Aikin ceto na fuskantar barazana a ambaliyar Brazil

...

Asalin hoton, EPA

Gwamnan jihar Rio Grande do Sul ta Brazil, ya sanar da tura ƙarin ƴan sanda dubu ɗaya domin hana satar kayan mutane a wjen da ambaliya ta yi mummunar ɓarna.

Mutane aƙalla 96 suka mutu kuma har yanzu akwai wasu gwammai da ba a san wajen da suke ba.

Gwamna Eduardo Leite ya buƙaci gwamnatin tarayya ta kai masu ɗauki, duk da cewa ya sanar da matakin gwamnatin sa na ɗaukar ƙarin ma’aikatan gaggawa domin tabbatar da tsaro.

Yanzu haka dai akwai tawagar agaji da yawa da suka daina fita gudanar da aikin su idan yamma ta yi a yankin, saboda ɓullar wasu ɓata gari dake kai masu hari, da kuma y masu ƙwace.

Hukumomi sun kuma yi gargaɗin cewa yanayi zai ƙara taɓarɓarewa nan da ƴan kwanaki masu zuwa.

An yi hasashen samun ruwan sama mai ƙarfi da iska da kuma tsananin sanyi a yau Laraba.

Masu aikin ceto ne ke amfani da kwale-kwale wajen kwashe mutanen da ambaliyar ta ritsa da su, kuma Daniel Odrisch na da daga cikin su.

Ya ce "Abin takaici ne yadda muke ganin mutane cikin yanayi na ruɗani, suna gudun ceton rayuwar su ba tare da sanin wajen da suka dosa ba, basu da wanda zasu iya kira ta waya saboda wayar ta daina aiki. Babu wani tabbacin wajen da zasu je domin ganin ƴan uwa da abokan arzikin su. Gasu nan dai kawai."

Aikin ceton na ci gaba da gudana, amma ana yawan samun cikas saboda fargabar da masu aikin ke ciki.