Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Munanan fadace-fadace tsakanin mawaka na kasar Lesotho
- Marubuci, Daga Tim Whewell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Gabar da ke tsakanin taurarin makadan nau'in kayan kidan zamani na accordion ko kuma a gargajiyance Famo a masarautar Lesotho ta Kudancin Afirka, ta haifar da yawan matafiya 'yan daba da suka mayar da karamar kasar babban wurin kisan kai na nahiyar.
"Watakila na samu tsira ne saboda ni mace ce,'' Puseletso Seema ta bayyana a hankali, radar ta wata murya ce mai karfi da ta taba dauke hankulan mutane a wuraren shan barasa da filayen wasa a fadin Afirka ta Kudu da sauransu.
Wacce ake yi wa kirari da Sarauniya Famo, shararren kidan kasa na Lesotho, tana zaune a kan wata doguwar kujera a karamin gidanta, da abubuwa kalilan da ke nuna nasarorinta na shekaru da dama.
"Kowa yana son ya nuna shi namiji ne ta hanyar mallakar bindiga,'' in ji ta.
Famo ya bunkasa a lokacin da "wakokin yabo na masu tafiyar kafa" - wani salo ne na rubutattun wakoki ko gambara da makiyaya ko mafiya kan rika rerawa don rage tsawon sa'oin da sukan shafe suna tafiya yayin kula da shanu ko kuma tafiyar kafa ta cikin tsaunkunan Lesotho - wanda daga bisani aka koma amfani da kayan kidan zamani na accordion.
Amma a shekarar 2004, bayan da aka zargi wani mawakin Famo da harbe wani mawakin, hakan ya haddasa yawan kisan daukar fansa. Kuma a cikin shekara 10 da suka gabata, an bindige mawakan Famo da dama, da daruruwan sauran mutane masu alaka da kidan - da suka hada da masu shiryawa, da masu bibiya, da masu gabatarwa da saka wakoki da kuma iyalan mawakan.
"Sukan shigo gida suna neman ka - kuma idan ba ka nan ai su kashe matarka, su kashe 'yayanka, su hallaka kowa a cikin iyalan. Kauyuka sun kasance gidan marayu saboda kidan famo,'' in ji daya daga cikin wadanda suka fara kikiro shi, Sebonomoea Ramainoane.
Ba duka mawakan Famo ba ne ke fama da takaddama - wani makadin accordia Leteketa ya bayyana cewa bai taba shiga cikin fadan 'yan daba ba.
An tilasta wa da dama tsere wa gidajensu. Yake-yaken Famo su ne manyan dalilan da ya sa kasar mai kyau da yawan yankunan karkara, da mutane miliyan biyu - kuma daukacinta kewaye da Afirka ta Kudu - ta kasance ta shida a duniya wajen aikata kisan kai.
"Kishi, babu wani abu sai kishi,'' Seema ta ce lokacin da take bayyana yadda tashin hankalin ya fara. ''A lokacin da makadan suka fara yin fice, suna hada wakoki cike da zage-zage.''
Seema, kamar sauran taurarin Famo, ta taso a cikin wahala. ''Na fara waka tun ina karama,'' ta ce. ''Na yi kiwon shanu. Wannan ba aikin 'yan mata ba ne, amma nakan fafata da maza a wurin kiwo.''
Ta bar gida don neman nasarori wajen nishadantar da dubban maza daga Lesotho da ke aiki a nesa da gida a wurin hakar ma'adinain gwal da lu'u lu'u na Afirka ta Kudu, inda Famo ya samo asali a tsakiyar karni na 20.
Sunan ya samo asali ne daga "wafamola", wata kalma a harshen Sesotho na Lesotho, da ke nufin irin salon rawar wakar da mata kan yi suna juyawa a lokacin da dan-tofinsu ke budewa.
Seema ta samu yin fice a fagen rawa, tana karkada kugunta a cikin dan-tofin da aka yi da ciyawa a yayin da take daga sandan fasa. "Suna samun nishadantarwa,'' in ji ta game da mahaka ma'adanan da ke cikin 'yan kallon.
"Amma suna jin tsoro na. Sun yi tsammani zan kai musu duka ne. Daga nan na sauka daga dandalin cike da daure fuska. Babu wanda ke iya zuwa kusa da ni gaba da gaba.''
Seema ta karfafa guiwar wani tsohon makiyayi da ake kira Bereng Majoro wajen yin sana'ar waka. Sunan sa na sana'ar waka shi ne Lekase, da ake nufi da "makara".
"Yin waka gasa ce," ya shaida min a yayin da muke zaune a wani wuri a wajen Maseru babban birnin kasar Lesotho, inda yanzu ya yi murabus..
"Kowa yana son zama mai samun nasara."
Mawakan Famo da magoya bayansu a kasashen Afirka da Kudu da Lesotho, kawunansu sun rarrabu zuwa kungiyoyin masu gaba da juna, akan kuma iya gane su da irin gwado na gargajiya masu launuka na da ban, da suke saka wa. Launin rayawa na 'yan kungiyar Terene ne, daya daga cikin manyan kungiyoyin; lunukan baki da fari na nuni da kungiyar Seakhi, wacce Lekase ke ciki.
Lokacin da aka yi wa daya mawakin kungiyarsu barazana, Lekase, wanda har yanzu ke zaune a Afirka ta Kudu kan boye kan sa. A ko da yaushe yana dauke da bindiga.
Ya ki ya bayyana ko shin ya taba kashe mutane, yana yi wa tambayar dariya. Amma ya bayyana cewa: ''Na kan mayar da martani, saboda idan na ga an binne wani, bayan sanin cewa sauran kungiyoyi ne suka kashe shi, na kan ji bacin rai. Don haka dole in dauki fansa."
Idan muka dawo Lesotho, daya wanda aka kai wa harin daukar fansa mawakin Famo ne Salope Mohlobuti, da aka harbe a wani gidansa da ke waje daya a cikin tsaunukan Matelile a shekarar 2010. A wakarsa ta karshe, ya yi ta zagin wadanda suka kashe wani mawakin, danuwansa yana kiransu da suna ''kananan yara."
Bayan da suka fusata da wadannan kalamai na wakar ne shi ma suka kai masa farmaki.
A halin yanzu, dan Salope, Malefetsane, mai shekaru 17, ya ajiye wakar a cikin wayarsa don tunawa da mahaifinsa.
Amma ya bayyana cewa ya gwammace ya cigaba da zama makiyayi a kan ya zama mawaki.
"Yanzu na daina sauraron wannan wakar sosai, saboda kalaman sun haifar da fusata. Game da kashe-kashe ne kana ba na son saka kai na cikin wannan. Wakar ta da hallaka mahaifina."
Wasu mawakan irin su Seema, na kaucewa shiga cikin tashin hankalin. Ta bayyana cewa ba ta taba zagin kowa ba a cikin wakarta.
"Na yi waka game da komai na rayuwata…game da lalacewa aurena, da lokacin da aurena ya mutu, na kuma yi waka kan yadda aure ke lalacewa."
Amma duk wanda ya shiga cikin Famo ya saka rayuwarsa cikin hadari. Ko su kan su mai gabatar da wakokin ana kashe s, in ji Tsepang Makakole, mai gabatar da shirye-shirye a sashen FM na gidan rediyon MoAfrika.
"Idan kana gabatar da shirye-shirye sai ka tabbatar da cewa a kullum kana saka wakokin duka kungiyoyin. Muddin ka ki saka daya, za su ce: 'Ba ka saon mu,' Daga nan sau su harbe ka."
Yanzu da kashe-kashen ba kawai sakamakon wakokin accordium ba ne.
Kungiyoyin Famo da ba sa ga-maciji da juna su ma suna fada a kan mallakar ikon wajen hakar ma'adinan zinari mai samun kudi a Afirka ta Kudu inda aksarin mabiyansu ke aiki.
A lokacin bikin Kirsimetin da ya wuce, wani mai hakar ma'adinai Sello Ntaote, ya zo gida a karon farko cikin shekaru uku don ziyartar matarsa da 'yayansa maza biyu a Lesotho.
Kwanaki kadan bayan nan aka harbe shi har kahira a jajiberin bikin sabuwar shekara - tare da saurab baki uku.
Abokansa sun yi amanna an kashe shi ne a kan aikata ''cin amana'', saboda bai jima da barin wurin hakar ma'adinai wanda 'yan dabar Famo ke rike da iko ba, zuwa wani wurin bayan da ya kwashe duk abinda ya mallaka ya tafi da su.
A cikin makon ne, sauran mutane uku suka mutu a wani abu da ake tunanin mai alaka da kisan 'yan kungiyar Famo.
Saboda nuna fusata da fargaba kan hare-haren, wanda ke sa mutane tserewa daga gidajensu, daga bisani mazauna kauyuka suka shirya wata ganawa ta nuna rashin jin dadi. Wani shugaban al'umma ya bayyana cewa an yi mata barazanar kisa kawai don ta yi magana a kan tashin hankalin. Da sama sun zargi 'yan sanda kan gazawa wajen ba su kariya, da kuma hada kai da 'yan dabar.
A watan Nuwambar da ya gabata, bindigogi 75 suka yi batan dabo a ofishin 'yansanda a gundumar tsakiya ta Mafeteng. Mataimakin ministan harkokin cikin gida Maimane Maphathe ya shaida wa BBC cewa ana cigaba da gudanar da bincike kan jami'an.
"Gwamnati ba ta yin kasa a guiwa wajen hukunta duk wani jami'in dansandan da aka kama da aikata manyan laifuka," ya ce.
Amma alakar da ke tsakanin 'yan siyasa da wakar Famo ta dade da yin karfi. Ntei Tsehlana, shugaban daya daga cikin manyan kungiyoyin 'yan dabar Famo da aka fi tsoro Terene, ya yi aiki a matsayin direban ma'aikatar harkokin cikin gida har ya zuwa lokacin mutuwarsa.
Duk da cewa an zabe shi a matsayin wanda zai gaji wanda ya kafa kungiyar Terene, daya daga cikin taurarin Famo, Mosotho Chakela, Tsehlana ba mawaki ba ne. Lokacin da na hadu da shi a farkon wannan shekarar ya musanta cewa shi dan dabar kungiyar ne.
Tsehlana ya kuma musanta bayar da umarnin a yi kisa. ''A matsayinmu na shugabannin kungiya, muna kokarin ganin mun hada wadannan kashe-kashe…sai dai kawai a wasu lokuta, ba na iya yin komai a kai, saboda mambobinmu kan xe: 'Bai kamata mu zura ido muna kallon ana kai mana farmaki ba,'' ya ce.
Mr Maphathe, mataimakin ministan harkokin cikin gida ya shaida min cewa ma'aikatar da dauki Tsehlana aiki ne cike da fatan zai shawo kan matsalolin, saboda ''watakila idan aka dauki wasu daga cikin wadannan mutane (na kungiyoyin Famo) , sauran za su gane muhimmancin samun aik, kuma za su yi aiki tukuru wajen taimaka wa gwamnati a yakin da ta ke yi da wadannan kashe-kashe."
Amma tashin hankalin ya rutsa da Tsehlana. Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, da ake tsammani daga daya kungiyar ne sun harbe shi a ranar 2 ga watan Aprilun shekarar 2022, a yayin da yake halartar wani taron mawaka da wata jam'iyar siyasa ta shirya. Daga bisani ya mutu a asibiti.
Magoya bayansa sun cafke mutane da dana da suka yi ikirarin maharan ne, kana suna mika wa 'yansanda su. Amma 'yansandan sun sako wadanda ake zargin ba tare da tuhumarsu ba, duk da cewa suna kan gudanar da bincike.
Yanzu ba kasafai ake gudanar da taron mawakan Famo kai-tsaye ba, ana daukar sa a matsayin mai matukar hadari.
"Sun lalata sana'armu, saboda fadan cikin gida," Sarauniyar Famo, Puseletso Seema, yanzu mai shekaru 73 ta bayyana.
Duk da nasarorin da ta samu, amma ta yi rayuwa marar dadi. Duka 'yayanta uku sun mutu - daya yayin haihuwa, daya kuma da rashin lafiya, a yayin da kuma aka kashe daya.
Kuma saboda ficen da ta yi, 'yan fashi da makami na shan kai mata hari, wadanda suka sace mata kayyaki da suka hada da kayan kida na accordion - da akasarin faye-fayen CDs na wakokinta.
Ta yi ta fadi tashin kula da jikokinta - da sauran marayu da dama - ita kadai. Ba tare da kayan kidanta na accordion ba, ta ce ba za ta sake samun kudin da za ta rika ciyar da su sosai ba.
"Idan da ina da kayan kidana, da ba za mu rasa gas din girki ba, ba zamu rasa cin tuwon masara ba, za su samu duk irin abubuwan da suke bukata na rayuwa."
Kamar wata tsohuwar abokiyar sana'arta kuma tauraruwa Lekase, ta yi nadamar shiga harkar wakokin Famo.
"Ina jin bacin rai. Wasun mu su rika samun kudin tafiyar da rayuwa ta hanyar wakokin, amma yanzu muna ta fadi tashin samun abin hannu," in ji ta.
"Ni fitacciyar mawakiya ve, amma yanzu na zama almajira. Wakokin Famo sun saka ni cikin bacin rai."