Ina ne Ƙudus kuma me ya sa ake taƙaddama kan shi?

Asalin hoton, Reuters
Falasɗinawa sun soma azumin watan Ramadan mai tsarki yayin da yaƙi ke ci gaba da ƙazanta tsakanin dakarun Isra'ila da mayaƙan Hamas a Gaza.
A birnin Ƙudus, faɗa ya ɓarke ranar Lahadi, jajiberin Ramadan, inda ƴan sandan Isra'ila suka hana ɗaruruwan Falasɗinawa shiga masallacin birnin da aka fi sani da al-Aqsa - na uku mafi tsarki a musulunci.
Kamfanonin dillancin labarai mallakin Isra'ila da na Falasɗinawa duka sun wallafa bidiyo da ke nuna ƴan sandan Isra'ila riƙe da sanda suna bin Falasɗinawa tare da buga musu ita a wajen.
Dubban ƴan sanda aka aike zuwa titunan Old City da ke Ƙudus inda ake sa ran dubban mutane za su yi ibada a masallacin lokacin Ramadan.
Taƙaita shiga masallacin
Tun harin 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai, Isra'ila ta hana Falasɗinawa shiga masallacin na birnin Ƙudus. An hana maza ƴan ƙasa da shekara 45 da matasa da Falasɗinawa da ke zaune a yankin Gabar Yamma shiga tsawon watanni.
Ministan tsaron Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi, Itamar Ben-Gvir shi ma ya yi kira a tsananta matakin hana shiga masallacin ga musulmai ƴan Isra'ila inda ya ce an yi haka ne domin hana Hamas yin murnar nasara yayin da ƴan Isra'ila da ke tsare har yanzu suke Gaza.
Sai dai Firaiministan Isra'ia, Benjamin Netanyahju ya yi fatali da tsarin. Babu ƙarin bayani kan yawan mutanen da za a bari su shiga masallacin a watan Ramadan.
Ministan harkokin wajen Jordan, Ayman Safadi, a ranar Litinin 11 ga wtaan Maris, ya ce matakin taƙaita shiga masallacin da Isra'ila ta ƙaƙaba kan musulmai lokacin Ramadan na ingiza lamarin zuwa babba.
Masallacin na birnin Ƙudus shi ne na uku mafi tsarki a Musulunci. Ana kuma kiran sa a matsayin Temple Mount, wuri mafi tsari ga Yahudawa.
Musulmai sun yi imanin cewa masallacin ne wurin da Annabi Muhammad SAW ya tashi zuwa sama.
An daɗe ana taƙaddama kan wurin kuma ɗaya ne daga cikin abin da ya haddasa yaƙi a 2021 tsakanin Isra'ila da Hamas.
Me ya sa Ƙudus ke da muhimmanci?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masallacin Ƙudus na tsakiyar tsohon birnin, wanda ake kira Old City sannan yana kan wani tudu da musulmai ke kira al-Haram al Sharif ko kuma wuri mai tsarki.
Wurin mai kadada 14 ga Yahudawa shi ne Har ha-Bayit, ko kuma Temple Mount.
Masallacin Ƙudus suna ne da aka raɗa wa ginin baki ɗaya kuma gida ne da wurare biyu masu tsarki ga musulmai: hubbar masallacin Ƙudus ko masallacin Qibli - da aka gina a ƙarni na takwas.
Ƙudus shi ne wuri na uku mafi tsari ga musulmai bayan Makkah da Madina.
Annabawa da dama sun yi ibada a wurin, kamar Annabi Ibrahima da Annabi Dauda da Annabi Sulaiman da Annabi Ilyas da kuma Annabi Isa AS.
Musulmi sun yi imanin cewa Annabi Muhammad ya taho daga Makkah zuwa masallacin Ƙudus kuma daga nan ne ya tashi zuwa sama a daren Isra'i da Mi'iraj a 620CE.
Wannan wuri kuma shi ne mafi tsarki ga Yahudawa.
Sun yarda cewa Sarki Solomon ya gina wurin ibada na farko shekaru 3,000 da suka wuce. Romaniyawa sun lalata wurin bauta na biyu da aka gina na Yahudawa a na 70CE.
Wa ke tafiyar da ginin masallacin Ƙudus a yanzu?
Isra'ila ta mamaye masallacin Ƙudus a yaƙin da aka yi a shekarar 1967 tsakanin Isra'ila da Larabawa makwabtanta sannan ta haɗe shi da gabashin Ƙudus da kuma wasu yankuna na Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Waɗannan yankuna na ƙarƙashin ikon Masar da Jordan a lokacin sannan matakin Isra'ila bai samu karɓuwa ba a idon duniya.
Sarkin Jordan shi ne ke da hurumin wuraren ibada na Musulmai da Kirista da ke harabar ginin Ƙudus.
Ya naɗa mambobin hukumar zakka da hubusi domin lura da wurin.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙarƙashin daɗaɗɗiyar yarjejeniyar da aka yi, waɗanda ba musulmi ba na iya kai ziyara ginin masallacin Ƙudus amma musulmi ne kaɗai za su iya ibada a cikin masallacin.
Hukumar da ke kula da Yahudawa a Isra'ila ta haramta wa Yahudawa shiga wurin ibadar na Temple Mount saboda ana ganin wurin tsarkakakke ne sosai su shiga.
Gwamnatin Isra'ila ta yanke cewa mabiya addinin kirista da Yahudawa na iya kai ziyara wajen a matsayin masu yawon buɗe ido sannan kawai na tsawon sa'a huɗu a rana sannan kwana biyar a mako.
Yahudawa na ibada ne a ɓangaren yammaci - Western Wall ko Wailing Wall, a ƙarƙashin Temple Mount - da ake ganin shi ne wuri na ƙarshe na ragowar wurin ibadar da Solomon ya samar.
Rikicin da aka yi a masallacin Ƙudus
A shekarar 2000, Ariel Sharon wanda a lokacin shi ne shugaban babbar jam'iyyar adawa a Isra'ila ya jagoranci tawagar ƴan majalisa daga jam'iyyar Likud zuwa wurin.
Ya ce: "Temple Mount a hannunmu yake kuma zai ci gaba da zama a hannunmu. Shi ne wuri mafi tsarki ga Yahudawa kuma ƴancin duk wani Bayahude ne ya kai ziyara Temple Mount."
Falasɗinawa sun nuna ja inda aka samu tashin rikici da ya janyo tashin hankali na biyu na Falasɗinawa da ake kira al-Aqsa Intifada. Fiye da Falasɗinawa 3,000 da ƴan Isra'ila 1,000 ne suka mutu.

Asalin hoton, Reuters
A watan Mayun 2021, Falasɗinawa da ke zanga-zanga kan korar wasu iyalai sun yi arangama da ƴan sandan Isra'ila a ginin masallacin Ƙudus abin da ya janyo aƙalla Falasɗinawa 163 da ƴan sandan Isra'ila 17 suka ji rauni.
A martaninta, ƙungiyar Hamas ta harba rokoki zuwa Ƙudus daga zirin Gaza abin da ya haifar da yaƙin kwana 11 da Isra'ila.
A 2022, karon farko da azumin Ramadana ya zo daidai da lokacin ibadar Yahudawa cikin shekaru 30, an samu tashin hankali inda ƴan sandan Isra'ila suka gyara filin wajen kafin yi wa Yahudawa masu ziyara rakiya zuwa wurin.
Ƴan sanda sun ce an cilla duwatsu ƙasa zuwa katangar da ke yammaci (Western Wall).

Asalin hoton, Reuters
A Afrilun 2023, ƴan sanda sun kai samame zuwa masallacin birnin Ƙudus inda suka ce masu raji sun katange kansu da masu ibada a ciki. Ƴan sanda sun ce sun yi amfani da duwatsu da tartsatsin wuta a matsayin makamai.
Falasɗinawa sun ce ƴan sanda sun yi amfani da gurneti da harsashin roba kuma mutum 50 sun ji rauni.
An soma zanga-zangar saboda rahotannin cewa masu tsattsauran ra'ayin Yahudawa sun shirya yanka akuya a wurin ibadar na Temple Mount kamar yadda Yahudawa suka yi a cikin Injila kafin Romaniyawa su lalata ginin.
Ƴan sandan Isra'ila da hukumomin da ke kula da al'amuran addini, sun ce ba za su bari a yi yanka a wajen ba.
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dage cewa ƴan sanda sun kai ɗauki domin tabbatar da cewa musulmi da kirista sun samu damar gudanr da ibadar su a Temple Mount.
Sai dai hukumar kula da zakka da hubusi ta kira samamen ƴan sandan a matsayin katsalandan ga amfanin masallacin a matsayin wurin ibada ga musulmi kaɗai.
Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ruwaito mayaƙa sun harba rokoki 16 daga Gaza a matsayin martani.






