Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Sunday Igboho ya buƙaci Fulani su fice daga jihar Oyo?
Ɗan fafutikar kafa ƙasar Yarabawa zalla, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya sake bai wa al'ummar Fulani makiyaya umarnin ficewa daga jihar Oyo da ke kudancin Najeriya nan take.
Igboho ya zargi Fulanin da yin garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe a jihar.
Wani mai magana da yawun Igboho mai suna Olayemi Koiki ya faɗa cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafukan zumunta cewa shugaban nasu ya ba da umarni ga mabiyansa su shiga dajin Oke-Ogun domin korar duk wani Bafulatani da ke zaune a wurin.
Sai dai kuma gwamnatin jihar Oyo ta yi watsi da umarnin na Sunday Igboho inda mai magana da yawunta Sulaimon Olanrewaju, ya faɗa wa sashen BBC Yoruba cewa ɗan fafutikar ba shi da ikon korar wani ɗan ƙasa daga ko'ina.
Mista Igboho ya yi iƙirarin cewa an aikata kisan kai da sace mutane da dama a dajin Oke-Ogun.
'Igboho ba ya da ikon korar Fulani'
Gwamnatin jihar Oyo ta ce Sunday Ighoho ba shi da ikon fitar da wani mutum daga wurin zamansa a ƙarƙashin doka.
"Igboho ba shi cikin gwamnati, ba kuma ɗansanda ba ne, ba kuma soja ba ne," a cewar Sulaimon Olanrewaju.
"Hukumomi ne kaɗai za su iya wannan aikin ba Sunday Ighoho ba, kuma wannan ra'ayinsa ne ba wai abin da gwamnati ke son yi ba."
Ya ƙara da cewa gwamnati na aiki tare da 'yansanda da sojoji da 'yan sa-kai wajen kare mazauna jihar ta Oyo, "saboda doka ta bai wa kowane ɗan ƙasa damar zama a ko'ina cikin Najeriya".
Martanin al'ummar Fulani
Sarkin Fulani na jihar Oyo Alhaji Abdulƙadir ya shaida wa sashen BBC Yoruba cewa suna ta ƙoƙarin ganin an samu mafita ga matsalar.
Ya ce gwamnati na ƙoƙarin tabbatar wa al'umma cewa Igboho ba shi da iko kan iƙirarinsa, amma kuma waɗanda suka san shi na ta roƙo a zauna a yi sulhu da shi.
Alhaji Abdulƙadir ya ce makiyaya na cikin zaman ɗarɗar a yankin musamman al'ummar Fulani.
Ya ce ya tuntuɓi hukumomin tsaro domin shiga tsakani kan al'amarin kuma sun tabbatar da cewa za a shawo kan matsalar.
Ya ƙara da cewa sun kasa sukuni domin ba su inda za su nufa ba bayan yankin ya kasance kamar gida a gare su domin galibinsu sun shafe shekaru a wurin.