Dole a sake nazari kan masarautun Kano - Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce babu shakka za a sake nazari kan dokar da ta kafa sabbin masarautu aKano.

Cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a jihar ta Kano, Kwankwaso wanda ake wa kallon shi ne uba a gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya ce an kafa masarautun ne da wata niyya ta daban wadda ba ta dace ba.

Wannan dai wata dambarwa ce da ake yi wa kallon tana ƙasa tana dabo tun ba yanzu ba. Tun bayan nasarar da Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano a zaben da aka yi a bara, wasu magoya bayansa suka riƙa kiran a rusa masarautun.

An tambayi Kwankwaso ko mai zai iya cewa game da lamarin masarautun jihar Kano, sai ya ce "Gaskiya yana ɗaya daga cikin abubuwan da ba a taɓa zama da ni a kai ba, amma kuma nasan dole za a zo a yi magana."

"A duba a ga abin da ya kamata a yi a kai, gyara za a yi ko rusau za a yi," in ji Kwankwaso.

Tsohon gwamnan ya ce "ai gyara za a yi a kai" a don haka dole za a yi nazari kan dokar.

Cikin tattaunawar da aka yi da shi ta kimanin sa'o'i biyu, Kwankwaso ya tabo lamura da dama, waɗanda suka hada da batun alaƙarsa da Shugaban Jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Sai dai maganar gyaran dokar masarautun jihar ce ta fi ɗaukar hankalin mutanen jahar da ma makwabtanta.

A watan Maris ɗin shekarar 2020 ne, gwamnatin jihar Kano ta bakin sakataren gwamnati, Alhaji Usman Alhaji, ta sanar da cire Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga kujerarsa.

Wannan dai wani mataki ne da ya raba kan al'ummar jihar Kano, wasu sun goyi bayan cire Sarkin wasu kuma suka nuna adawarsu da shi.

Kazalika masu sharhi sun yi zargin tsamin dangantaka da ke tsakani Kwankwaso da Ganduje ita ta shafi Sarki Muhammadu Sanusi II, tun da Kwankwaso ne ya naɗa shi bayan rasuwar Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

Sai dai a lokacin sanarwar gwamnatin Kano ta bayyana dalilai irinsu: sukar manufofin gwamnatin Kano, da rashin biyayya ga gwamnatin da kuma kare mutuncin jihar da dai wasu ƙarin dalilai.

Gabanin sauke shin ne kuma, gwamnati ta samar da ƙarin masarautu huɗu da suka zama tamkar kishiyoyi ga masarautar Kano.

Tun bayan wannan lokacin mutanen da ke tare da Kwankwaso ke fatan ganin sun kafa gwamnati domin dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II kan karagarsa.

Sai dai abin tambayar anan shi ne, shi Muhammadu Sanusi II zai sake karbar Sarautar idan an mayar ma shi?