Martinez ya zama sabon kocin Portugal

Roberto Martinez
Bayanan hoto, Roberto Martinez

An nada tsohon kocin Belguim da Everton, Roberto Martinez a matsayin sabon kocin Portugal.

Dan kasar Sifaniya mai shekara 49, ya maye gurbin Fernando Santos, wanda ya ajiye mukaminsa bayan Portugal ta sha kashi a hannun Moroko a gasar cin kofin duniya ta FIFA da aka kamala a watan daya gabata,

Martinez ya ajiye aiki a matsayin kocin Belgium bayan shekara shida yana horar da yan wasan wasan kasar bayan da aka fitar da su a wasan rukuni na gasar cin kofin duniya.

“Na yi matukar farin ciki da na wakilci da ya daga cikin tawagogin wasan kwallon kafa da suka fi hazaka a duniya.”in ji Martinez.

"Ina matukar farin cikin kasancewa a nan. Tun ranar farko da na fara tattaunawa da shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar na san cewa wannan shiri ne na wadanni da zai faranta min rai. am very excited to be here.

" Na san akwai masu kyakkyawan fata da kuma dogon buri, amma akwai kwararu a hukumar kwallon kafa kuma na san za mu iya cimma wadannan manufofi."

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Portugal Fernando Gomes ya ce : " Wannan muhimiyyar rana ce ga tawagar kwallon kafa ta kasar."

Martinez ya shafe shekara hudu a matsayin kocin kungiyar Wigan, inda a ciki sun dauki kofin gasar FA a 2013 FA Cup, kafin ya wuce Everton in da sun zama na biyar sau daya da kuma na 11 sau biyu a gasar Firmiya

A shekara ta 2016 aka nada shi kocin Belguim, inda ya jagorance su zuwa saman teburin FIFA a 2018 bayan sun zo na uku a gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha.

Portgugal ta lashe gasar cin kofin nahiyar Turai ta 2016 da gasar cin kofin kasashen Turai ta 2018-2019 a tsawon shekara takwas da Santos ya yi yana jagorantar kungiyar

Sai dai sau daya kacal suka samu nasara a wasani uku na rukuni-rukuni da suka buga a Qatar kuma sun fuskanci komabaya bayan da Santos ya ajiye dan wasan gaba Cristiano Ronaldo a zagayen wasan sili daya kwale.