Me ya sa ƴan siyasa ke sauya sheƙa tun zaɓe bai ƙarato ba?

..

Asalin hoton, Others

Lokacin karatu: Minti 3

Ƙasa da shekara ɗaya da rabi da kama aikin sabuwar gwamnati, sauya sheƙa da ƴan siyasa ke yi daga wannan jam'iyya zuwa waccan ya zama ruwan dare.

Al'amarin dai ya fi ƙamari tsakanin jam'iyya mai mulki ta APC da na adawa musamman PDP da NNPP da kuma LP.

Ko a ƙarshen makon nan sai da wasu ɗaruruwan ƴan jam'iyyar APC a jihar Kano suka sanar da ficewa daga jam'iyyar zuwa jam'iyya mai mulki ta NNPP.

Sai dai kafin nan sai da wasu ƴaƴan jam'iyyar ta NNPP suka fice zuwa jam'iyyar APC.

Ko a jihar Rivers ma jam'iyyar APP ce ta lashe ƙananan hukumomi 22 daga cikin 23 na jihar a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi , biyan ficewar ƴan takarar shugabancin ƙananan hukumomin daga jam'iyyar PDP.

Me ke janyo sauya sheƙa?

Malam Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa ne kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a ta Kano wato CAS, inda ya ce "sauya sheƙa al'ada ce ta siyasa da ƴan siyasa suka fi yi a lokuta guda biyu."

Bayan kafa gwamnati: A wannan jamhuriya ta huɗu sauya sheƙa ya zama ruwan dare saɓanin sauran jamhuriyoyin da suka gabata. A kan samu yanayin da ƴan jam'iyya kan fice daga jam'iyya bayan kafa gwamnati bisa tunanin cewa an kafa gwamnati da su amma ba su samu abin da suke so ba. Hakan sai ya sa su bar jam'iyyar zuwa wata. Ko dai su bar wadda ta kafa gwamnatin jiha zuwa wadda ke mulki a tarayya ko kuma su bar mai mulkin ƙasa zuwa mai mulki a jiha.

Gabanin zaɓe: Ƴan siyasa a wasu lokuta kan sauya sheƙar siyasa daga jam'iyyar da suke tunanin za a danne su musamman batun takara da rigingimun cikin gida. Idan suka san ba za su samu takara ba sai su bar jam'iyyar su koma inda za su samu takara. Akwai kuma batun son rai inda da dama ƴan siyasar kan sauya jam'iyyar da suke ganin ta fi maiƙo.

Banbancin sauya sheƙa a yanzu da a baya

..

Asalin hoton, Getty Images

Malam Kabiru Sufi ya ce wataƙila za a iya cewa ƴan siyasar jamhuriya ta farko da ta biyu da ta uku da ma farkon ta huɗu sun fi ƴan siyasar yanzu juriya saboda akwai siyasar aƙida a waɗancan lokutan.

"A waɗancan lokutan ana ganin tasirin siyasar aƙida ce take hana mutanen sauya sheka saboda suna da juriyar abin da suka saka a gaba. Duk da cewa a yanzu ma aƙida kan sa a sauya sheƙa.

Misali idan aka kafa gwamnati amma kuma sai aka fuskanci akwai banbancin aƙida shi ne sai ka ga wasu sun fice daga wannan jam'iyyar da ta kafa mulkin zuwa wata." Kamar yadda Malam Sufi ya yi ƙarin haske.

Fa'ida da illar sauya sheƙa a dimokraɗiyya?

Malam Kabiru Sufi ya ce sauya sheƙa na da amfani da illa ga mulkin dimokraɗiyya.

"Sauya sheƙa mai ma'ana ka iya bai wa dimokraɗiyya dama ta ci gaba da samun karsashi musamman ta hanyar juya wa jam'iyya mai mulki baya.

Hakan yana tasiri a tunanin masu mulki ko jam'iyya sanin cewa ƴan jam'iyyarsu ka iya barin su saboda wani abun da suke yi ba daidai ba abin da zai sa dole su sauya salo." In ji Malam Sufi.

Sai dai kuma masanin kimiyyar siyasar ya ce a kan samu yanayin da sauya sheƙar kan yi illa ga tsarin mulkin dimokraɗiyya.

"Idan tsalleke-tsallaken ya yi yawa sannan ya zama ba don jama'a ake yi ba sai don buƙatar kai to kenan hakan ya nuna siyasar jam'iyyu ko ma dimokraɗiyyar ta zama maras amfani kamar abin da yake yawan faruwa a yanzu haka."