An cire Grealish da Maguire daga tawagar Ingila ta Euro 2024

Asalin hoton, Reuters
Ana sa ran ɗan wasan gaba na Manchester City Jack Grealish, da ɗan bayan Manchester United Harry Maguire ba za su buga wa Ingila gasar Euro 2024 ba.
Zuwa yanzu ba a tabbatar da hakan ba a hukumance, amma kocin Ingila Gareth Southgate zai yi taron manema labarai da ƙarfe 6:00 kafin wasansu da Iceland a filin wasa na Wembley ranar Juma'a.
Sai dai kuma, an fahimci cewa Magiure bai warke ba yadda ya kamata daga raunin da ya ji a bayan ƙwaurinsa a watan Afrilu, wanda ya sa bai buga wa United wasan ƙarshe na FA da ta cinye City ba.
Grealish bai buga wasan ba gaba ɗaya kamar yadda babu shi a manyan wasnnin City da ta buga da Tottenham da kuma West Ham a ƙarshen gasar.
Tsohon ɗan wasan na Aston Villa ya buga wa Ingila wasan da ta ci Bosnia-Herzegovina 3-0 ranar Litinin, har ma aka dinga yabonsa.
Grealish d a Maguire na cikin tawagar 'yan wasa 33 kafin a rage mutum bakwai daga cikinsu zuwa 26 domin buga gasar ƙasashen Turai ta Euro 2024.
Tun da farko a ranar Alhamis an tabbatar cire ɗan wasan tsakiyar Tottenham James Maddison mai shekara 27 daga tawagar, da na Liverpool Curtis Jones mai shekara 23.
Ingila za ta buɗe wasanninta ne a Runin C da Serbia ranar 16 ga watan Yuni kafin ta kara da Denmark, da kuma Slovenia.











