'Goyon bayan Obasanjo ga Peter Obi ba zai yi tasiri kan yawan kuri'un da zai samu ranar zabe ba'

A Najeriya masu sharhi kan al'amuran yau-da-kullum na bayyana ra'ayinsu kan goyon bayan da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce ya bai wa ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar Labour Peter Obi
Dakta Abubukar Kari na jami'ar Abuja, kuma mai nazari kan harkokin siyasa a Najeriya ya ce goyon bayan da Obasanjon ke yi wa mista Obi ba zai yi wani tasiri ga nasarar ɗan takarar ba.
Domin kuwa a cewarsa a tarihin siyasar Najeriya mista Obasanjo ko rumfar zaɓensa bai taɓa kawowa ba.
Dakta Kari ya ce "Obasanjo dai tsohon shugaban kasa ne wanda ya mulki Najeriya har sau biyu, kuma ana iya cewa yana da karfin fada-a-ji a ciki da wajen kasar nan - ta bangare daya ke nan - to amma idan ana zaton goyon bayan da ya ba Peter Obi na iya zama hanyar samun yawan kuri'u, ana iya cewa ba shi da tasiri sosai."
Sai dai yana ganin babban tasirin goyon bayan shi ne, "zai karfafa wa magoya bayan Peter Obi gwuiwa, sai dai wasu na ganin yana da tasiri a tsakanin kasashen waje a diflomasiyance, wanda Peter Obin zai iya cin gajiyar haka."
A ranar Lahadi ne dai tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya fito ƙarara ya nuna goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, a daidai lokacin da ake tunkarar babban zaben kasar da za a yi a watan Fabrairu.
Obasanjo ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya yi wa take da "Rokona ga 'yan Najeriya musammam matasan Najeriya."
Tsohon Shugaban ya ce babu ɗaya daga cikin 'yan takarar shugabancin kasar da ba shi da kashi a gindinsa, amma idan za a kwatantasu ta fuskar ilimi da bin ka'ida da kuma irin ci gaban da za su iya kawowa Najeriya to Obi ya sha gaban kowa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Abubakar Kari ya yi tsokaci kan yadda sauran manyan 'yan takarar mukamin shugaban kasa za su karbi labarin goyon bayan da Obasanjo ya ce zai ba Mista Obi.
"Wannan fitowa da Obasanjo yayi, zai fusata su Atiku Abubakar da Ahmed Bola Tinubu. Dama can akwai jikakkiya tsakaninsu da Obasanjo."
Ya ce za su ga kamar ya muzanta su saboda yana zawarcin matasa ne akan su mara wa Peter Obi baya, kuma ka ga su ma matasan suke zawarci.
Kan batun ko goyon bayan na iya shafar yakin neman zaben da ke gudana a halin yanzu, Dakta Kari ya ce bai ga wata alamar hakan na faruwa ba.
"Kamar yadda na ce a baya, wannan zai karfafa wa Peter Obi da magoya bayansa gwiwwa ne kawai, musamman ma ganin cewa jikin Misat Obin ya yi sanyi, musamman tun lokacin da yaƙin neman zaɓe ya kankama, sai aka daina jin ɗuriyarsa sosai-sosai."
Ya ce akwai ɓangarorin Najeriya da ba a san shi, "kuma ba a ma jin motsinsa. Amma idan aka ji mutane kamar Obasanjo na mara masa baya, to watakila wasu masu zaɓe su kalle shi."











