Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Klopp zai bar Liverpool a ƙarshen kakar bana
Kocin Liverpool Jurgen Kloop zai yi murabus daga muƙamunsa a ƙarshen wannan kakar, yana cewa “ya fara gajiya da aikin”.
A watan Oktobar 20215 Liverpool ta ɗauki Klopp, kuma kwantaraginsa za ta ƙare ne a 2026.
Ya lashe Champions a 2019 kafin daga baya ya ci wa Liverpool Premier na farko cikin shekara 30 a 2019-20.
“Na shaida wa ƙungiyar tun a watan Nuwamba,” in ji Klopp, wanda ya shaida wa ƙungiyar hukuncin da ya ɗauka a Premier.
“Na san zai girgiza mutane da dama a wannan lokacin, lokacin da za su ji hakan a karon farko, amma zan iya bayani kan hakan.
“Ina son komai game da Liverpool, Ina son komai game da biurnin, Ina son komai game da masu goyon bayanmu, Ina son ƙungiyar, Ina son ma’aikatanmu. Ina son komai. Amma ɗaukar wannan matakin ya nuna cewa ina buƙatar ɗaukar wannan mataki.
“Na fara gajiya ne, amma a zahiri ba ni da wata matsala da wannan ƙungiyar, na san ranar da zan sanar da irin wannan matakin za ta zo, amma ba ni da wata matsala a yanzu a wannan kungiya. Na san ba zan dawwama ina wannan aikin ba”.
Liverpool ta lashe duk wani kofi babba tun lokacin da Klopp ɗan ƙasar Jamus ya koma ƙungiyar a 2015.
Klopp ya ɗaukarwa Liverpool kofin nahiyar Turai na shida a 2019, lokacin da ya doke Liverpool a wasan ƙarshe da aka yi a Madrid.
Bayan nan, ta ci Uefa Super Cup da na kofin duniya na Fifa Club, sai kuma mafi muhimmanci a wajensu wato Premier Lig.