Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace ƙasa ce Lesotho - wadda Trump ya ce 'babu wanda ya san ta'?
- Marubuci, Basillioh Rukanga
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 5
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ''babu wanda ya san wata ƙasa Lesotho'', da ke nahiyar Afirka, kalaman da suka girgiza gwamnatin ƙasar.
Ƙaramar ƙasar da ke kudancin Afirka, wadda ƙasar Afirka ta Kudu ke zagaye da ita, na da tarin tsaunuka a cikinta.
Ga wasu abubuwa tara game da ƙasar:
'Masarautar Sammai'
Masarautar Lesotho ta ƙunshi tarin tuddai, inda ba a iya zuwa wasu ƙauyukan ƙasar da dama, sai a kan doki ko a ƙafa ko kuma a ƙananan jirage.
Ana kiranta da ''Masarautar Sammai'' kuma ita kaɗai ce ƙasa mai ƴanci a duniya da ke kan tsauni, inda gaba ɗayan ƙasar ke sama da mita 1,000,(ƙafa 3,281)daga ƙasa, kamar yadda rumbun ajiyar bayanai na Encyclopaedia Britannica ya nuna.
Wuri mafi kusa da ƙasa shi ne mai nisan mita 1,400.
Ƙasar ta yi fice wajen zama ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da ake fuskantar tangarɗar saukar jirage.
Shafin yanar gizo na Business Insider ya bayyana tashin jirgi a ƙasar tamkar ''jefo ɗan tsuntsu daga sheƙarsa da nufin koya masa tashi''.
Afirka ta Kudu ce ta zagaye ƙasar ta ko'ina
Lestho zagaye take da ƙasar Afirka ta Kudu ta kowane ɓangare, amma tsaunuka ne suka yi wa ƙasashen biyu iyaka.
Ƙasar ba ta da albarka noma, lamarin da ya sa mafi yawan al'ummarta ke fama da ƙarancin abinci, kuma suka dogara kan ayyukan ƙodago a Afirka ta Kudu.
Cikin fiye da gomman shekaru, dubban ƴan ƙasar rashin aikin yi ke tilasta wa ficewa zuwa Afirka ta Kudu domin neman ayyukan yi.
Al'ummar Lesotho - waɗanda suka kai fiye da miliyan biyu - na da al'adu da harshe iri guda da na al'ummar Afirka ta Kudu.
Harshen da suke magana da shi, Sesotho, na ɗaya daga cikin harasan hukuma 11 da ake amfani da su a Afirka ta Kudu.
Hasalima masu amfani da harshen a Afirka ta Kudu, (miliyan 4.6) sun zarta yawan al'ummar Lesotho.
Ruwa ne babban arzikin ƙasar
Ƙasar Lesotho na fama da ƙarancin ma'adinai, ɗaya daga cikin matsalolin muhalli da ƙasar da ke kan tsaunuka da tuddai mai ƙarancin ƙasar noma ke fuskanta.
Babban arzikin ƙasar shi ne ruwa - da aka fi sani da ''farin zinare a ƙasar - da ake fitarwa zuwa Afirka ta Kudu.
Tana kuma da ma'adinin Diamond da take fitarwa.
Wurin wasan zamiyar ƙanƙara mafi tsayi a Afirka
Idan kai ma'abocin wasan zamiya ko zamiyar ƙanƙara ne, a duk idan aka yi batun wasan, abin da zai zo ranka shi ne wuraren ƙanƙara na Turai da Arewacin Amurka.
Amma ƙasar Lesotho na da wuraren wasan zamiya masu ɗaukar hankalin ma'abota wasan. Tana da wurin wasa mafi tsayi da ƙayatarwa a Afirka.
Wurin wasan nata - mai suna Afriski - na kan tsauni da nisan mita 3,222 a saman tsaunin Maloti, wanda kuma ke jan hankali masu ziyara a ciki da wajen Afirka.
Ana kiran ƴan ƙasar 'Basotho' a turance.
Ana kiran mutanen Lesotho da Basotho a turance.
Wasu daga cikin al'adun ƴan ƙasar su ne barguna da malafar da aka fi sani da Mokorotlo.
Malafar alama ce ta ƙasar kuma tana cikin tsakiyar tutar ƙasar.
Akan yi bargunan da auduga mai kauri, ɗauke da kaloli masu yawa a jikinsu, inda kowane kala akwai abin da yake nufi game da tarihin ƴan ƙasar.
Al'ummar ƙasar kan sanya bargunan a matsayin mayafi a wuraren bukukuwa na musamman, sannan suna bayar da kyaututtukansu.
Tana cikin ƙasashen da HIV ya fi yawa a duniya
Ƙasar Lesotho na ɗaya daga cikin ƙasashen da cutar HIV ta fi ƙamari a duniya, inda mutum guda cikin matasa biyar ke ɗauke da cutar.
Haka kuma ta fi kowace ƙasa yawan masu kamuwa da cutar a cikin kowane 100,000 fiye da sauran ƙasashe, ciki har da makwabtanta Namibia da Botswana da kuma Eswatini.
A shekarar 2006 gwamnatin Amurka ta bai wa ƙasar dala biliyan guda domin yaƙi da cutar HIV, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana.
Yarima Harry na da gidauniya a Lesotho
Kamar Birtaniya, Lesotho mai tafiya kan tsarin sarauta. Hakan na nufin duk da cewa akwai sarki, ana kuma zaɓar firaminista wanda ke tafiyar da harkokin mulkin ƙasar.
Yariman Lesotho Prince Seeiso - ƙanan sarkin ƙasar na yanzu Letsie III - babban aboki ne ga Yarima Harry na Birtaniya.
Abokan biyu sun assasa gidauniya - Sentebale - da ke aiki da ƴan ƙasar domin tallafa wa matasan ƙasar masu ɗauke da cutar HIV/Aids.
Yarima Harry na Birtaniya ya fara zuwa Lesotho tun yana da shekara 19, kuma tun daga lokacin yake ziyartar ƙasar.
Tana sayar wa Amurka kayan jeans
An jima ana alaƙanta wandunan Jeans da Mutanen Amurka, amma a yanzu, da dama cikin waɗanda ake sakawa a Amurka
Kamfanonin tufafain ƙasar, kan yi wandunan jeans ga Amurkawa kamar nau'ikan Levi's da Wrangler a shekarun baya-bayan nan.
Kan haka ne ake yi mata laƙabi da "cibiyar jeans ta Afirka".
Baya ga jeans - Lesotho na ɗaya daga cikin ƙasashen Afirka da suka fi fitar da tufafi zuwa Amurka.
A shekarar da ta gabata, Lesotho ta fitar da tufafi na dala miliyan 237 zuwa Amurka ƙarƙashin yarjejeniyar 'African Growth and Opportunity Act' (Agoa), wanda ke bai wa ƙasashen Afirka da suka cancanta damar aika kayayyaki zuwa Amurka ba tare da biyan haraji ba.
Ita ce ƙasa ta biyu da suka aika kayayyaki masu yawa zuwa Amurka ƙarƙashin yarjejeiyar.
Da dama daga cikin kamfanonin tufafin lestho mallakin ƴanciranin China da Taiwan ne.
Ƙasar da aka fi samun laifin kashe kai a duniya
Masarautar mai cike da tsaunuka, ita ce ƙasar da aka fi yawan samun mutanen da ke kashe kansu a duniya.
Hukumar Lafiya ta Duniya, ta ce kashi 87.5 cikin kowane 100,000 na al'ummarta ke kashe kansu a kowacce shekara.
A wannan shekara ƙasar ta ninka ƙasar da ke biye da ita a kashe kai a matsayin ta biyu, Guyana har sau 10.
Sai dai wani cikakken dalilin waɗannan alƙaluma - Masana na cewa shan miyagun ƙwayoyi da barasa da rashin ayyukan yi da rashin masu lura da ƙwaƙwalwa sun taimaka.
Ƙarin rahoto daga Wedaeli Chibelushi