa maras tsafta da rashin tsaftar muhalli da kayan cimaka.

Gwamnati za ta duba hanyar da mutanen Maiduguri ke amfani da ita wajen samun ruwan sha, domin tabbatar da tsafta da ingancin ruwan, a yi gwaji domin gano wadanne irin kwayoyin cuta ne a ciki in ji jami'in.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ce za su yi kokarin ganin an yi aikin cikin gaggawa, ''Za mu duba maganin da ya kamata mu yi amfani da shi domin tsaftace ruwan, aikin annoba irin wannan aikin mutane da dama ne akwai hadin gwiwa tsakanin ma'aikatan hukumar agajin gaggawa ta NEMA da ma'aikatar ruwa ta Najeriya da gwamnatin Borno har da kungiyoyi masu zaman kansu. Yanzu dai mun taho da sinadrin kulorin (Chorine) na tsaftace ruwa, za mu sanya shi ta yadda ba zai yi illa ga dan'Adam ba.''

Ambaliyar ruwan da aka jima ba a fuskanta ba a jihar Borno tun shekarar 1995, ta janyo aikin jin-kai da ceto mafi girma a arewacin Najeriya, inda gwamnatin tarayya da jihohi da hukumomin bayar da agaji na ciki da wajen Najeriya da masu hannu da shuni har da marassa karfi sun hada karfi da karfe domin ceto wadanda suka makale a gidajensu, da masu tsananin bukatar taimako.

Sai dai har yanzu da alama ana ci gaba da fuskantar korafe-korafe daga mazauna birnin Maidugurin, kan rashin isar da tallafi ga wadanda ke tsananin bukatar taimakon.