Weghorst zai tafi Man Utd, Arsenal ta nada sabon koci

Wout Weghorst has scored five goals in 19 appearances for the Netherlands

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan gaba na Burnley daNetherlands Wout Weghorst, wanda ke zaman aro a Besiktas, ya nemi ya fanshi kansa da kansa inda zai biya kungiyar ta Turkiyya kudi daga aljihunsa domin ta sake shi ya tafi Manchester United, wanda kuma zai iya samun hakan a Talatar nan. (Gokhan Dinc daga Express)

Kociyan Benfica Roger Schmidt ya ce babu wata sauran magana game da zawarcin da Chelsea ke yi na dan wasan tsakiya na Argentina Enzo Fernandez, wanda kwantiraginsa ya kunshi sharadin biyan fam miliyan 106 ga duk kungiyar da take sonsa. (Mirror)

Atletico Madrid na son tsawaita kwantiragin dan gaban Portugal Joao Felix da shekara daya wato har zuwa 2027, kafin dan wasan mai shekara 23 ya tafi aro Chelsea har zuwa karshen kakar nan. (Marca)

Chelsea ta tashi tsaye a kan zawarcin dan gaban Borussia Monchengladbach Marcus Thuram, dan Faransa, wanda kwantiraginsa zai kare da bazara, haka kuma Blues din na duba yuwuwar sayen dan gaban PSV Eindhoven Noni Madueke na tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21. (Times )

Brighton ta yi watsi da tayin baki da Tottenham ta gabatar mata a kan dan wasanta na gaba Leandro Trossard, kuma daman ba ta da niyyar sayar da dan Portugal din a watan nan na Janairu. (Football Insider)

West Ham United ta sake gabatar da bukatarta kan dan wasanSevilla Youssef En-Nesyri kuma tana sa ran samun aron dan Morokon mai shekara 25 har zuwa karshen kakar nan. (Times)

Tattaunawa ta yi nisa tsakanin Leeds United da kungiyar Hoffenheim ta Jamus, kan Georginio Rutter, na Faransa mai shekara 20, a cinikin da ake ganin kungiyar ta Premier ba ta taba sayen dan wasan da ya kai wannan farashin ba na fam miliyan 35.3 (Sky Sports)

Leeds United za ta bar Joe Gelhardt ya tafi aro a watan Janairun nan saboda an gaya wa matashin dan wasan na Ingila mai shekara 20 ba ya cikin tsarin kociyansu Jesse March a sauran lokacin da ya rage na kakar nan. (Football Insider)

Nottingham Forest na tattaunawa kan sayen dan wasan tsakiya na Brazil Danilo a kan fam miliyan 18 da sauran tsarabe-tsarabe daga Palmeiras. (Mail) 

Kungiyar Al Nassr ta Saudiyya na son daukan Sergio Busquets, na Sifaniya wanda kwantiraginsa da Barcelona zai kare a bazara. (ESPN)

Arsenal ta nada tsohon dan wasan Ingila naFutsal (wasan 'yan biyar-biyar) Hussein Isa, a matsayin jami'in horad da 'yan wasanta. Dan Sifaniyar da ke fitowa a tallace-tallacen talabijin a matsayin kamar Lionel Messi zai fara aikinsa kafin kakar 2023-24. (Athletic)