Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka ga watan Azumin Ramadan a Najeriya
Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, ta umarci Musulman ƙasar su fara azumin Watan Ramadan a ranar Laraba 18 ga watan Fabrairun 2026.
Matakin na alamta shigar watan Ramadan mai alfarma - wanda musulmi a faɗin duniya ke gudanar da ibadar azumi, ɗaya daga cikin shika-shikan musulunci biyar.
Cikin wata sanarwa da fadar Sarkin Musulumin ta fitar a ranar Talata da daddare ya ce an samu bayanan ganin watan a wurare daban-daban a ƙasa.
Don haka ne fadar ta sanar da Laraba 18 ga watan Fabrairu a matsayin ranar 1 ga watan Ramadan na 1447AH.
Sarkin Musulmin ya buƙaci ƴan ƙasar su yi ibada tare da sanya Najeriya cikin addu'o'in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Tun da farko hukumomin Saudiyya sun sanar da ganin watan azumin tare da bayar da umarnin tashi da azumin a ranar Laraba.
Azumin Ramadan lokaci ne da al'ummar Musulmi a faɗin duniya ke zage damtse domin yin ayyukan da za su inganta imaninsu tare da kyautata wa ƴan uwa da abokan arziki duk saboda neman tsira da samun lada.
Watan azumi lokaci ne da Allah ubangiji yake ninka ladan ibadu da mutane ke yi.
Har wa yau a watan ne kuma aka saukar wa Manzon Allah (SAW) Al-Qur'ani Mai Girma.
Yaya ake ganin jinjirin wata?
Simwal Usman Jibrin, wanda masani ne kan ganin wata, kuma jami'i a kwamitin ganin wata na fadar Sarkin Musulmi a Najeriya ya ce ana neman jinjirin wata ne bayan faɗuwar rana.
"Ana neman jinjirin wata ne bayan faɗuwar rana kasancewar a ranar 29, wata da rana kan ɓullo ne kusan lokaci ɗaya sannan kuma su faɗi a kusan lokaci ɗaya.
Masani kan lamarin ganin wata, Simwal Usman ya ce babu ƙayyadadden lokacin da wata ke kwashewa a sararin samaniya a ranar farko bayan faduwar rana.
Ayyukan alkairi da ake son yi cikin watan azumi
Akwai nau'ikan ayyukan alkairi da ake son mai azumi ya lazimta kamar yadda malamai suka yi bayani.
Sheikh Halliru Abdullahi Maraya da ke birnin Kaduna, fitaccen malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, ya kuma yi karin bayani kan wasu ayyukan da ake so mai azumi ya yawaita yi
- Yawaita karatun Al-Kur'ani
Malamin addinin Musuluncin ya ce yawaita karatun Al-Qur'ani mai girma a wannan lokaci na azumi yana haɓaka lada saboda falalarsa.
- Yawaita zikiri
Sheikh Halliru Maraya ya kwaɗaita wa mutane cewa su yawaita yin zikiri kamar istigfari da salatin annabi da hailala da kuma yawan tasbihi.
- Yawaita ciyarwa
Malamin ya kuma ce ciyarwa a wannan lokaci na azumi ba karamin abu ba ne saboda falalar da ke tattare da hakan. Ya ce Manzon Allah (SAW) ya kwaɗaitawa mutane muhimmancin ciyarwa.
"Ya kamata mu kwaikwayi irin yadda ƙasahe kamar Saudiyya ke samar da abinci irin nasu domin ciyarwa. Mutane za su iya haɗa karfi domin ciyar da masu azumi," in ji Sheikh Halliru Maraya.
- Sallar dare
Sheikh Maraya ya ce wani abu da ke haɓaka lada a watan azumi shi ne yawaitar nafilolin dare musmaman tahajjud da sallar tarawihi saboda falalar yin haka ba ta misaltuwa.
- Kame baki
Malamin ya ce mai azumi ya kasance yana kame baki daga yin karairayi saboda hakan na janyo tawaya ga azumi. Ya ce ko da mutum ba ya azumi karya haramun ce a gare shi.
"Haka kuma kame baki daga yi da mutane, misali irin yadda mutane ke zama a bakin hanya suna yi da duk wanda ya wuce, duka ya kamata a kiyaye," in ji Malamin.
- Halartar wuraren tafsiri
Sheikh Halliru ya ce mutane su rika bayar da lokacinsu wajen halartar tafsirai da kuma jin sakon Allah, inda ya ce hakan zai bai wa mutum damar sanin abubuwan da Allah yake so da wadanda ba ya so.
- Ziyarar asibitoci da gidajen yari
Wane abu kuma da Malamin ya ce na ɗaya daga cikin hanyoyi na samun lada shi ne ziyarar asibitoci da kuma gidajen yari domin taimakawa bayin Allah.
"Ziyarar asibitoci da gidajen yari na da muhimmancin gaske kuma hanya ce ta samun lada sosai. Tallafawa masu kula da marasa lafiya da kuma su marasa lafiyan da likitoci suka ba su damar yin azumi zai haɓaka ladar mutum matuka.
"Mutane za su iya haɗa-kai wajen kai kayan tallafi domin raba wa Musulmai da ke gidajen yari wajen ganin sun samu abincin buɗe-baki da kuma sahur," in ji Sheikh Halliru Maraya.