Abubuwan da ya kamata ku sani kan hawan jini

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

Kungiyar The World Hypertension League ce ta ware ranar 17 ga watan Mayu kowacce shekara domin tunatarwa kan hatsarin hawan jini da yadda za a kauce wa kamuwa da shi.

Wata kwararriyar likita, Dr Anisa Ambursa, ta shaida wa BBC cewa hanyoyin samun hawan jini sun rabu kashi biyu: wadanda za a iya canza su da wadanda ba za a yi ba.