Ta yaya maza ke kamuwa da cutar sanyin al'aura ta Candidiasis?

homme

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Giulia Granchi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brasil
  • Lokacin karatu: Minti 4

Duk da cewa an fi sanin mata da kamuwa da cutar sanyin al'aura da hunhuna ke haifarwa, wato 'candidiasis' fiye da maza, an gano cewa a yanzu maza ma na iya kamuwa da ita.

Candidiasis cuta ce wadda wata ƙwayar cuta ta hunhuna (fungus) mai suna 'Candida albicans' ke haifarwa, wadda ke sa ƙaiƙayi da zafi a jikin al'aura.

'Candida albicans' wata ƙwayar cutar hunhuna ce ce da take zama a jikin mutum tare da sauran ƙwayoyin halittar jiki.

Amma kuma wannan ƙwayar cutar tana iya haifar da cuta idan ta samu yanayi mai sauƙi ko kuma idan ta yi yawa fiye da kima.

Idan wani abu ya sa wannan ƙwayar cutar ta fara yawaita fiye da yadda ya kamata a jiki, to hakan yana lalata daidaiton jiki sai kuma cutar candidiasis ta bayyana.

Me ya sa aka fi samun wannan cutar a mata?

Akwai dalilai da dama da suka sa mata suka fi kamuwa da wannan cutar, wadanda suka haɗa da;

Rashin daidaiton sinadarai a jikin da ke faruwa a lokacin al'ada da juna-biyu da lokacin da ake amfani ƙwayoyin hana haihuwa da dai sauran su, na ƙirƙirar yanayi da zai haddasa hunhuna ta yi yawa.

Hakazalika, al'aurar mace tana kasancewa da danshi a kodayaushe, tana kuma iya ƙirƙirar yanayin da zai haifar da wannan cutar kuma ta yaɗu cikin sauƙi.

Ga maza kuma , idan ba sa barin iska ta kai ga al'aurarsu, wadda za ta taimaka wajen busar da gajeren wandonsu da ya jiƙe sanadiyyar amfani da ruwa, hakan zai saka wurin ya kasance da danshi, shi ma wanda zai iya ƙirƙirar yanayin kamuwa da cutar, in ji ƙwararriyar likita, Bianca Macedo daga ƙungiyar likitocin urology ta Brazil.

...

Asalin hoton, Getty Images

Wasu ƙarin abubuwa ma na iya haifar da cutar candidiasis a maza a cewar Macedo, waɗannan suka haɗa da:

  • Rashin tsaftace al'aura yadda ya kamata
  • Yawan fata a kan al'aura (foreskin)

Ga duka maza da mata kuma:

  • Ciwon suga, domin ƙwayar fungus ɗin na samun fa'ida daga yawan sukari a jini
  • Yawan amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta (antibiotics) akai-akai, domin suna kashe ƙwayoyin halitta masu amfani da ke kiyaye yawaitar ƙwayar cutar Candida albicans.
  • Cututtuka da ke rage ƙarfin garkuwar jiki, da sauran abubuwan da ke rage kariyar garkuwar jiki irin su gashi wato chemotherapy da rashin abinci mai gina jiki, da shan miyagun ƙwayoyi.

Alamomin da mata za su gani ko ji idan suka kamu da wannan cutar sun hada da

  • Fitar da farin ruwa kamar kalar ruwan madara daga al'aurarsu.
  • Jin zafi kamar ƙonewa a al'aurarsu
  • Jin zafi wajen yin fitsari.
  • Jin zafi sosai yayin jima'i.
  • Jin ƙaiƙayi sosai

Alamomin cutar a maza kuma sun haɗa da;

  • Jajayen tabo a kan mazakutarsu.
  • Kumburi kaɗan a al'aurarsu.
  • Jin ƙaiƙayi mai tsanani.

Yana da muhimmanci a fahimci cewa ba a ɗaukar wannan cuta ta hanyar jima'i, domin mafi yawan lokuta tana faruwa ne saboda abubuwan da aka lissafa a sama in ji Macedo.

homme se grattant

Asalin hoton, Getty Images

Gano cutar da maganinta a maza

Yawanci likitoci na iya gane cutar candidiasis ta hanyar duba mazakuta kai tsaye, ba tare da yin gwaje-gwaje ba.

Amma idan akwai shakku ko raunukan da ke da wuyar warkewa, za a iya yin gwaje-gwaje kamar cire ƙwayar cuta ko biopsy.

"Ana iya gane nau'ukan candidiasis daban-daban ta hanyar ɗaukar samfurin fata ko ruwa da ke fitowa ko kuma bincikar raunuka domin gano nau'in ƙwayar cutar.

Amma yawanci ana iya fara magani kafin a yi gwaje-gwajen," in ji Alex Meller, likita a asibitin Santa Paula da ke Brazil.

Candida albicans na iya yawaita da sauri kuma ya fi wahalar warkarwa ga masu rauni a garkuwar jiki.

Amma a mafi yawan lokuta, cutar na iya warkewa da kanta cikin kwanaki biyu zuwa uku.

Bayan tsaftace jiki.

Za a iya magance wannan cutar a maza ta hanyar amfani da

  • Man shafawa na musamman
  • Ƙwayoyin kariya ko kashe ƙwayar cutar fungi
  • Yin amfani da man kashe hunhuna na tsawon kwanaki 3 zuwa 5.
  • Ƙwayar sha ta baki

Sauran na'ukan cutar candidiasis

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Candidiasis na iya bayyana a sassa daban-daban na jiki.

A jarirai da yara, mafi yawan nau'in candidiasis shi ne thrush ko thrush na baki, wanda ke bayyana a leɓe ko cikin baki, da kuma makogwaro.

Wannan cuta na bayyana da fari-fari a harshe, cikin leɓe, da makogwaro, yana kawo wahalar hadiya abinci da kuma jin zafi.

Candidiasis na iya bayyana a fata, kamar farin-farin ɗɗingo musamman a wuraren da suke da danshi kamar hannu da kugu, da ƙasan nono. Cutar na haifar da jan tabo a fata da ƙaiƙayi mai tsanani da kuma fasa fata.

Hakanan, candidiasis na iya shafar ciki, idan kwayar cutar ta yi yawa saboda rashin daidaito a kayan ciki ko yawan amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta, ko rashin ƙarfi ga garkuwar jiki.

Sauran alamomin cutar sun haɗa da ciwon ciki da kumburin ciki da kuma.

Akwai kuma nau'in cutar da ake kira da 'systemic candidiasis' shi ne nau'i mafi tsanani, inda kwayar cutar ke yaduwa a jiki ta jini.

Wannan yana faruwa musamman ga waɗanda garkuwar jikinsu ba ta da ƙarfi, kamar masu cutar HIV, da masu yin dashe ko masu amfani da magungunan rage ƙarfin garkuwar jiki.

Alamomin wannan nau'in cutar sun haɗa da zazzabi da yawan zufa da ciwon tsoka da ciwon gaɓoɓi kuma zai iya zama babban haɗari ga rayuwa idan ba a bi da shi yadda ya kamata ba.