Yadda wakilin BBC da iyalansa suka tsinci kansu cikin tsaka-mai-wuya a Gaza

- Marubuci, Adnan El-Bursh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
Kusan watanni uku Adnan El-Bursh ya kwashe ya na bayar da rahotonnin yanayin da ake ciki a Gaza a lokacin da ya ke zaune a wani tanti, inda yake cin abinci sau ɗaya a rana, tare da fafutikar kula da matarsa da ƴaƴansa biyar.
Ma'aikacin BBC na sashen Larabci ya bayyana lokutan da suka fi zama masu tayar da hankali a gare shi har abin ya kai shi bango a lokacin da yake bayar da rahotonnin yaƙin.
- Gargaɗi: Wannan rahoto na ƙunshe da bayanai da hutunan da ka iya sosa zuciyar mai karatu.
Ɗaya daga cikin lokutan da ba zan taɓa mantawa da su ba a cikin wata shida da suka gabata shi ne wani dare da duka muka kwana a kan titi. Na kkalli fuskokin matata da na ƴaƴana rungume da juna sakamakon tsananin sanyin da aka fuskanta a birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza, na ji takaici a ranar.
Tagwayena masu shekara 19, Zakia da Batoul tare da ƙanwarsu Yumna mai shekara 14 suka kwanta a wuri guda, yayin da Mohamed mai shekara takwas tare da ƙanwarsa Razan mai shekara biyar suka kwanta tare da mahaifiyarsa.
A lokacin da muke ƙoƙarin isa shalƙwatar hukumar bayar da agajin Falasɗinawa ta 'Palestinian Red Crescent Society' sai muka ji ruwan ƙarar harsasai a cikin daren da kuma ƙarar jirage marasa matuƙa a saman kawunanmu.
Mun yi ƙoƙarin samun gidan haya, to sai dai kash! ashe hakan ba mafita ba ce, domin kuwa washe garin ranar, sai mamallakin gidan ya kira ni yake faɗa min cewa sojojin Isra'ila sun yi masa gargaɗin cewa za a kai wa gidan harin bam.
A lokacin ina wajen aiki, amma iyalan nawa sai suka ɗauki kayansu suka fita daga gidan.

Mun haɗu da su a shalƙwatar ƙungiyar agaji ta Red Crescent, wadda ke cike da ƴan gudun hijira.
Ni da wani ɗan'uwana muka kwana a harabar shalkwatar ƙungiyar muna tattauna yadda za mu yi don tseratar da iyalan namu.
Mun baro gidajenmu a garin Jabalia kwanaki kaɗan kafin ranar 13 ga watan Oktoba, inda muka baro mafi yawan kayanmu, bayan da sojojin Isra'ila suka ce kowa ya fice daga yankin arewacin Gaza zuwa kudanci domin tseratar da rayukansu.
A yanzu kuma muna guje wa bam a wurin da aka ce mana mu dawo don tsira da rayukanmu. Abu ne mai wahalar tunawa, Na ji takaici da tashin hankali da baƙin ciki kasancewa ba zan iya kare iyalina ba.

Daga nan kuma iyalaina suka koma wani gida a Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, yayin da ni kuma na kasance tare da tawagar BBC a wani tanti da ke asibitin Nasser a Khan Younis. Nakan kuma ziyarce su duk bayan 'yan kwanaki.
Ga hanyoyin sadarwar ba su da kyau, babu sadarwar intanet babu sabis na waya a wasu lokuta. Akwai lokacin da na yi kwana huɗu zuwa biyar ban ji daga gare su ba.
A Khan Younis, tawagar BBC - kusan mu bakwai - mun rayu da cin abinci sau ɗaya a rana. Ko da akwai abincin, a wasu lokuta ba mu ci, saboda akwai wahalar wurin yin bahaya.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wannan lokacin ne abokina shugaban ofishin Al Jazeera, Wael Al-Dahdouh ya rasa iyalansa.
Inda harin sojojin Isra'ila ya faɗa kan gidan da iyalansa ke zaune, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar matarsa da matashin ɗansa, da ƙaramar 'yarsa mai shekara bakwai da jikansa mai shekara guda.
Sojojin Isra'ila sun ce ''suna ɗaukar matakan'' rage mutuwar fararen hula, to sai dai sun ce sun kai harin - da ya kashe iyalan ɗan jaridar - kan wasu ''mayaƙan Hamas da ke zaune a yankin''.
Na kalli bidiyon abokin nawa - wanda muka shafe shekara 20 muna abota - yana kuka a gaban gawarwakin iyalan nasa a tsakiyar birnin Gaza. Na yi fatan kasancewa tare da shi a wannan lokaci.
Haka kuma akwai labarai da dama da suka zo min na mutuwar abokaina da dangina da makwabta. Zuciyata ta kaɗu. Na rasa kusan mutum 200 a wannan yaƙin.
A wannan rana ina tsaka da bayar da rahoto kai-tsaye a talabijin, sai na fashe da kuka . Da dare hawaye sun kasa barin idona, abin da ya faru da abokina Wael ya zauna min a zuciya

Na bayar da rahotonin yaƙe-yaƙen Gaza na kusan shekara 15, amma wanna yaƙi daban yake, kama daga munanan hare-hare da aka samu zuwa yawan mutaneda suka mutu.
Da misalin ƙarfe 06:15 na asubahin ranar 7 ga watan Oktoba, ƙarar wani abin fashewa ya tashe ni daga barci, inda naji 'ya'yana suna ta kururuwa. Sai na leƙa waje da tagar gidana, sai kuwa na ga ana ta harba rokoki daga Gaza zuwa Isra'ila.
A lokacin ne muka fahimci cewa Hamas ta karya katangar Isra'ila - a harin da ya kashe kusan mutum 1,200 tare da yin garkuwa da mutum 250 - Lamarin da muka tabbata cewa ba mu ga komai ba na hari, don kuwa tabbas mun sani Isra'ila za ta mayar da martani.
Fiye da mutum 34,000 ne aka kashe a Gaza, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Hamas ta bayyana. kuma har yanzu akwai fargabar jikkata da kuma mutuwa.
Kwana biyu da fara yaƙin, Na je kasuwar Jabalia, domin sayen kayan abinci. Kasuwar a cike take da mutanen da suka je sayayya, saboda fargabar rashin samun damar fita kasuwar sakamakon hare-haren Isra'ila.
Minti 10 da barina kasuwar aka saki wani mummunan harin bom, lamarin da ya wargaza kasuwar ciki har da manyan kantunan da na yi sayayya a ciki.
Na son fuskokin masu kantunan. Da yawa daga cikinsu sun mutu.

Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta 'Amnesty International' ta ce aƙalla mutum 69 aka kashe a harin, kuma za a gudanar da bincikekan harin a matsayin laifin yaƙi.
Sojojin ISra'ila dai ba su ce komai kan tambayar da BBC ta yi musu kan lamarin.
Abin da take cewa a gaba ɗayan yaƙin, shi ne tana kai hare-haren nata ne kan mayaƙan Hamas, waɗanda ta ce suna gudanar da ayyukansu daga yankunan fararen hula
Tana kuma cewa ''Akwai wasu dokokin duniya da suka amince da hare-haren da sojojin ke yi''.
Kafin yaƙin, Jabalia na da kyakkyawan yanayi, gari ne mai zaman lafiya. A can aka haife ni kuma a can nake zaune, ina ryuwa cikin farin cike tare da iyalaina, cike da burace-buracen rayuwa.
Ina da gona a gabashin garin, inda nake noma zaitun da lemo da kuma lemon tsami da hannuna. Gona ce mai kyau gonin ban sha'awa, can nake hutawa bayan na tashi daga aiki.

Asalin hoton, Adnan El-Bursh
Ranar da muke yanke hukuncin ficewa daga arewacin Gaza zuwa Khan Younis - inda muka bar gidajenmu da ofishinmu na BBC a birnin Gaza - ranar ce da ba zan taɓa mantawa da ita ba.
Mu fiye da 10 cushe cikin ƙaramar mota, ni da iyalaina mun niƙi hanya zuwa kudancin Gaza, ta hanyar bin wani titi guda ɗaya da ke cike da dubban mutane a ƙafa da ababen hawa, maƙare da kayyaki.
Tafiya ce mai cike da hatsari, domin ana tafiya ana kai hari gefe-da-gefe ne titin.
Damuwa da razani da halin rashin tabbas da baƙin ciki suka cika fuskokin iyalina, da sauran mutanen da ke kan hanyar.

Yaran suka riƙa tambayata: ''Wai ina za mu je ne? Amma gobe za mu dawo?''
Na so a ce a lokacin na ɗauki hotunanmu ni da yaran da matata a lokacin da muke tsakan da wanna tafiya.
Mahaifina malamin makaranta ne mai koyar da harshen Larabci, kuma na yi da na sanin rashin ɗaukar wasu littattafansa da ya bar min bayan mutuwarsa.
Daga baya wani makwabcina ya sanar da ni cewa an ruguza gidana, tare da ƙona gona ta.
Bayan wanna tafiya zuwa kudancin Gaza mai cike da takaici, da kwanan muka yi a wajen shalkwatar ƙungiyar Red Crescent, na ci gaba da aiki daga Khan Younis na tsawon makonni.
Su kuma iyalaina suna can a Nuseirat kuma kasancewar ba ta tare ya sa na riƙa jin wani yanayi, mai cike da tunaninsu.

Sannan kuma a farkon watan Disamba, Isra'ila ta fara kiran mutane su fice daga wani ɓangare na Khan Younis zuwa wasu yankuna, ciki har da Rafah da kudancin birnin.
Haka kuma sojojin ISra'ila suka rufe babban titin da ke kaiwa arewacin Gaza, wadda ita ce nake bi don zuwa wurin da iyalaina suke.
Don haka ban ma san ta yadda zan je wurinsu ba, koma ina zan mayar da su.
Tuni birnin Rafah ya cika da dandazon jama'a, kusan babau matsaka tsinke a birnin.
Na yi kwanaki ina cikin jimami da takaici da bain cikin rashin sanin halin da iayalaina ke cike.
Daga nan sai muka samu labarin cewa sojojin Isra'ila na dannawa kan babban titin da nufin raba yankin kudanci da tsakiyar Gaza.
Na shiga firgicin cewa za a kashe ni ko a kashe iyalaina, na fitar da ran ba za mu sake ganin juna ba.
A karon farko da na ji a jikina cewa rayuwata ta zo ƙarshe. Ban ma san wace rana ba ce. Na yi tunanin na haƙura da aiki na koma wajen iyalaina, in ma mutuwar za mu yi mu mutu tare.
Daga ƙarshe dai, ranar 11 ga watan Disamba na tuƙa mota tare da wasu abokan aikina zuwa Nuseirat.
A lokacin da na isa, ƙaramin ɗana ya rugo da gudu ya rungume ni, tare da kama wuyana ya riƙe sosai.
Mun samau nasarar mayar da su Rafah. Wurin da tawagar BBC ta sake komawa domin ci gaba da aika rahotonni. Akwai lokuta da dama da ba zan manta ba.

Asalin hoton, Getty
A ƙarsheƙarshen watan Disamba, na bayar da rahoton lokacin da Rundunar Tsaron Isra'ila (IDF) ta miƙa wa hukumomi a Gaza a gawawwaki 80.
IDF ta ce ta kwashe gawawwakin ne zuwa Gaza domin bincikawa ko akwai waɗanda aka yi garkuwa da su a cikin su.
Wata babbar mota ce ta shiga da gawawwakin zuwa cikin maƙabartar da ke yankin Rafah.
Ɗoyin da ke tashi a lokacin da aka buɗe kwantenar da ta ɗauko gawawwakin ba ya misaltuwa.
Ma'aikata sanye da takunkumin fuska ne suka rufe gawawwakin waɗanda ke cikin shuɗin manyan ledoji a wani ƙaton rami wanda aka haƙa da motar gina rami.
Ban taɓa ganin abu kamar haka ba. Ba zan iya kwatanta munin lamarin ba.
Sai kuma a watan Janairu lokacin da nake ɗauko rahoto a asibitin Rafah, inda a daidai lokacin aka shigo da wasu gawawwakin, ciki har da gawar wani ɗan Wael Al-Dahdouh, wato babban ɗansa mai suna Hamza, wanda ɗanjarida ne mai aiki da kafar yaɗa labaru ta Aljazeera.
Wane ne zai faɗa wa Wael wannan labarin? Tamkar abu ne da ba zai yiwu ba ganin irin mummunan abubuwan da ya riga ya fuskanta.
Ban iya tsayawa na saurara ba a lokacin da ɗaya daga cikin abokan aikinmu ya kira wani na kusa da Wael domin shaida masa labarin.

Asalin hoton, Getty
Wani hari ta sama da Isra'ila ta kai ne kan motar da Hamza da abokin aikinsa mai ɗaukar hoto Mustafa Thuraya ke ciki ne ya kashe su, jim kaɗan bayan sun bayar da rahoto kan ɓarnar da wani harin na Isra'ila ya yi a yankin.
Sojojin Isra'ila sun zargin cewa mutanen "sun kasance ƴaƴan ƙungiyar ƴan ta'dda ne da ke a Gaza". Iyalan ma'aikatan na Aljazeera sun ƙaryata wannan iƙirari.
Rundunar sojin Isra'ila ta yi zargin cewa mutanen biyu na amfani ne da wata na'urar maras matuƙi "lamarin da ke haifar da barazana ga dakarun na Isra'ila", sai dai wani binciken jaridar Washington Post ta nuna akasin hakan.

Ƙungiyar kula da ƴanjarida ta Reporters Without Borders ta ce sama da ƴanjarida 100 ne aka kashe a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba, kuma akasarinsu Falasɗinawa ne.
Rundunar tsaro ta Isra'ila ta ce ba ta "taɓa kuma ba za ta taɓa kai wa ƴanjarida hari da gangan ba".
Ta ce tana "ɗaukar duk wasu matakan da suka dace na aiki domin kare cutar da fararen hula, ciki har da ƴanjarida", amma "ci gaba da kasancewa a fagen da ake gwabza yaƙi na cike da haɗari".
Daga baya, labari ya iso wa BBC cewa iyalan ma'aikatanta sun samu takardar izinin ficewa daga Gaza.
Makwanni huɗu bayan nan, mu ma mun samu ficewa ta mashigar Rafah da ke kan iyaka, tare da taimakon hukumomin Masar.
Na yi wannan rubutu ne daga Qatar. Amma na san cewa a Jabalia, mutane na amfani da ciyawa da kuma abincin dabbobi a matsayin nasu abincin, yayin da ni kuma nake cin abinci mai kyawu a otal.
Nakan ji takaicin hakan - sai ina ji tamkar ina cin guba ne.
Babu alamar haske a gaba. Gaza ita ce rayuwata. Ina so na koma wata rana, amma a yanzu abin da kamar wuya.







