Duk mutanen da ke cikin jirgin da ya ɓata a ƙarƙashin teku sun mutu

Titan Passengers

Asalin hoton, Dawood Family/Lotus Eye Photography/Reuters

Fasinjoji biyar da ke cikin jirgin ruwa mai nutsewa da ya ɓata a ƙarƙashin teku sun mutu, a cewar wani jami’i a cikin dakarun tsaron gaɓar tekun Amurka.

Kamfanin da ke kula da sufurin jirgin mai suna Titan ya ce mutanen biyar "masu tafiye-tafiyen bincike ne na haƙiƙa waɗanda suka yi tarayya a kan ƙudurin ƙwaƙuduba".

Dakarun Tsaron Gaɓar Tekun sun ce an gano wani fili mai cike da tarkace a kusa da karikicen jirgin Titanic tun da farko da safiyar Alhamis.

Jirgin ya ɓata ne a ranar Lahadi.

Mutanen da ke cikin jirgin sun haɗar da Stockton Rush, babban jami'in kamfanin da ya mallaki jirgin OceanGate mai shekara 61, da kuma wani ɗan kasuwar Birtaniya ɗan asalin Pakistan, Shahzada Dawood mai shekara 48 da ɗansa Suleman sai wani ɗan kasuwar Birtaniya, Hamish Harding ɗan shekara 58.

Na biyar ɗin shi ne Paul-Henry Nargeolet, tsohon sojan ninƙayar Faransa ɗan shekara 77 da ya yi fice wajen tafiye-tafiyen binciken ƙasa.

Yayin wani taron manema labarai ranar Alhamis, Rear Admiral John Mauger na Rundunar Tsaron Gaɓar Tekun Amurka ya ce an yi imani tarkacen suna da kama da sassan jirgin da ke tafiyar ƙarƙashin tekun.

Jirgin ruwan Titan na karkashin teku

Asalin hoton, Reuters

An gano tarkace a binciken da ake yi na Titan, jirgin da ke tafiya a ƙarƙashin teku da ya ɓace, kamar yadda aka ba da rahoton a ciki har da wani sashen wajen jirgin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ƙwararren mai ninƙaya David Mearns ya faɗa wa BBC shugaban ƙungiyar masu tafiye-tafiyen binciken ƙasa na Explorers Club - wanda ke da alaƙa da ƙwararrun masu ninƙaya - ya ce tarkace ya ƙunshi "wani faifan sauka a dandamali da kuma wata kariyar baya daga jirgin ƙarƙashin tekun".

Dakarun Tsaron Gaɓar Tekun Amurka tun da farko sun ce an gano "wani fili mai tarkace".

Yanzu ana ci gaba da bin ƙwaƙƙwafi.

Wata na'urar binciken ƙarƙashin teku da ake sarrafawa daga nesa ce ta hango tarkacen a kusa da karikicen jirgin ruwan Titanic.

Biyu daga cikin mutum biyar da ke cikin jirgin, akwai Hamish Harding wnai ɗan kasuwan Burtaniya da Bafaranshe mai tafiye-tafiyen bincike Paul-Henri Nargeolet, dukkansu wakilai ne na ƙungiyar Explorer's Club ma sansani a Amurka.

Jirgin ruwan ƙarƙashin tekun mai suna Titan ya ɓata ne a wani wuri mai nisa a cikin Tekun Arewacin Atalantika ranar Lahadi ɗauke da iskar oksijin ta tsawon kwana huɗu da mutum biyar a ciki.

Aikin bincike

Aikin neman jirgin ruwan na sunduki da ke tafiya a karkashin teku, wanda ke dauke da mutum biyar, ya dugunzuma hankalin duniya.

Musamman manyan kasashen Yamma, ganin cewa iskar shaka da jirgin ya yi guzuri wadda mutanen ke amfani da ita ta doshi karewa, wadda ta rage an yi kiyasi ba ta kai ta tsawon sa’a 20 ba, ga shi kuma har yanzu lalube kawai ake yi.

Jami’an tsaron gabar tekun Amurka da ke jagorantar wannan aiki, wanda ake ci gaba da tura duk wasu manyan na’urori masu fasaha ta yankan shakku da jirage na sama da na ruwa da na karkashin teku, sun ce an fadada yankin da ake tsammanin ganin jirgin ruwan a tekun na Atalantika saboda sauyin yanayi da kuma igiyar ruwa.

A yanzu an fadada laluben a yankin da ya ninka jihar Connecticut ta Amurka biyu, jihar mai fadin murabba’in kilomita sama da dubu goma sha uku, zuwa dubu 26 ke nan a yanzu, inda ake neman jirgin a sama da kuma cikin teku, zurfin kilomita hudu.

Jami’an sun ce ana jin karin kara a yankin da ake neman jirgin ruwan. Amma kuma sun ce ba su san karar ta meye ba, illa dai masu aikin ceto na ci gaba da duba wajen.

Kyaftin Jamie Frederick da ke jagorantar bayar da bayanai kan aikin ya bayyana kwarin gwiwarsu a kan aikin, inda ya ce har yanzu suna da fata za a ga jirgin a kuma ceto mutanen ciki:

Ya ce, ‘’ Ah, wannan aiki ne na nema da ceto, kashi dari bisa dari. Muna. Tsundum muke a tsakiyar aikin na nema da ceto, kuma za mu ci gaba da sanya duk wani abu da muke da shi a wannan kokari nagano jirgin na Titan da mutanen da ke cikinsa.’’

Jiragen sojin sama na Canada sun shiga aikin, sannan akwai jiragen ruwa da na’urori masu tafiya a ruwa da ka iya jiyo motsi ko kara, da daukar hotuna, wadanda butun-butumi masu fasaha ke sarrafawa duka an baza su a aikin a teku.

Ana sa ran samun wani cigaba da zai karfafa gwiwar gano jirgin ruwan da kuma ceto mutanen da ke ciki idan wani jirgin ruwa na Faransa da ke kan hanya ya isa wajen.

Jirgin na Faransa zai iya aika mutum-mutumi mai na’ura can cikin tekun, zurfin kafa dubu 20.

Mutane biyar da ke cikin jirgin ruwan na karkashin teku wanda ya bata tun ranar Lahadi da safe, a kan hanyarsa ta zuwa kasan tekun na Atalantika, inda katafaren jirgin ruwan nan na Titanic da ya yi hadari a shekarar 1912 yake, ‘yan Birtaniya ne uku Hamish Harding da attajiri Shahzada Dawood da dansa Suleman Dawood dalibi mai sheakara 19.

Sai mai ninkaya dan Faransa Paul Henri Nar-jo-lay da shugaban kamfanin jirgin ruwan na yawon bude idanu.