Ana aikin gano jirgin ruwan ƙarƙashin teku da ya ɓace da mutane a Amurka

Ana can ana gagarumin aikin ceto a Arewacin tekun Atalantika, daga gabar Amurka bayan da wani dan karamin jirgin ruwa na karkashin teku dauke da mutum biyar ya bace a kan hanyarsa ta zuwa karkashin teku inda katafaren jirgin ruwan nan Titanic da ya nitse yake.
Mutanen da yawancinsu ‘yan yawon bude idanu ne za su je ganin yadda mataccen jirgin ruwan na Titanic yake ne.
Jami’an da ke tsaron gabar teku sun ce dan karamin jirgin ruwan na sunduki mai tsawon kafa 20, da ke tafiya a karkashin teku ya bace aka daina jin duriyarsa, tun daga ranar Lahadi da safe da ya yi ninkaya ya nausa can cikin teku, kusan sa’a daya da minti 45.
Jirgin na sunduki da ke tafiya a karkashin teku, yana daukar ‘yan yawon bude idanu ne, wadanda ke biyan dala dubu 250 domin yawo da su a karkashin teku tsawon kwana takwas hadi da zuwa wajen da Titanic din da ya yi hadari a 1912, yake, a can a zirfin kafa 12, 500 a kasan teku.
An dai gano jirgin na Titanic ne a wajen da ke na nisan kilomita 600 daga gabar tekun garin Newfoundland da ke kasar Canada.
Kuma tun daga shekarun 1980 da aka gano inda yake a karkashin tekun ake ta ziyartarsa.
Yanzu dai wannan aikin na gudana ne daga nisan mil 900 daga gabar arewa maso gabas ta tekun Atalantika ta Amurka.
Ana amfani da jiragen sama da fasaha iri daban-daban ta binciken saman ruwan teku da kuma karkashinsa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da yake magana a wajen wani taron manema labarai, Rear Admiral John Mauger, na rundunar gabar tekun Amurka, ya bayyana abin da ake yi na kokarin gano jirgin na karkashin teku;
‘’Wuri ne mai nisa kuma abu ne mai wuyar gaske gudanar da bincike a wannan wuri mai nisa, to amma muna kokarin amfani da duk wani abu da muke da shi, domin mu tabbatar mun gano jirgin mu ceto mutanen da ke cikinsa.’’
Daya daga cikin mutane biyar da ke cikin jirgin attajirin nan ne dan Birtaniya Hamish Harding wanda ya ziyarci sararin samaniya a shekarar da ta wuce.
A cikin biyar din uku ‘yan yawon bude idanu ne daya matukin jirgin dayan kuma injiniyansa ko kuma kwararre a kan jirgin.
Kamfanin da ke da jirgin ruwan OceanGate Expeditions ya ce yana duba dukkanin wata hanya da za ta kai ga ceto mutanen.
Kamfanin ya ce yana samun tayin taimako sosai daga hukumomin gwamnati da yawa da kamfanoni masu aikin shiga karkashin teku, a yayin da yake kokarin samun ji daga wadanda ke cikin jirgin ruwan.
Jirgin ruwan yana da isassun kayan da mutum biyar da ke cikinsa za su iya rayuwa ba tare da wata matsala ba, har tsawon sa’a 96.











