Ganawa uku da Tinubu ya yi domin lallashin masu shirya zanga-zanga

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na gaisawa da Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar 25 ga watan Yuli, 2024

Asalin hoton, PRESIDENCY NG

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya, Bola Tinubu lokacin da yake gaisawa da Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar 25 ga watan Yuli, 2024
    • Marubuci, Ibrahim Haruna Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

Lokaci na ci gaba da matsowa game da zanga-zangar da wasu matasa ke shiryawa a Najeriya, wadda suka ce za su yi ne domin nuna fushinsu kan matsin rayuwa da rashin tsaro.

Sai dai yayin da matasan ke nasu shirin, gwamnatin Najeriya ita ma tana nata.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi jerin ganawa da kusan duk masu faɗa a ji a ƙasar a ƙoƙarin janyo hankalin matasa wajen ganin su jingine shirin nasu na yin zanga-zanga.

Wannan baya ga sauran ganawa ke nan da sauran manyan jami'an gwamnati suka yi a ƙoƙarin nemo hanyoyin da za a lallashi matasan su janye ƙudurinsu na yin zanga-zanga.

Misali, sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu sun jagoranci wani taro da ministocin gwamnatin Tinubu a ranar Laraba game da batun.

Haka nan Tinubu ya umarci gwamnoni su koma jihohinsu domin ganawa da mutane tare da lallashin su kan batun zanga-zangar.

BBC ta duba wasu daga cikin muhimman masu ruwa da tsaki da shugaban na Najeriya ya gana da su game da batun zanga-zangar:

1- Sarakunan Gargajiya

Wasu daga cikin sarakunan da suka halarci ganawa da shugaban Najeriya a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuli, 2024

Asalin hoton, PRESIDENCY NG

Bayanan hoto, Wasu daga cikin sarakunan da suka halarci ganawa da shugaban Najeriya a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuli, 2024

Na gaba-gaba a cikin waɗanda shugaban ƙasar ya tattauna da su a ranar Alhamis su ne sarakuna daga sassan ƙasar.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, ta ce a lokacin tattaunawar, Shugaba Tinubu ya ce ya damu ƙwarai da damuwar al'ummar ƙasa kuma zai mayar da hankali a kai.

Waɗanda suka halarci ganawar sun haɗa da Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.

Haka nan akwai sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli, da Etsu Nupe, Yahaya Abubakar da ma wasu da dama.

Ganawar da Tinubu ya yi da sarakuna ba zai rasa nasaba da kallon da ake yi wa sarakuna a matsayin iyayen al'umma ba.

Suna daga cikin masu faɗa a ji tsakanin al'umma, kuma ana ganin cewa zai iya yiwuwa abin da za su faɗa wa mabiyansu ya taimaka wajen kwantar da hakali tare da hana faruwar zanga-zangar.

2 - Malaman addinnin Musulunci

Shugaban Najeriya Bola Tinubu tare da manyan malaman addinin Musulunci na ƙasar bayan ganawa da su a ranar 25 ga watan Yulin 2024

Asalin hoton, PRESIDENCY NG

Wani rukunin al'umma da shugaban ƙasar na Najeriya ya gana da su, su ne malaman addinin Musulunci daga bangarori daban-daban.

A lokacin ganawar da ta gudana ranar Alhamis, kusan abu ɗaya ne Tinubun ya shaida musu kamar yadda ya shaida wa sarakuna.

Sai dai malaman sun ce ya ba su dama su faɗa masa ƙorafe-ƙorafensu.

Sun ce sun nuna wa shugaban irin tsanani da damuwa da jama’a ke ciki, inda suka gabatar masa da wasu shawarwari kan yadda gwamnati ta za ta bi domin sama wa jama’a sauki.

"Shugaban ƙasa ya saurare mu kuma ya ce a ja hankalin al'umma su ƙara haƙuri... a yi haƙuri, nan gaba kaɗan za a ga canje-canje cikin waɗannan ƙorafe-ƙorafe da muka kawo," in ji shugaban ƙungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'ah wa Ikamatus Sunnah, na Najeriya, Sheik Abdullahi Bala Lau.

Su ma malaman addini, kamar sarakuna, mutane ne da ke da ɗimbin mabiya, kuma maganganunsu na tasiri a cikin al'umma.

3 - Gwamnonin Jam'iyyar APC

Shugaban Najeriya Bola Tinubu da gwamnonin jihohi na jam'iyyar APC a lokacin taron da suka yi ranar 25 ga watan Yulin 2024

Asalin hoton, PRESIDENCY NG

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Tinubu da gwamnonin jihohi na jam'iyyar APC a lokacin taron da suka yi ranar 25 ga watan Yulin 2024

Tun farko a ranar ta Alhamis, shugaba Tinubu ya yi wata ganawa da gwamnonin jam'iyyar APC.

Bayan kammala taron ƙungiyar gwamnonin na APC ta ce ba ta san dalilin da ya sa wasu ƴan Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zanga ba.

A jawabi a taron manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron ƙungiyar a Abuja, babban birnin ƙasar, shugaban ƙungiyar - wanda shi ne gwamnan jihar Imo, Hope Udozinma - ya ce ''mu ba mu san dalilin da ya sa suke shirin yin zanga-zangar ba, inda mun sani za mu gayyace su don zama da su domin samun maslaha''.

Haka nan gwamnonin sun yi kira ga ƴan Najeriya su yi haƙuri tare da bai wa gwamnati ƙarin lokaci.

Gwamnonin jam'iyyar APC bayan kammala taron da suka yi a Abuja

Asalin hoton, KEBBI STATE GOVT

Gwamnoni na da ƙarfin faɗa a ji a Najeriya kuma suna da matuƙar tasiri a harkokin siyasar ƙasar.

A kwanakin baya ne shugaban ƙasar ya sanar da cewa ya bai wa kowane gwamna tirelar shinkafa 20 domin rabawa ga talakawa.

Shugaban ya ce ya yi hakan ne domin rage raɗaɗin matsin tattalin arziƙi da al'umma ke ciki.

Sai dai gwamnatin ta ja hankalin ƴan siyasa su raba tallafin yadda ya kamata, kasancewar ana zargin cewa sau da yawa irin wannan tallafi bai cika kai wa al'ummar da suka fi buƙata ba.

Me jama'a ke cewa kan tattaunawar?

Tun kafin waɗannan jerin tattaunawa da shugaban ƙasar ya gudanar da masu faɗa a ji, da dama daga cikin masu neman ganin zanga-zangar ta gudana suke zargin cewa gwamnatin na ƙoƙarin yin amfani da malamai da sarakuna wajen rufe bakin al'umma da hana su yin zanga-zangar.

Irin wannan zargi ne ya haddasa takun-saƙa tsakanin matasa da sarakuna arewacin ƙasar.

Har ta kai ga cewa matasan sun fito a shafukan sada zumunta suna zargin cewa 'an bai wa malamai kuɗi' ne domin su hana su gudanar da zanga-zangar, sannan suna kallon su a matsayin tamkar 'ƴan amshin shata'.

Sai dai bayan ganawar da aka yi tsakanin malaman addinin Musulunci na arewacin Najeriya da shugaba Tinubu, ɗaya daga cikin manyan malaman addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi ya ce "idan ma akwai waɗanda suke ƴan amshin shata, wannan group (malaman) babu ƴan amshin shata".

Shin ganawar za ta hana zanga-zanga?

Ya zuwa yanzu dai za a iya cewa gwamnatin ta nuna tana sane da halin da ake ciki a ƙasar saboda jerin ganawar da Tinubu da sauran manyan jami'an gwamnati suka gudanar a ƙoƙarin hana faruwar zanga-zangar da matasan ke shiryawa.

Sai dai babu tabbas ko matakan da gwamnatin ta ɗauka za su yi tasiri ko kuma a'a.

Rashin yarda, wata gagarumar katanga ce da ke tsakanin jagorori da mabiya a Najeriya.

Sau da dama al'umma na yi wa kalaman shugabanni, musamman ma ƴan siyasa kallon na fatar-baka kawai.

Hakan ba zai rasa nasaba da zargin da ake yi wa ƴan siyasan na gaza cika alƙawurran da suke ɗauka a loakcin zaɓe ba.

Amma ba zai zama da mamaki ba, idan a wannan karo al'ummar suka yarda da wannan yunƙuri na gwamnatin tarayyar, ganin yadda shugaban ƙasar ya yi ta fadi-tashin nuna wa al'umma cewa yana sane da halin da suke ciki.