Suez Canal: Yadda jirgin ruwa ya tare gagarumar mashigar Suez ta duniya
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
An yi nasarar tsallakar da katafaren jirgin ruwan nan na dakon kaya da ya maƙale ya kuma tare mashigar ruwan Suez da ke Masar kusan tsawon mako ɗaya.
Tarin jiragen ruwa na janwe sun yi nasarar janye jirgin daga inda ya kafe kuma ya tare mashigar, inda suka sake ɗora jirgin mai suna Ever Given a cikin ruwan bayan da ya kafe tun ranar Talata.
Sai dai zuwa yanzu ba a san ko jiragen ruwa za su koma su ci gaba da zirga-zirga ba a wannan hanya wadda ke ɗaya daga cikin hanyar jiragen ruwa mafi muhimmanci a duniya.
Kafewar jirgin ta hana ɗaruruwan jiragen ruwa da ke ɗauke da kaya na biliyoyin dala wucewa na tsawon kwanaki.